YAR'AIKI

1.9K 49 0
                                    

🌸🌸🌸🌸🌸🌸

       *YAR'AIKI*

   🌸🌸🌸🌸🌸🌸

~*Love and romantic story*~

*STORY AND WRITTEN BY FATEEMARH ZAHRA EEDREES*

*whattpad @ Eedreesfateemarh*

*page 19-20*

®🌁

*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
{{Ƙungiya Domin wayar da ƙan mata , Farin jini writer's domin ci gaban, Mata.}}

      ★{{F.J.W.A.}}★📖🖊️

https://www.facebook.com/Farin-Jini-Writers-association-101140968266505/

*Bismillah*

Kamar bazatayi magana ba sekuma tace"karuwar ka de.tafada tareda kallonsa.

Wani irrin kallo jalil yayi mata duk idonsa sunyi jawur,atsawace yace"fitarmin a mota.

Kallonsa tayi dan bata yar'da shi yayi maganan ba.

Wani tsawa daya kuma daka matane yasa ta babu shiri tasauka.

Tana sauka yaja motarsa atsiyace yabar wajan.

Wasu zafafan hawaye ne suka zubar mata akan kunci,daman tasani abinda yake nema yasamu tunda yagama kwakulleta ai dole yayi mata hakan.hawayen fuskarta ta goge sanan ta Tara taxi tawuce gida.

A bangaren hajiya ko abinda yake bata mamaki shine kyau da hasken da nafeesat tayi.

Yau kusan kwana uku kenan nafeesa bata sa jalil a idoba,duk ji take babu dadi.

Yau ne ranar da Daddy ze dawo,hajiya nataje aiki ba,se girke-girke ake,gida duk ya bade da kamshi,yau hajiya dakanta tashiga kitchen dan girkawa masoyinta abinci.bayan sun gama suka jerashi akan dining table,sanan hajiya tashiga dan gyara jikinta,bayan sun gama komai suka zauna a palor suna jiran dawowan dad.

Ya jalil ne yashigo falon idonsa yayi jawur kamar wuta,kwalla nabin kuncinsa.

Nafeesa naganin hakan tatashi dagudu ta isa gabansa tana tambayarsa lafiya?

amma yakasa amsa mata,itama hajiya tana tambayarsa

Cikin kuka ya bude baki yace"hajiya shikenan mun zama marayu?

Hajiya dabata gane inda maganarsa ta dosa ba tace marayu kuma?

Daga mata kai yayi alamun eh.

"Jalil kamin bayani bangane mekake magana akai ba.

Cikin kuka yafara fadin"hajiya dad yarasu,jirginsu tayi hatsari,dad ya rasu ya barmu,dad....

Bekai ga karasawa ba hajiya tafara salati tana kuka shikenan.

Nafeesa ko zaman dirshen tayi tama kuka sena zuci,shikenan dad yarasu,shikenan fa,a iya saninta dad mutumin kirki ne,bashida wani halin alawadar,allah de yakai rahma kabarinsa.

Duk dangin alhaji Hashim,makusansa da abokanansa na waje sunzo ma iyalansa ta'aziya,ankai sa gidansa na aihini.

Jalil duk yareme,ya susuce,bakaramin tausayi yake bawa nafeesa ba dan tasan zafin rashin iyaye bare ma inka girma dasu.

Bayan kwana hudu da rasuwan alhaji Hashim,duk an watse,daga su hajiaya se su aunty karima se alokacin suka Kara tabatar da rashin dasukayi,dan gidan yamusu fadi,babu dadi.

Bayan arba'in,jalil ne yacigaba da kulla da dukiyar mahaifinsa,ayanzu yayiwa nafeesa nisa dan yau yina wanan kasan gobe yina wacan sede waya,a yanzuh nafeesa tagama jarabawar weac dinta,sede abinda ke damunta guda a yanzuh bata son cin abinci inde taci setayi amansa,ga jiri datakeji,bata jin kwarin jikinta.

suna cikin waya da jalil take sanar dashi matsalarta.

Murmushi kawai yayi mata sanan yafada mata magungunan dazata siyo tadunka shansu zata samu sauki abinda takeji insha Allah.

*Sis zaku ganshi babu yawa wallahi banjin dadin jikinane shiyasa,kuyi hakuri danallah,nagode da comment naku*

*more comment*
*more typing*

*Real farhana*😍😍

~*Pls share*~🙏

YAR'AIKIWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu