Chapter 24

413 48 0
                                    

💍CIKAKKIYAR MACE💍

✍🏻Real Rashida Bature

PAGE2️⃣3️⃣

An sanya ranar auren amjaad da rumana wata biyu masu zuwa .

gaba d'aya amjaad ya tayarda hankalisa ,amma inba kasanshi ba ,bazaka lura da hakan ba,bazaka lura da hankalinshi atashe yakeba matukar ba cikakken saninshi kayiba, idon sa duk sun fad'a ya rame bakinshi ya bushe irin alamar me zazzabi.

"safwan ne zaune kusa dashi a falon amjaad din ya dubeshi yace amjaad ka sassauta ma kanka ,kadubi yanda duk kasanya ma kanka damuwa sekace akanka aka fara aure duk ka tsangwami kanka .

"harara amjaad yayi ma safwan tareda cewa dole kace haka tunda bama kai za'a aura ma waccan mara mutumcin ba ,wallahi ni inda wata dabanne sam baze dameniba amma abba ya dage se na auri wancan mara tarbiyan ,infa akayi auren nan tayi riba kenan  burinta ya cika , alkawarindatayi na kota Yaya Sena aureta zai cika kenan ,
tsaki yaja tareda kau da kanshi gefe wallahi duk kaina ya kulle nama rasa wani irin tunani zanyi ,dole ne kafun auren nan nasamo mafita ma kaina.

"wani mafita kenan kakeson samu ? safwan yamishi tambayar tareda gyara zaman shi .

"shiru yayi na tsawon wasu lokaci sannan yace wacece kake ganin zata iya min aiki batare da ansamu matsala ba ? ko nawa ne zan biya ta
amjaad yama safwan tambayar tamkar bashi yayi ba domin system d'inshi yake dannawa batare da ya d'ago kanshi ba.

"man kamin bayani yanda zan gane ,sam ni bansan me kake nufiba ,wani irin aikine za'a maka ?

"Shiru amjaad yayi tare da dafe goshin shi da hannayensa yace so nakeyi na daura ma yarinyar nan hawan jini , sonakeyi na guma mata bakin ciki , sonakeyi ta karyata kanta da kanta ,so nakeyi ta gane ba'a so dole .

"Ya rabbi ! amjaad wai me kake shirinyi ne ? karfa kaje kayi abunda zai Sanya abba yayi fushi dakai ,ni aganina tunda ka amsa masa zaka aureta to ni inaga no need ka tsaya kana wasu abubuwan akan wata mace har kake neman kai ka daura ma kanka hawan jinin garin zaman tunanin mafita .

"no safwan ka fahimci ni, ba wai zan mata komai bane, kaidai kawai ina son ka samomin classic baby wacce zata iya playing game din dankeson had'awa.

"shiru safwan yayi yana me duban abokin nashi yace sekamin bayani inyaso Sena san da wacce zan hadaku Wanda baza'a samu matsala ba.

"zama amjaad ya gyara tareda duban safwan ya gaya mishi bukatarshi tare da cewa banson abun ya d'auki lokaci don haka seka nemo da wuri.

"Shiru safwan yayi yana tunani har tsawan wani lokaci sannan yace yes itace zatayi ,banida ko ja khubra ce zata iya playing wannan roll din .

"wani kallo ya watso ma safwan tareda cewa banson shirme ana maganar arziki zakawani ce wancan yarin yar , gaskiya brain dinka bata aiki dai dai,oya sake tunani.

"Allah itace dai dai kai itace zata iya ,inkana ganin kamar wasa ne ka barni da komai zakasha mamaki .

"Au da kazaci nine zanje na sameta da wannan zancen? kanshi ya gyada yace inkuwa haka ka zata kayi kuskure sam banson raini kakuma san ita babu abunda tafi kwarewa akai kamar rashin kunya don haka karka sake sunana ya futo acikin labarin ka.

"Eyye kaga ango, kafa tuna, bafa agaban amaryanka kake ba barekace zaka tsara mata yanda zatayi ,don haka kabini ahankali kona fasa abunda nayi niya .

"Ka dad'e baka fasaba nidai na gama magana don haka a kiyaye.

"Zaune nake a falon mu Ina yanke farce na sabida yanda naga aundan fara fitowa.
sallama naji anyi muryan senaji kamar nasan me shi danga zanshiga tunani Sena amsa sallamar tare da cewa waye ?

"Yar hajiya ashe kina nan bakije gidan gona ba .ya fad'a daga bakin kofar d'aga labulen nayi nace bisimillah ya shigo falon muka gaisa naje na kawo mashi drink ya dubi falon yace kaka bata kusane naji gidan shiru ne ?

"Nace aikuwa yanzu ta shiga cikin gidan ,Kona Kira maka ita ne?
" A'a no no barta harta dawo .

Shirune yabiyo baya, yaci cincin da zob'o bayan ya gama yace khubra gurinki nazo neman wata  alfarma ko zaki iya yimana .

"d'ago kaina nayi na dubeshi nace taimako kuma ya safwan?

"yace to kusan hakan zance .wato khubra so mukeyi ku k'ulla soyayyar karya keda amjaad .... Ido na futo dashi waje batare dana jira naji karashin maganar ba nafara gir giza mishi nace
amma dai zolayata kakeyi ko?

"kallo na yi yace bazaki iya bane ? Kakuma kin raina ma kyawunki ne ?

"Kai na girgiza nace ko d'aya gani nayi hakan bame yuwuwa bane ,don Sam bazanyi abunda zai jayomin zubar mutumci nava ,sannan na sayo ma kaina raini agurin wancan me shegiyar ji da Kai din, agaskiya kaje ka nemu wata ,karma kabari wani yaji don Allah.

Khubra ki fahimceni ki taimaka ma abokina don Allah ,.
wai nikam ya safwan miyasa bazaka nemu wata bane kam ga mata dayawa gari zakazo ka sanyani ariginmar wancan mutumin Ina zaune kalau .

"wato khubra so yakeyi ku kullawa wannan abun domin ya rama abunda tayi mishi bafa wai ki soshi da gaske bane , kawai bukatar mu kuringa nunama kowa cewan kuna soyayya ne tunda ku kunsan ba hakan bane .

"Shiru nayi nace hmmm kaban lokaci zanyi tunani akai ,amma kasanar masa gwamnati bata aikin banza tunda fansa zai d'auka dole ne ya biya   don bazaici bulus ba dole yabiya in yanason aiki me kyau .

Murmushi safwan yayi yace to hakanma mun gode yanzu ki bamu number ki inyaso Sena kira naji me kika yanke akai.

Ina gaisuwa masoyan book dinnan .

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now