*💫⭐SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION⭐💫*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''
💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
PAGE3️⃣5️⃣
Anty kufcy wai mom tace ku shirya yanzu zamuje gidan kanin abban mu yaronshi ya rasu , sunyi waya da bros suna can zamu iskesu acan don d'azu akayi rasuwan , innalillahi, nace babba ko yaro ne yarasun? tace ya girma don yana jami'a ma ciwon ciki ne ya kamashi jiya da daddare yau kuma Allah yayi masa rasuwa,shine mom tace kushirya muje dukanmu don ita harta shirya ita da hajiya mu kawai suke jira ,mikewa nayi nace to barin shirya ki gayama rumana please kafun nagama shiryawa karsuta jiranmu .futa tayi nikuma na tashi nafara shiri banwani b'ata lokaci ba don nayi wankana tun d'azu shiyasa kawai na d'auko riga da zani na wani atamfa super red me adon see green ,ban wani shafa komai a fuskata ba illa powder da don dama ni bame yawan son cika kwalliya ma fuska ta ba ne baran yanzu da zamuje gidan mutuwa ,hijab dina na d'auko kalan kayan nasanya, tareda pos dina donna Sanya phone d'ina da key din sashina , main falo na nufo nasamu sateera har ta dawo itama cikin Shirin ta tana sanye da dogon riga na lace se hijab dinta kalan kayan ta ,tace barin duba anty rumana ko itama ta gama ,Kai na d'aga mata Ina me gyara zaman agogon hannuna ,shiganta d'akin ta samu rumana kwance akan gado tana danna wayarta daga ita se rigan barcin tun safe tashinta bata canza ba ,dubanta sateera tayi tace anty rumana ke kaid'ai muke jira fa ,yatsina fuska tayi, tace halan ni nace ku jirani ko?
sororo sateera ta tsaya kallonta tareda cewa ban gane me kike cewa ba ? kallon banza ta mata tareda cewa ,ke dubeni da kyau kinga namiki kalan matsiyata ?tunda kuka had'a tafiya da wancar banzar to ni bazanje da ku tare da itaba, don haka zaku iya tafiya in takama dole senaje gidan mutuwar to zanzo daga baya amma ba tare da wancar abarba ,zaki iya tafiya nagama magana.
Juyawa sateera tayi batare da tace komaiba ,tana zuwa falo tace mune anty kufcy ,dubanta nayi nace ya haka? tace muje kawai,bayanta na biyo nasamu tana zayyane mà iyayenta duk yanda sukayi da rumana , hajiya tace wannan yarinya dai anyi gantalalliya shiyasa tun ganinta na farko danayi halayyar ta basuminba Sam,Kai mom ta kad'a tace muje batare da ta tofa komaiba.acan muka wuni har saida mukayi sallan magriba kafin muka dawo gida .jikina se wani iri yakemin na zama waje d'aya danayi bayi na zarce na watsa ruwa ma jikina ko zanji dad'in yin barci , ina futowa a wanka natada sallar isha'i bayan na idar ne na gama duk wani abunda zanyi naje na rufe k'ofa ta don yau banice da girki ba nazo nayi kwanciya ta don ko jiran zuwanshi yimin sallama banyi ba ,barci me nauyi ne yayi gaba dani.
yau tunda na tashi na fara ayyuka na dawuri don inason nagama girkin da za'a tafi dashi gidan rasuwan ,don haka ban zaunaba ,bani na gamaba se wajan k'arfe dayan rana,tuwo nayi miyar ugun Wanda yaji naman kaji ,a manyan kula na zuba tuwon nasa miya ma awani katon cooler yanda zai ishi tuwon ,a gurguje na shirya komai naje nayi wanka na shirya cikin riga da skirt na atamfa kwalliyar dai itace ta kullum ,ganin da sauran time na dawowar amjaad gida yasani d'auko hijab d'ina na Sanya na d'auki cooler tuwon na futo dashi bakin fallon mu don na bama security sukaimin cikin gida don bazan iya d'auka ba nakai harcan, bud'e k'ofar sashina yàyi dai dai da bud'e k'ofar falon mu da amjaad yayi ,ganin haka yasa rumana tashi cikin karai raya ta nufeshi tana mishi welcome ,rumgumarshi tayi tareda had'e bakinsu waje d'aya tana tsotsa hakan yayi dai dai da futowa ta daga b'angarena ,wani irin abune ya gulleni a kirji,amma ganin danayi tayi hakane da gayya don naji haushi se dana karaso kusa dasu, nace kaga na rumana, angon qamshi ,da kad'an tallafi bayantan mana ,kabarta ita kad'ai take sarrafa ka , gaskiya bamu yardaba ,hannunshi yasa yakamo hannuna,nace bi ahankali karkasa na zubar da abun hannuna ,janye rumana yayi ajikinshi tareda Kara rikemun hannun ya karb'i cooler hannunana yace hauka kikeyi zaki d'auko wannan abu me nauyi haka ,meyasa bazaki kira security su fitar miki dashiba ?
,marai raice fuska nayi cikin shagwaba nace ,baby ni banson suke shigamin har b'angarena ne shiyasa zan futo musu dashi nan bakin k'ofar sesu d'auka sukai mota ,dubanà yayi yàce I know still I trust you Shona, sannan yasa hannu ya amshe ya ajiye tareda shigar dani jikinshi yana shin shinani yace banson haka daga yau ,karkije kijima kanki rauni ,ganin zai shige gona da iri kuma banice dashiba alokacin ,cikin hikima na zame jikina nace karka manta lokacin anty na ne yazu Ina me kashe mata ido ,bàsarwa yayi, nikuma na nufi d'akina don d'auko kulan miyar ,rumana na kalla wacce tacika tayi fammm don ba haka tasoba,taso b'atamin raine ta cusamin bak'in ciki se kuma itace nacusa mata ,kwafa tayi ta zauna akan kujera tareda yin crossing leg d'inta tana kad'asu ,dubanta yayi yace nida safwan ne mukazo yana waje dafatan kin kammala abinci don sauri mukeyi zamuje gurin karb'an gaisuwan rasuwannan,
awulakance ta kalleshi tace wallahi nikam nagaji da wannan d'aura sauk'en ,sekace wata baiwa ko "yar aiki ,ai na gayama ko agidanmu bani shiga kitchen ,kuma na gayama tun wuri kasamo me mana girki inma bazaka samoba kabari nama momy na magana ta kawomin me girki ,imma bazaka iya biyanta bane dady na ze biyata amma kak'i don haka sedai wallahi kasan nayi dani don nima dakake ganina anan zaman jiranka nakeyi ka kawomin don yunwa nakeji tun tea din safe danasha ,zaiyi magana kenan na futo d'auke da miyar dazamu tafi dashi ,bayan na rufe sashina nazo dai dai gurinsu nace masa baby mun tafi sekazo ,najuya gurinta nace anty rumana muntafi semun dawo ,wata uwar tsaki taja tareda cewa munfurcin banza munafurcin hofi hakadai zaki K'are abun dangin miji , saboda tsananin talaucin ku shiyasa zakike binsu agindi agindi don kisamu fada agunsu makira kawai wallahi asannu senayi maganinki annamimiya , murmushi nayi mata nace to ko zakizo mujene karki zauna shiru ke d'aya agida kinga baby ma tare zamu tafi dashi?wani zabura tayi tace kul karki kara gigin had'a hanya dani,don hakan bame yuwuwa bane kina Yar matsiyata .......,wani irin tsawa amjaad ya daka mata batareda ta karasa kalaman taba, yace wai shin ke bakida hankaline ?wata irin dak'ik'iya ce ke ,wato kinga nayi shiru bance miki komaiba dabakije ba shine zaki futomin dawani hali na jakuna agida , harki budi baki kice zaki zagarmin mata a gabana , to wannan yazama na farko kuma na k'arshe inba hakaba zanbaki mamaki .ya juya afusace yayi hanyar futa a falon,dubanta nayi Ina murmushi nace indai nice bakiga komaiba don wannan kad'an yamiki indai kince ke munafurcine nikuma asannu batareda na furtaba zansanyashi yacimiki dai dai da yanda kikeso yain ,sannan ki ringa nutsuwa kafun kice zaki takaloni inba hakaba kece dashan takaici,inbanda jakanta irin naki tunda nazo gidannan kintab'ajin ya d'agamin murya ko sau d'aya? kintabajin ya gayamin bak'ar magana ?kintaba ganin ya d'aga hannu ya Sanya ajikina? ke kinaganin don kin rungumeshi agabana shine zaisa naji haushi ?to kisani ko kwantar dake yayi agabana yana ci babu abunda zanji don nasan yana rage wakansa nauyi ne don nasan ba abunda zai d'iba anan se bauri ,don da bakinki kin fad'a bayajin dad'in ki ko tari bayayi idan yana kusantarki ,nikuwa bakeba harta masu gadin gidannan sun shaida da irin roman democrad'iya dayake d'iba daga jikina ,saboda daga ihun dayakeyi kad'ai ya isa ya wadatar dame sauraro ,don haka kibini asannu inba hakaba zakisha wuya aguna ,ahankali zanke nuk'aki wallahi .banjira cewarta ba nayi wufff nafuce don nasan na guma mata zazzafa .wani kukan kura rumana tayi ta biyoni abaya sukayi kicibus da......

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
General FictionLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...