💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
*SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'
PAGE4️⃣1️⃣
me kake nufi ne son?mom tana me duban amjaad.
mom na yarda da khubra,ko ba aurena akanta bazata aikata haka ba,kuma abunda zaki lura yau aka d'auki wannan pic din,domin nan nida khubra ne tana ganin motar dana siyo mata, kuma duk yanda mukayi ne kafin na futa shine akayi amfani dashi,aka cireni akasanya wani ,abunda zai dad'a sawa na gaskata khubra kayan jikinta yau tafara sanyawa,domin jiya dazan dawo natawo mata dashi,kuma time d'in dana futa itakuma tazo nankinga kenan beci ace da futana harta je ta had'u da wanj ba kuma tazo nan,kinga kuwa tabbas da'akwai wanda yake bibiyar lamarinmu.
Kai mom ta gyad'a tareda cewa ikon Allah,yanzu wani nakirinne zai yi wannan aika aikan?Kai duniya.
Kama khubra mom tayi tace kukan ya isa haka daughter,mubi komai ahankali in sha Allahu sai angano duk Wanda yayi wannan aikin,sannan zaigamu da hukunci me tsanani.
mik'ewa nayi ,na nufi hanyar fita daga falon ,wani hajijiya ne take d'ibana amma haka na daure nacigaba da tafiya mom ne ta mike daga kan kujera tabiyo bayana tanamin magana ,juyowan dazanyi naga wani irin duhu ya lullubemin idona sannan kamar wacce aka hankad'a baya.
********
Baba me zuma alherin allah,ya murje yayi kumatu abunshi,zaune yake akan dadduman dayake shimfide akasan tiles din falon,ga dambun dhinkafa Wanda yaji hadi tareda tashin qamshi,agefe kuma Inna saratu ne zaune ana fifita ma baba me zuma badon dan ba fanka ba sedon karin girmama megidan nata,lumshe ido tayi ta bud'e shi tace megida farincinkin zuciyata sonakeyi naga kazama wani big alhaji duk wannan rama su tafi karka ganka yanzu dakayi kibar nan kamar ka rame.
gefen fuskanta ya shafo yace gimbiya ta matukar zandunga samun wannan tattalin daga gareku tofa tabbas Ina gaya miki wataran se annemo me sassake k'ofar gidannan ,don wannan kayan harka da akeban ,inasamun cikakken gamsuwa daga iyalina ,ga zakin maggin danaji ankaro miki kamar wacce ta tsunduma akogin zuma ,ya k'arashe maganar da lasar labba,rufe ido inna saratu tayi tace Kai my oga zaka rikitani dayawa fa ,irin wannan kod'awa.
dariya yayi yace bazaki gane bane ,ni kad'ai nasan me nakeji ,ni kad'ai nasan me nake kwankwad'a.
rufe ido inna saratu tayi tace gaskiya nikam karka lalatani ,dariyan shima baba me zuma yayi yace na nawa kuma.
yau tunda kakus ta tashi takejin jikinta wani iri ,haka dai ta daure tacigaba da sabgoginta ,amma akasan zuciyar ta tanajin babu dad'i ajikinta,futa tayi tanufi gidan gona don dubo rabe,takuwayi sa'a ta sameshi bai futa Kai egg ba.
Cikin gidan suka dawo tare sanda suka shiga cikin falon ta zauna kana ta dubi rabe tace ,so nakeyi ka kiramin diyar albarka ,domin yau jina nakeyi wani iri ,kamar wani abu na faruwa da d'iyata.dariya rabe yayi yace Kai kakus kindai fara rikicin tsufarki kawai zakice ,kedaga kinji jikin ki ya amsa sekice ba lafiyaba , to nikam ba kudi a wayata ,sedai in zaki bada d'ari asayo kati akira addar?
wani kallo tayi mishi ,nicema zanbaka kud'in katin?to lallai yau na dad'a tabbatarwa kaina nayi babban rashi agidannan,inda yar albarka ce sedai naga kawai tasiyo katin tasa tana kiramin Wanda nake so,tana maganar tana matsar kwalla.
mikewa tayi tanufi cikin gidan,tana tafiya tana surutai ahaka ta isa sashin baba me zuma.
baba me zuma yana tsaka da more aurenshi yaji maganar kakus ,zumbur ya mike tareda gyara kayanshi yace hajiya kece tafe ,aida kinsa anyo kirana.
Yo d'annan ba dole kaga nazo da kainaba ,tana magana tana karasa shigowa cikin d'akin,mikewa inna saratu tayi gayarda kakus cikin girmamawa tareda futa a falon tabasu waje donta gana da d'an nata.
to hajiya Ina sauraronki,yauwa jamilu daman so nakeyi kakiramin yarinyar kiki ,yau hankali na yayi gurinta ,inba naji halinda take ciki bane hankalina bazai kwantaba.
To shikenan,wayarshi ya d'auko akan table din dayake falon,kiran layina yayi yashiga ,amma harta tsinke ba'a d'aga ba,sake Kira yayi still hakanne,seda yakira sau bakwai kafin kakus tace ya bari haka ,don daya Kira na barko Kakus cewa tayi yayita Kira harse an dauka.

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
General FictionLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...