Chapter 29

455 52 4
                                    

💍CIKAKKIYAR MACE💍

  ✍🏻Real Rashida Bature

PAGE2️⃣8️⃣

Babban masallacin fada tacika ta batse harta waje kan titi acike take da mutane ,aure ne Wanda ba'a taba yin irinshi ba acikin garin bauchi ,domin ya tara manyan gari Wanda sukaci suka tada Kai,mai martaba sarkin bauchi shine zai jagoranci auren Wanda shi zai zamo waliyin amaren guda biyu ,kowa ya hallara karfe 11:am na ranàr asabar dinnan aka daura auren rumana da amjaad,bayan angama daura nata aka sake sanarda sabon wani daurin auren ,nan take aka daura na khubra da amjaad nan take guri ya cakame da hayaniya ,masu addu'a nayi masu gulma nàyi don baza'a fàbà.

Shirye shirye akeyi takowani b'angare ,yayin da rumana ta zage se Shan gyara takeyi itace ci wannan ci wancan ,ga gyaran jiki ta Shashi babu karya domin takanas momy ta tasanya aka dauko wata me gyaran jiki daga maiduguri domin ta gyara ta ,an tsumata sosai , amarya se faman yo yo takeyi tana  hura hanci ta dubi aminiyar ta Jamila tace , wallahi friend Ina tausaya ma amjaad domin yanda nake jin kaina ko hmmmm,ta girgiza Kai sannan tacigaba , allah sai ya gane kuranshi ,zaisan mata ma suna suka tara,domin d'an d'anan farko idan yamin zai d'ano ma kanshi ,wallàhi duk wannan wula kancin dayamin Sena rama don zai gane bashi da wayo.

"Qawata Ina me Kara tabbatar miki da cewa tsok'alar  farko da amjaad zeyi maki zai zauce miki, zai zamo bawanki se yanda kikayi dashi ,domin wannan had'in dana baki jiya kikayi matsi dashi d'in, an tabbatar min da ingancinsa domin asatinnan yafito new model ne maganinan kedai kawai muyi fatar Allah yakaimu zuwa dare idan an kaiki ,daga gobe zaki fara shimfid'a mulkin ki agidan amjaad zai zama kece mijin shine matan.

dariya sukasa tare tafawa .

"Rumana ta dubi jamcy tace wallahi shiyasa nake matukar kaunar ki saboda duk wani abunda zai sanyani farinciki shi kikeso Allah ya nunamin ranar da zan biyaki .

Haba kawata akan d'an wannan abun bakisan akanki har kisan Kai zanyiba ,kedai kawai muyi addu'a hak'an mu tacimma ruwa kawai.

Tace amiin my jamcy ,kinga haryanxu shiru me make up din bata karaso ba ga time nata tafiya wallahi Allah Allah nakeyi naga nakasance akusa da amjaad tunda aka daura auren nan gaba d'aya wata irin masifaffiyar sha'awar shice take tsokalina .
dariya jamcy ta Sanya tace yo ankwan biyu ba'a hadu ba ai Dole.

"a b'angaren amjaad tunda aka d'aura auren zazzabi take sand'ansa yana daurewa bayison a ganoshi ,daga bayàma sashin hajiya ya nufa ya tarar da baki a falon haka ya tsallakesu yanufi cikin bedroom dinta yaci sa'a kuwa ba kowa aciki se hajiyar tana duba abubuwan buki datake rabama duk bakon dayazo musu murnan auren .

"dubanshi tayi se k'ek'e tace kaikuma yaya haka duk kayi wani zuru zuru dakai ?tun safe nake lura dakai kafun kuje d'aurin auren nan nake ganinka wani iri daga bayama dawowa kayi gida ka kwabe kayan ka kwantamin agaso wai bakajin dad'i duk ban kulakaba yakamata ka warware asamu agama bukinnan lafiya kowa ya watse .

"Murmushin dole ya k'irkiro yayi mata yace hajiya ta ,kaina ke ciwo jikina duk ciwo yakemin inaga wannan zurga zurgan danayi ne ya haifarmin da ciwon jikin .
sannu yaron kiriki girman kenan kaidai kayita hakuri halin mata se da hakuri duk dama ita wancan din ba yamzu zata tare ba sedaga baya amma duk da haka kayi kokarin ganin ka sauke mata duk wata hakkinta daya rataya a wuyarka karka yarda don ita bata gidanka tana gidansu kace abunda kama wannan bazakayi ma wancanba dolene ka lura ka zamo namiji tsayayye agidanshi karka yarda kasake addu'a da ibada bare har wata daga cikin su susamu kofar juyaka matukar zaka rike ibanda to fa zance ya kare komai zai sameka da yardan allah zaizo maka da sauki duk da bamu fatan hakan Allah yayi maka albarka yabaka ikon yin adalci atsakaninsu yasa sukuma suyi maka biyayya su zamo masu tausayinka .

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now