PAGE FOUR

122 9 1
                                    

🌹🌷🌷🌹

        *ABARWA RAI....!*
            *(abunda yaso)*

                🌹🌷🌷🌹


           *BY*
*AMINA IBRAHIM*
*UMMU AMEER*
*wattpad@ummu ameer*

💫  *ANNUR WRITERS ASSOCIATION*
*(the home of peace charity honour and super writer's)* 🌹🌷🌹


👉🏼🌷   *PAGE 4*

       Sati biyu nacika ya sake dawowah malam Abdul Karim ya bashi damar zuwa yaga siyah,domin yariga yayi bincike gameda shi,lokacin da yaje gareta zuciyarshi cike take da tsoro saboda yana tuna abunda nainah tacemishi saiyaji gaba daya zuciyarshi ta tsinke,sallama tayimishi tare da cewa " barka da wuni.

Murmushi yayi yace" barka dai siyah kin wuni lafiya.

" tace lafiya lou.

"Sunana aryan Ahmad adam anan cikin G.R.A muke zaune ba da nisaba,mahaifina ya rasu shekara biyar da suka wuce, inada qanne guda uku aadil afreen amratu,Daman kuma ba wani abu ne yakawoni wurinki ba illah soyayyar da Nike miki saboda Allah,sati na daya da dawowah daga Istanbul nafito zagaya gari,sai gashi kuma Allah ya hada ni dake,nadade ina zuwa nan ina kallonki da yanda kike gabatarda mu'amalarki na lurah da cewa halin ki nagari ne siyah kinada kirki kuma kinada tarbiya,ga kuma tsantsar kyau,inada wani aboki nan unguwar yake safraz tare mukayi karatu dashi, shinasa yayi min bincike akanki,yau nazo gareki domin in nemi yardarki inaso in aureki idan kin amince.

Sai yanzu ta dago fuska ta kalleshi idanunta cike da hawaye tace" kanason siyah! Diyar malamin islamiyyah mai sayarda dabbobi,siyah mai sayarda awara a qofar gida,Aryan ni ba kowa bace ba diyar kowa ba,kaganni kuma kaga kalar gidanmu,ranar farko daka fara furta min kalmar so,nasan kafi qarfina saboda kai bakayi kala daya da ni ba ,yau nafito ne kawai saboda baba Abdul Karim yayimin izinin fitowa  gareka.

"Kuma kasani yanda nasaba gayawa sauran mutanenda suke zuwa gareni kaima zan gayamaka......!

" dan Allah na roqeki siyah, kiyi wa girman Allah kiyi haquri kada ki nemi ki dakatar dani,wallahi inajin duk wadanda suke zuwa gunki,babu wanda yake miki sonda nikeyi miki please I beg your pardon Karki yimin haka,na dade ina Neman matarda zan aura wadda ta dace da rayuwata bansamu ba sai yanzu please...

"Goge hawayenda suka fara zubo mata ta yi sannan tace" bansan kalar ansar da zan baka ba Aryan,bansan wane matsayi kake ba araina tukun.
Kawai ta juya tashige gida.

Su najmah da fitowarsu kenan zasu wuce gida duk sunji abunda suka tattauna atsakaninsu,bayan tashige gida sukazo wurinshi nainah tace mishi" kayi haquri insha Allah zata saurareka.

" girgiza kai yayi yace " toh minene wai dalilinta naqin saurarar samari dan Allah Ku fadamin.

Liyah ce tace" anty siyah tana qin saurarar samari ne saboda kada ta yi aure ,takasa akan taimakon da takeyiwa yaya tahseen da aalim gameda da karatunsu,duk qoqarinda kaga tanayi akan sana'ar ta tanayi ne saboda su,kada su samu matsala akan karatun su,koda bazata iya biyamusu duka ba,zata iya ragemusu wani abu.

Baisan lokacinda hawaye suka cika mishi ido ba,tunanine barkatai aranshi,najmah ce ta katse mishi tunani da cewar" amma yanzu kayi haquri insha Allah tunda har baba yasan dakai komai zaiyi daidai.

Suka sake komawa cikin gidan, direct dan qaramin dakinsu suka shige inda siyah take,sukayi ta lallaba amma taqi amincewa saida suka kira yaya tahseen suka mishi bayanin abunda ka faruwa yace su bata waya,yayita yimata nasiha kuma yace mata idan har ta amince dashi taji ya kwanta mata arai toh ta aureshi,siyah tana matuqar qaunar yayanta,kuma tanajin maganarshi sosai,tace tunda har shima ya amince dashi shikenan zata aureshi din.

ABARWA RAI (Complete)Where stories live. Discover now