PAGE SIXTEEN

100 8 1
                                    

🌹🌷🌷🌷🌹

            *ABARWA RAI...!*
                *abunda yaso*

                🌹🌷🌷🌷🌹

          *BY*
*AMINA IBRAHIM*
*OMM AMEER*
*wattpad@ummu ameer*

💫   *ANNUR WRITERS ASSOCIATION*
  *(the home of charity peace honour and super writer's)*


     👉🏼🌷 *PAGE 16*



yanzu kam taji sauqi sosai tanacin abinci da taimakon nainah da yaya tahseen bata damuba akan rashin ganin momma da baba saboda angayamata cewar sun tafi tadurga wurin ganin mahaifiyar momma da batada lafiya, amma kuma kullum cikin zullumi suke saboda gashi dai ankusa bata sallama daga asibiti toh idan suka koma gida dole komai Daren dadewa tasan da cewar babu baba,amma kuma nainah ta dauki wani quduri acikin ranta wanda zata aiwatar wanda insha Allah tana tunanin idan ta aikata hakan zaisa siyah ta dau dangana idan ma batayi ba dai a asibiti suke sai a koma sabuwar jinya koda wani abu yasake faruwa da ita da ace sai ankoma kuma wani abu ya faru duk da dai ba'a fata.

Sosai take dariya akan yanda takeyiwa nasreen wasa tana dariya harda qyalqyalawa itama sai abun yake sata dariya tagumi nainah ta rabka tana kallonta har cikin ranta taji dadin yanda taga 'yar uwarta na walwala kuma tanaso wannan farin cikin ya dore acikin rayuwarsu matsowa tayi ta zauna kusa da ita ta karbi nasreen din da cewa lallaima anty siyah yanzu gani a tsaye kikeyiwa nasreen wannan wasan baki ko jin kunyar cewar ita 'yar farin ce.
Miqewa ta sakeyi tace ina zuwa anty minti biyu,fita tayi takaiwa goggo umaimah nasreen din sannan ta dawo dakin.

Riqe hannuwanta tayi tace "anty siyah!
Ras! Taji qirjinta ya buga, kallonta tayi ido cikin ido tace" na'am nainah mikuma ya faru?? Saboda idan kika yi irin wannan zaman a tare dani na tabbata akwai wani abu.

Murmushi nainah tayi tace"anty siyah ke musulma ce,kinsan da cewar ubangiji mabuwayi mai hikimah ya sanya wasu sharudda acikin musulunci wanda bazaka taba zama cikakken musulmi mai imani ba har sai ka yadda dasu ka kuma yi imani dasu cewar "mutum yayi imani da Allah,da mala'ikkunsa ,da littanfansa ,da manzanninsa,da rana ta qarshe,sannan mutum yayi imani da qaddara mai kyau ko akasinta,saboda haka kiyi haquri da duk abunda yazomiki ki yarda da qaddara,kuma komai Daren dadewa za'a mutu baza'a taba tabbata ba acikin duniyar nan duk wanda ya cuceki ya zalinceki kibarshi da Allah akwai ranar saka mako ranar da babu tsimi babu dabara babu wani sarki sai Allah, ranar da wata rayuwa bazata iya amfanar da wata rayuwa da komai ba ranarda duk zaluncinda dan uwanka ya maka zaku tsayu agaban Allah, toh minene abun damuwa aciki ,ranace wanda Allah yayi alqawari sai ya isar ma bayinsa wadanda aka zalunta hatta akan dabba mai qaho data cutarda 'yar uwarta marar qaho ballantana gamu 'yan Adam.
Anty siyah karki manta manzon Allah (s.a.w) yace" lallai dayanku' ana hada halittarsa acikin cikin mahaifiyar sa acikin kwanaki arba'in yana maniyyi,sannan yakoma gudan jini acikin wasu kwanaki arba'in, sannan yakoma gudan tsoka kwatankwacin wasu kwanaki arba'in, sannan a aika masa mala'ika domin ya busa masa rai sannan ya umurceshi da wasu kalmomi guda hudu,rubutun arzikinsa,da ajalinsa''ranar mutuwarsa,dakuma aikinsa, sannan, shi mai rabone ko marar rabo, tundaga nan zaki gane cewar dan Adam bakowa bane duk taqamarka duk mulkinka duk arzikinka ko talaucinka toh daga wannan matsayi ka fara kuma anriga da antabbarta maka da ranar mutuwarka toh miye zaka tsayawa har duniya ta rudeka kamanta da wadannan abubuwan har ka yarda kaci amana kayi zalinci.
Sannan Allah dakanshi yace yana tare da masu haquri.
Saboda ki yi haquri ki sanya Allah acikin al'amurranki haqiqa zai isarmiki kuma kizama mai tawakkali,ayanzu maganar da zan fada miki tanada girman gaske kuma zata Sosa miki zuciya amma barin kashi aciki baya maganin yunwa ko da ace ban fada miki ita ayauba dole watan watarana zaki zo ki sani.
"Anty saidai haquri saboda Allah yayiwa baba rasuwa yau kusan sati daya kenan"

ABARWA RAI (Complete)Where stories live. Discover now