PAGE THIRTY SEVEN

89 10 4
                                    

🌹🌷🌷🌷🌹

         *ABARWA RAI*

             🌹🌷🌷🌷🌹


    *OUMM AMEER*

   💫 *ANNUR WRITERS ASSOCIATION*
*(the home of charity peace honour and super writers)*

      👉🏽🌷    *PAGE 37*

     "Siyah 'yatah! Nagode da wannan babban taimakon da kikayimin Allah yasaka miki da alheri.
Kinganshi? Haka yake tsawon lokacinnan saidai kallo,yanzu taimakonda zakiyi shine,zaki kula da cin abincinsa,wanka,da sauransu,harzuwa lokacinda zai samu  lafiya,kada kikawo komai aranki ki dauka wannan zamanda zakiyi nadan lokaci da ya sami sauqi,zaki yi tafiyarki ki barshi.
"Yanzu aikinki zai fara ni zan je gida in dan yi wasu aikace aikace idan nakammala zandawo.

Cikin mutuntawa tace"toh mama babu matsala,Allah ya bashi lafiya,saikin dawo.

Tattara kayanta mama tayi da alama dai yanzu zaman na siyah ne,mama zata koma gida.

Rakata tayi har mota tare da riqa mata wasu kayan,saida ta fice sannan tadawo gun Aryan din.
Kujera taja tareda zaunawa inda yake,kallonshi take zuciyarta cike da tausayinshi,wai wannan Aryan ne,Aryan Dan gayu dan qwalisa komai nashi fes,amma yau shine kwance anan baisan inda kanshi yakeba,yayi baqi ya rame,ga qasumba duk ta cika mishi fuska.
Bata ankaraba saidai da taji saukar hawaye daga kuncinta.
"What?? Tears rolling down to her cheeks? Why? Shin tausayinshi taji kome?.
Wane gefen zuciyarta nagayamata cewar"ai duk musulmi dan uwan musulmi ne idan kaganshi a wani hali yakamata ka tausaya mishi.
Haryanzu idanunta akan fuskarshi take,tunanin rayuwar da sukayi abaya ta fara,cikin farinciki da aminci amma saikuma,hoton ranar rabuwarsu ya bayyana acikin idanunta....??

"Hello madam! Madam..!
Firgigit tayi tare da waigowa doc ta gani tsaye a gefenta yace"madam lafiya kuwa!?
Murmushin dole ta qirqiro tare da cewa"lafiya qlau.
Gyada kanshi yayi yace"kiyi haquri insha Allah zaisamu lafiya,jiyama da muka qara mishi gwaji alhamdulillah ana samun nasara sosai,kedai ki qara qoqari wurin kula dashi,nan yayimata bayanin duk yanda zata ringa yimishi.

"Ga wadannan tabs din kiriqa bashi morning and evening,ki kula sosai ki tabbata yaci abinci koda kadan ne.
Tace"ok! Thank yhu doc.
Basket din abinci ya nuna mata yace"yanzu akabawa driver yakawo.
(Aadil ne yakawo abinci,sun dauki alqawarin ba wanda zai qara zuwa sai zuwa kwana uku haka)
Ahankali ya sake bude idanunshi tar ya saukesu akanta.
Itakam harga Allah idan suka hada ido dashi wani yanayi takeji nadaban.

Miqewa tayi a rude tamarasa miyakamata tafarayi mishi.
Nazarinta doc yayi yayi murmushi yace"kinsan yanayin kula da marar lafiya especially idan ba ka sababa akwai wahala,yanzu ki taimaka mishi yafara yin wanka daga nan yaci abinci yasha maganin.
Gyada kai kawai tayi,daman mama tayimata bayanin komai yanda ake taimaka mishi yayi wankan.
Toilet din tashiga wanda already manne yake a room din nashi.
Saida ta gyara komai sannan ta dawo haryanzu kallonta kawai yake,tafi minti biyar tsaye akanshi daga nan ta cire shakka a hankali tacemishi"yanzu zamuje kayi wanka ne.
Hannunshi ta riqe tare da miqar dashi zaune,singlet din shi tacire mishi ta riqashi ahankali sukaje toilet din,tooth brush ta bashi tare da towel saita fito ta tsaya abakin qofar tare da bashi baya.

Tsaki taja yafi sau goma,aranta mita take"wannan wane irin wulaqanci ne? Shikenan saboda mutum bashida lafiya sai yayita wulaqanci shi wankanda zaiyi baifi minti goma zuwa sha biyar ba,amma yaje ya zauna aciki kusan one hour ake magana ya barta nan sanqame kamar wata body guide.

Saida ta qara kusan mintuna Biyar kafin taji alamar yagama,saboda tadaina jin motsin ruwa.
Toilet din ta shige tsaye taganshi dore da towel da alama yagama jiranta yake.
Kan plastic chair tamishi masauki  tare da saka wani towel din ta tsanemishi ruwa,cream ta shafa mishi tare da saka san qaramin comb ta gyara mishi gashinshi da yayi yawa,kayanshi ta bude ta dauko mishi wani boxer da singlet ya canza,haryanzu kallonta kawai yake,ita kuma gabadai ta maida hankalinta gun abunda take mishi.

ABARWA RAI (Complete)Where stories live. Discover now