🌹🌷🌷🌷🌹
*ABARWA RAI...!*🌹🌷🌷🌷🌹
*BY*
*AMINA IBRAHIM*
*OUMM AMEER*
*wattpad@ummu ameer*💫 *ANNUR WRITERS ASSOCIATION*
*(the home of charity peace honour and super writer's)*👉🏽🌷 *PAGE 23*
******saida ta share sati biyu masu kyau a haka ba wanda ya taba zuwa inda take,gashi duk wayar da take da su siyah bata taba gayamusu cewar wai tun ranar da aka kawota aadil bayanan ba,coz now she took the blame cewar wannan duk laifinta ne da ace bata cemishi yaje ba da qila babu inda zashi ya barta,toh amma how comes ace wai har washe garin ranar da aka kawota babu wanda yazo daga cikin en gidansu,kuma gashi harda akwati aka hado mata da ita tun ranar kawota,may be suma suna sane kenan da irin wulaqancinda ya shirya mata,tayi muguwar rama akan takaici da irin quncinda take ciki,duk bayan kwana biyu kuma idan tafito da safe takan taradda cefane komai da komai an ajiye mata abakin door dinta,tayi zuwa wurin bakin gate yafi sau dubu amma bata taba ganin kowa ba, kuma gidan a rufe yake, amma wannan dakin mai gadin saiya ke yi mata kamar akwai mutum aciki,amma bata taba ganinshi ba.
Damuwa take ciki sosai tayi missing dinshi aranta,a 'yan kwana kinnan kam kasa haquri tayi,tashiga kiran number wayar shi amma switch off,saidaga baya ta tuna cewar ai number 9ja bazata iyayi acan ba.
Saidai kawai tayita kuka a hankali tana tuna irin kalamanshi masu dadi aranta,gaskiya yanzu kam ta yarda da cewar tana sonshi har cikin ranta,amma abu daya take tunawa taji baqin ciki irin acewai yana can da wata da sunan mata da miji,idan ta tuna hakan kuma saitaji komai yafitar mata arai game dashi,she hate that amal to extend bata maso yanzu tana tuna sunanta kuma.Shiryawa tayi tunda sassafe cikin doguwar abaya baqa mai dauke da adon stones red and milk colour rolling tayi da veil dinta,tayi kyau saidai daka ganta zakaga ramar ta afili,wayarta ta dauko ta fito,yau wllhy komai za'ayi saidai ayi amma saita fita daga cikin gidan nan,kuma saitaga uban waye yake rufe gate din,idan ma takama ta haura gate ginin ne saita haure ta fice.
Tana isa taja qaramar qofar gate din tajita a datse,takalminta ta cire tasaka wurin tsinin ta shiga bubbugawa da qarfi tsiya,ganin shiru yasata dauko wani dutsi tashiga qwanqwasawa still ba wanda tagani komawa tayi tashiga zagaya gidan ko Allah zaisa tasamu inda zata haura,wani ladder ta gani da alamu tun lokacin da akayi ginin gidan yake nan,shi ta dauko ta nufi gate din dashi wayarta tasaka abakinta tashiga taka ladder din ganin da gaske take yasashi fitowa daga cikin dakin da sauri yace "subhanallah! Hajiya dan Allah dakata,yi haquri mikikeyi haka??
Da farko tsoro taji saida tajuyo ta kalleshi sannan ta gane cewar mutum ne,mamaki ne yakamata,cikin sauri ta sauko batare da bata lokaci ba ta daukeshi da wani wawan tafi,saida ya riqe kunce.
Cikin fushi ta nuna shi da yatsa tace"yanzu kai saboda kana mugu azzalumi bakada imani ko kadan arayuwarka kazo ka rufe ni duk tsawon lokacinnan iyeh? Kafadamin ribarmin kaci dakayimin haka??
Jikinshi na rawa yace" dan Allah hajiya ki gafarceni wlhy ba laifi bane,Mai gidan ne yabani wannan umarnin dan Allah kiyi haquri.
Gyada kanta tashigayi tuni hawaye suka fara bin kuncinta.
Nuna ta mishi da qofa tace"budemin qofa infita.
Dan qara rusunawa yayi yace hajiya dan kiyi haquri wlhy umarnin mai gidan ne cewar kada abarki.....!"Hey you better shut off your mouth and go an open the gate for me,nonsense ni zaka kawowa iskanci da renin hankali.
Jikinshi na rawa yace" toh hajiya tuba nake,da sauri yashiga ya dauko makulli yazo ya bude mata ta fice,saida tadan yo nisa saita tuna cewar ai bata dauko kudin abun hawaba,juyowa tayi ta dawo.
Tana turo qofar tayi kicibis da shi,da alamar waya ke da mai gidan nashi.
Hannu ta miqa mishi tace bani wayar kallon wayar yayi saikuma yamiqa mata.
Hannunta na rawa ta karbi ta dan dora akan kunnenta kamar maijin tsoron wani.
Jin daddadar muryarshi tayi wadda harta mutu bazata taba mantawa da itaba yana cewa"hello! Hello malam idi kana jina kuwa?? Hello!!
Magana yaketayi baisan miyasa malam idi yayi shiru ba,saboda bai kawo cewar ta karbi wayar ba tunda yaga yamishi cewar ta fice.
YOU ARE READING
ABARWA RAI (Complete)
FanfictionSoyayyah ce,tsantsar cin amana ce tare d butulci,Ku biyo ni insha Allah bazakuyi dana sani ba