11-12

323 12 1
                                    

👨🏻‍✈️CAPTAIN UMAR👨🏻‍✈️

Story and writing
By
Fatima(Zarah)

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Duk wacce tasan ba zata yi comment ba dan Allah kar ta Karantamun littafi.

*Typing..............*
*6/01/2021*

Page 11⏩12
************************
Alh Alhassan na da mata d'aya me suna Hajiya Rakiya da kuma yarinyar su guda d'aya wato Abeedah.

Kullun Alh Alhassan cikin yima Daddy hassada yake saboda daba dan shi ba da yanzu shine managing director d'in.

Wata ranar laraba ne,bayan daddy ya gama biyan duk wani ma'aikacinsa albashi duk Kuwa da cewa farkon watane,su kansu ma'aikatan sunyi mamaki sosai,driver d'in shi ya d'auka suka fita,umarni ya bashi da ya kaishi bank,suna zuwa yace ma driver d'in"Idi bani key d'in mota ,akwai inda zani"cikin jin kunya Idi ya mi'ko mai kasancewar tunda suka fito gida yake ta kallonsa wanda hakan ya haddasa ma Idi jin kunyar daddy,kud'i daddy ya fito dashi daga aljuhu ya mi'ka ma Idi se kuma yace"kai yaufa na baka albashi,ko dayake ri'ke kawai rabonka ne"hannu Idi yasa ya ansa sannan yace"na gode Alh,Allah yasa ka da Alkhairi",shiga mota kawai daddy yayi ya tafi yayinda Idi ya tari Express ya hau.

Tun hud'u da daddy ya fita be dawo ba har goman dare,hankalin Ammi ya tashi sosai,shi kuwa Abba be masan abin da ke faruwa ba saboda yasan yayan nasa baya hiran dare yana dawowa yake tafiya part d'in shi,hakan yasa shima be neme shiba,tun Ammi na jira a tsaye har ta zauna a kan kujera, wayanta ta d'auka ta Kira shi ,ansawa akayi tana cewa"hello"shima yana hello,wani abu kamar suka taji ya fizga wayar,hakan yasa ta kara kiransa ,amma se akace wayar is switched off,ita kanta batasan ya akayi bacci ya d'auketa ba se dai kawai farkawa tayi taji ana kiran sallan asuba,da sauri ta tashi taje parking lot d'in su dayake lokacin sun dawo GRA,tana zuwa taga ba motarsa,abinda ta fara kawowa a ranta shine"motarsa ta lalacewa ya barta a gurin gyara".

'Dakinsa ta wuce ta je ta duba taga ba kowa,cikin tashin hankali ta nufi part d'in Abba,tana xuwa tayi musu knocking,b ud'ewa akayi ta shigo"cikin tashin hankali Abba yace"yaya lafiya"cikin kuka tace"Daddyn su Zarah be dawo ba tunda ya fita jiya da yamma"wani irin tashin hankalin da Abba be taba jiba shi ya riskeshi a wannan lokacin"cikin sauri ya d'auki key d'in motarsa sannan yace"ku zauna bari Umar yazo se muje mu duba shi duk inda ya dace,'kila wani abune ya ri'keshi".

Shi kanshi Umar dayazo ya tadda wannan tashin hankalin ba 'karamin dauriya yayi ,fita sukayi da daddy duk inda ya kamata suje duk sunje basu gani ba.

At long last police station suka wuce Dan kai report,suna zuwa akace musu"ai wannan death case ne ,suje ABUTH"basu kawo komai ba dan a tunanin su ya bige wani ne ya rasu.Suna zuwa asibiti straight mutuary suka wuce kamar yanda aka sanar dasu a police station,gurin ma'aikatan Abba ya nufa yayinda Umar ya tsaya,takardan list d'in mutanen da suka rasu ne ya ja hankalin Umar har yaje ya fara karantawa,har yaxo inda aka rubuta Alh Abdullahi Isah Safana,ai a lokacin ba 'karamin tashin hankali ya riski Umar ba ,ji yayi kamar jini baya circulating jikinsa,kasa motsi yayi gaba d'aya.

Jin salatin da Abba ya zabga ne ya dawo dashi hankalinsa,kuka rurus Abba yasa kamar mace,kawai moment dinsu ya tuna shi da dan uwannasa,ma'aikatane kema Abba bayanin cewa kasheshi akayi ta hanya injecting poison da akayi a jikansa wanda yakeda had'arin gaske,poison din na kisa a 30minutes amma shi ya kai kusa 1hour be rasu ba,shiyasa a kayi anfani da 'karfi gurin kisan,cikin kuka Abba yace"inshallah se Allah ya tona as irinsu,bazan taba yafewa ba ko da duk abinda na mallaka ze kare".

Tun tara suke mutuary din amma basu aka ba ma gawan ba se karfe uku na rana,inda suka yo hanyar gida da Ambulance,Ammi Yanke jiki tayi ta fadi lokacin da taga an shigo da gawan Daddy,wanka ka mai aka shirya shi,inda aka Nemi iyalansa da kuma na kusa dashi su jemai addua,inna Ma'u duk tafisu nuna dauriya a zahiri yayinda a bad'ini kuma ba wanda ya kaita shiga cikin tashin hankali,haka aka sallace shi aka kaishi gidansa na gaskiya.

Tun daga lokacin Umar ya d'aura aniyar binciko duk me hannu a wannan kisa,amma har yau be samu wani abuba.

Saboda damuwar da Ammi ta shiga ne yasa Abba Yanke hukuncin taxo su zauna part daya da Mami dan ta ringa rage mata kewa.

*CIGABAN LABARI*

Koda Umar ya bar gun Abba,part dinsa ya nufa,kamar wanda aka tsikara yaje gurin dressing mirror,fuskarsa ya kare da ido,kawai tunanin daddy ya fara da sauri ya fito daga part d'inshi zuwa na Mami dan baya so ya sa ma kansa damuwa.

******
Ba'kar motace 'kirar zamani me tsadar gaske tayi parking a harabar makarantar Anglia Ruskin University dake East Anglia a Cambridge,duk da baa Cambridge kawai suke da campuses ba suna dashi a Chelmsford,Peterborough da kuma London.

Amma ita Abeedah tana Cambridge saboda sunfi specializing a business,mahaifinta ya fiso ta karanci business saboda yana so ta gaje shi nan gaba.

Kyakyawace sosai sanye take da Riga da wando ba jacket,kanta a kitse shi da attachment.

Abeedah kenan 'yar gidan Alh Alhassan,bata da tarbiya ko kadan,ga rashin kunya da fitsara ba club din da bata sani ba a England,gata kuma tantagayyar 'yar lesbian ce,hakan na faruwane saboda yadda Alh Alhassan baya tsawatar mata duk abinda tace shi yakeyi,tana ta ammali da miyagun kwayoyi sosai,rayuwarta kawai takeyi kamar ba zata mutu ba.

Bata san talakawa ko kadan sa'annan kuma tana da wulakanci.

Wayane a hannun ta tana gamawa ta nufi wani gida dake gefen makarantar,gurin wata abokiyar masha'arta ta nufa tana zuwa ta jata suka fara aikata masha'arsu(Allah ya karemu daga sharrin shaidan)...................

More comment............
More Typing.................

*FATIMA ZARAH*✍🏻

CAPTAIN UMAR Donde viven las historias. Descúbrelo ahora