4

1.8K 112 1
                                    

*FURUCINA NE*

            *NA*

*BATUL ADAM JATTKO*

'''Marubuciyar'''
*DAMA TA*
*AMFANIN SOYAYYA*
         '''NOW'''
*FURUCINA NE*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga  shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*Page 4*

NASIR ta samu ya toshe mata hanci sai famar wutsilniya take a k'afa da hannu
cikin sauri mommy ta k'arasa gurin ta ce "ya haka? Son kashe k'anwar taka za ka yi?".
mik'ewa ya yi ba alaman tsoro ko firgici idonsa cikin nata ya ce ''Mommy so nake na kashe ta kowa ya huta tunda dalilinta Abbana ya rasu".
Mommy ƙarasowa ta yi inda yake ta kama hannunsa ta zaunar da shi bakin gadon, ai ko da sauri ya mik'e yana yamusa fuska ya ce "Mommy ba na son ki sake zaunar da ni a kan bed din nan tunda kika kwatar da yarinyar a kai".

Mommy ba ta ce  komai ba ta zaunar da shi a kan jujeran 2setter  ta kira Harira me aikinta ta ce tafita da Nasrim bayan ta dauketa sun fita, da kusan mintuna 3 tana kallon sa ta nisa ta ce
''Nasir ka yarda da ƙaddara ba Nasrim ba ce ta kashe Abba, Allahn da ya halicce shi shi ya dauk'e shi dan bawai dan zuwan Nasrim kaɗai ba ne ka ga kafin Nasrim akwai k'addaran aure da ya shiga tsakanina da daddynku ba dan Allah ya sauk'e Abbanku ba da babu yanda za a yi  hakan ta faru  Nasrim yarinya ce ita, ba ta ma san kanta ba yanzu dan Allah ko ba ka dauki Nasrim a masayin k'anwa ba kar ka cutar da ita sabo da".
"Mommy meyasa ba kyason na cuceta".?
tace''saboda ina sonta".
"Mommy ni kindena sona".
"haba my Son ya zan dena sonka wallahi ko da irin Nasrim goma na haifa ba su isa na musu rabin son da nake maka ba".
"To mommy ba na son ki sake furta kina son ta ni kawai za ki ci gaba da so".

Dariya ta yi ta kai masa kiss a kumatu ta san abin nasa har da kishi da kuma ƙuruciya
"In sha Allah ba zan sake cewa ina son ta ba, kai zan ci gaba da cewa I love you my beautiful son."
murmushi yayi wanda ya lotsa duk kumatunsa
Ya ce"  I love you too my sweet mom".
"Thanks my dear Son kayi alk'awarin ba za ka cutar da Nasrim ba ko".
Ya ce "E, amma ni ma ina da sharuɗɗa:  Na farko ya zamana duk lokacin da zan shigo gaida ki kar na gan ta, kin san lokacin tashina tun kafin na zo ki kira masu aiki ki basu kar na shiko na ganta,
Na biyu idan an san ina gidan a daina barin ta a main parlour ko hanyan da zan gan ta in dai ban ganta ba ba zan cuce ta ba, ba na son ganinta".

Shiru mommy ta yi ganin da ta yi kamar kalamansa sun yi tsauri, amma dai farincikinsa shi ne kwanciyar hankalita dan ba ta son ganin sa cikin damuwa.
Sai ta fara magana cikin sanyi murya
tana cewa "In sha Allah zan kiyaye in dai hakan zai sanya ka farinciki dan alk'awarin da na daukarwa mahaifiyarka kenan za ka rayu cikin farinciki in sha Allah".
"Mafaifiya ta kuma?

Mommy ta ce'' Eh Nasir".
Daga nan ta kwashe komai ta fada masa ba ita ta haife shi ba, ta cigaba da cewa
"Ka k'addaran aure na da Abdulsamad shi yakashe ma haifiyar ka Halima saboda rabon yara uku da suka rasu kamar yanda k'addaran auren daddy ya kashe Abba duk da dama ina da niyar gaya maka ba ni na haife ka ba, ko dan ka yi wa mahaifiyarka Halima addu'a saboda ba ta da kowa sai kai ɗin nan, amma ba yanzu na yi niyar gaya maka ba sai ka kai ko da shekara 20 ne kafin ka sani yau de  na gaya maka ko wacece Haliman da kullum nake cewa ka mata addua  amma yanayin halinka ya sa na gaya maka yanzu daga yau ka yi wa Halima addua a matsayin mahaifiyarka ita da Abban ka".
Cikin mamaki yake binta da kallon
sai da ta gama ya ce
"Mommy idan ke ba mommy na ba ce me ya sa muke kama sosai dake? ko shi ya sa Hajja kullum take cewa ban gado halin Halima da Abba ba, ita ce hotonta a main parlourn mu da na Hajja ko?"
Ya jero mata duk waɗannan tambayoyin a jere

FURUCI NA NEWhere stories live. Discover now