25

980 103 14
                                    

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*FURUCINA NE*
( _rikicin babban gida_ )

*NA*

*BATUL ADAM JATTKO*
_marubuciyar_
*Dama ta*
*Amfanin Soyayya*

*25*



da sauri Nasrim tashiga tsakanin su tana jan Humaira daƙer tarabasu tace izza kaita mota Izza gaban Rafi,'at tazo tana murmushi tace " mrs Fu'ad kinyi kokari kuma acikin gidan ki keke mu munsan doko dan mu muke kafata ba afada da mutum acikin gidan sa duk abinda yameka kai katako amma idan a wani wajen ne baki isa ki daga ido ki kallemu bama ke idan a three brother ne wllh saide ki tsinci brain din ki a wajen kanki ai duk maccen da tayarda da kanta bata fada akan namiji"
"kut ni Rafi'ta Yakubu ƴar sarki jikar sarki wata take gaya magana haka garin nawaye dan uban mutum kuɗin ku din banza me da kuɗin naku inba rigima da rikici ba waye bai san har kisa kukeyi akan kuɗin ba ".
Nasrim jan Izza tayi tana dafa kafaɗan Rafi'at
idon ta cin nata tace " my sis kiyi hakuri dan Nasir ya haifi ɗan Agrif duk daya ne kede kiji da kan ki kuma ki gargaɗi mijinki muddin yaci gaba da ruɗani da kalaman sa masu rikitarwa to ina gaf da shiga rayuwar ku kuma idan kika sake nashiga cikin rayuwar ku to sunan ki sorry".
ta ƙaraahen maganan tareda jan hannun izza da humairah suka fice

har auka ƙarasa ficewa a parlour suna jin zage zagen Rafi'at

Nasrim tana cikin tuƙi ganin yanda duk moment din izza da humaira ya janza ahankali ta gangara gefen titi tayi parking ta juya ta kalli Humaira sannan ta sauƙe idon ta akan Izza tace meye haka sister dan Allah karku bari abinda Rafi'a tayi ya dameku dama yanda su khafulan sukayi kama da Nasir dole nawaje wanda baisan cikeken halaƙar muba ya zargi wani abu ko kunsan nima ada ina mugun mamakin yanda suka dauko komai nasa amma yanzu da aka gano momy da mahaifiyar Nasir ciki daya suka fito sai na dena mamaki kinga yarana mommy suka biyo dan de suma mazane shine ake ganin kamar tasu da nasir din kuma nima ai farine kawai ban dauko na mommy ba amma ai hancinmu da idon mu iri daya ne so meye abin damuwa zargine kuma Allah yasani".
tacikin mirror Humairah da Izza suka hada ido suka sauƙe atare izza tace "badamuwa tayi mugun cin zarafin mune taƙiraki har gida".

Nasrim tace "ba damuwa ta tada motan dan ta kauda nunanin su tace ". gobe thursday za ayi fulani's day na Rashida ku zaɓa mana ɗaya wanda zamuje a cikin Pattyn din tun bazamu iya zuwa duka ba" .

da sauri Humaira tace ".bride bath".

Izza tace " shegiya ƴar bidi'a to sister day zamuje ko Allah zaisa musamu ana walima".
Nasrim ta gyaɗa kai tafarayin rawa tana cewa "sai bidi'a sai bidi'a".

harsuka ƙarasa gida Nasrim tana cikin nishaɗi su Izza suna biyeta amma awani ɓangaren suba matuƙar tausaya mata ranan da gaskya zatayi halinta

Nasir awani anguwa da akayi sallan isha'i yaci gaba da zama acikin masallacin kama da misalin 11 wani mutum yashigo yace " ah waye kuma a masallaci har iyanzu lokacin rufe masallaci yayi kuma sai 4 na asuba idan ALLAH yakai ranmu".

Nasir ya ɗaga kai yana kallon mutumin da shi ba tsoho ba shiba yaro ba babba de haka ƙaton kwaɗo a hannu sa
yace "Babba karufeni
ni baƙone bani da wajen kwana".
mutumin cikin nazartan yanayin Nasir can yace "ayya ai bazai yuwu ba ƙa idane rufe masallaci amma kai baƙo daga ina".?
ahiru Nasir yayi yanayin saya canza
mutumin yace "shikenan ko zaka iya bina akwai shagon da yarana samari suke kwana a jikin gidana dan daganin ka bakayi kama da wanda zaka cutar da wani ba zaka iya bina".
ba musu Nasir ya maƙe yabi bayan mutumin har yakashi fanka da ƙwan suka fita yarufe, gidan nasa bani sa da masallacin
suna ƙarasawa bakin shagon mutumin yace " Hamza Ali Ibrashim Umar...
atare matasan samarin guda hudu suka fito cikin ladabi suka zube suna cewa gamu Baba

FURUCI NA NEWhere stories live. Discover now