Page 3&4

504 57 2
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 **WASU MATAN**  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar zeesardaunerh~💜🖤

*story and writting*
           by
*zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah mai rahama mai jinkai 📚

بسم الله الرحمن الرحيم
         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔

   *Page* 3~~4  
    

    ~_Wannan shafin  na sadaukar~ ~ ~da shi ga jarumai~~ ~writters association~ 🤝🥰💙

    Da shigar sa cikin matsakaicin d'akinsa ya zauna .......
yayin da ya nitsa cikin kogin tunani .........
Wai yaushe ne Saudatu zata chanxa halinta, yaushe ne zata san cewa zafin nema bashi ke kawo samuu bah ita a rayuwarta ba ta da godema Allah shi yasan ba haka halimatu ke masa ba, shiyasa idan ya tuna abunda yy mata sai yaji ransa duk a dagule. A ko da yaushe yana k'ara godema Allah da yasa halimatu ba ta mutu ba sai da tayafe masa, shikansa yasan ya yi rashi na mace ta gari mai hakuri da kawaici ga tsafta Allah ya jikanki da rahama matata. Ya share hawayen da baisan ma lokacin da suka sauka akan kuma tunsa ba.
Ako ina Ako wani gurii a gaban kowa yana iya fad'in cewa mata suna suka tara domin wasu matan zuciyar Musulunci garesu wasu matan kuwa zuciyar fir'auna garesu, kamar Saude ita a ko da yaushe ba abinda tasani illa Kud'i sannan taci dad'i tana da tsafta dai dai gwargwado amma bata kai Halima tunsa ba tunaninsa ne ya katse a lokacin da yaji kiran sallah azuhur yafito daga d'akin yayi alwala baiga Saude cikin tsakar gidan ba da'alama tana bayi ya nufi masallaci.

    Da isar sa A.M.A COMPANY direct office dinsa ya nufa bai tsaya b'ata lokaci ba yakira waya bayan yan mintutka akayi noking "yes come in", cewar Aliyu wanda ake kira Haidar mik'awa mutumin da ya shigo files d'in yayi ya ce "ya kaiwa accounter bayan fitar", mutumin ya duba time yaga 2:15 dafe goshinsa yay yace "oh Allah!", tare da nufar toilet din da ke cikin office d'in na sa, tsayawa misilta muku yadda toilet din yake bata lokacine domin komi na Aliyu haidar yana yinsa ne a tsari Alwala yayi bayan ya gama  ne ya shinfid'a darduma ya kabbarta salla domin tawucesa balle yace yy a masallacin companyn.
  
   

"Aleeya! Aleeya!! Aleeya" shine sunan da naji inna Saude na kira kamar mai shela a anguwa da sauri wadda naji an kira da Aleeya ta fito daga dakin su, matashiyar buduwar nan ce ta d'azu da mallam Yusuf ya cewa Mamana "masha Allah fata barakallahu Ahasanul halik'in", kyakkyawa ce ajen karshe duk da talauci ya nakasar da kyawunta kallo d'aya xaki mata kice wannan ta had'a jinsi da larabawa bai wai dan kyanta yayi yawa bane aa irin sihirtaccen kyawun nan gareta wanda idan mai kallo ya tsureta da ido domin wai ya gano muninta to Allah kyawu zai ga ta k'ara masa tanada round face irin wacce ake so ga zara zaran eyelashes  tareda dogon hancii had'i da pink lips, bakinta dan k'arami dashi zaka iya rantsewa hannun ta baza ya shiga ciki ba Allah ya mata diri mai kyau kamar ita tayi kanta shiyasa bata fita da gyale, a rayuwata ako ina take tana saye da hijab wani time ma harda liqab, a yanzun ma hakanne sanye take da hijab d'inta wanda ya wuce mata guiwa ta durk'usa kusa da inna Saude tareda cewa "dan Allah Inna kiyi hak'uri koda kika kirani ina sallah ne shiyasa ban amsa da wurii ba", tsaki inna taja "msssttwwwssss", tare da cewa "kedai kika sani kin shige d'aki kin dunkule salon malam yazo yace an maki wani abu nidai dan Allah tashi ki had'a wuta ki d'ora sanwar tuwo kinga uku ta kusa"  da "to", ta amsa tare da nufar wani gun da alama kici ne..............................................✍️✍️✍️

      *Zeesardaunerh*ce*

           ( ~yar karamar su babbar~ ~su~)👧🥰🤩

# _Comment_
# _like_
# _share_

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now