👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkaiYa ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 81&82Wani irin nauyi zuciya da ƙafafuwanta suka yi wanda dakyar ta iya cira su,yayin da kanta keyi mata wata irin sarawa kamar zaya rabe gida biyu,dakyar ta ke tafiya har ta kawo bakin titi ta shiga adai-daita,gabaɗaya ta rasa wane irin tunani zata yi,ji take kamar mafarkine take wanda bata fatan ya kasance gaskiya har abadan abada amma ina ƙaddara ta riga fata,bakin alkalami ya riga ya bushe.
"Hajiya.." mai adaidaitan ya faɗa cikin ɗaga murya wanda hakan ya saka ta dawo hayyacinta
"Tun ɗazu ina miki magana kimin shiru,idan baki tashi ba ki fita ina da abun yi,kawai kinzo kin zauna ma mutun a abun hawa batare da kin faɗi gurin da za'a kai ki ba,ko ke kurmace?"
"Kayi hakuri bawan Allah ban ji ka bane"
"tou naji,yanzun ina zana kai ki"
Sunan unguwar ta faɗa masa tare da kwatancen inda zaya kai ta .
Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta shiga ciki gidan ko sallama bata yi ba,da kallo mama Hawwa ta bita tana mamakin lafiya ta ganta a wannan yanayin,direct ɗakinta ta wuce tare da zubewa saman kujerun ta tama rasa mi zatayi wane tunani zatayi,kuka zata yi kome? duk abunda ya faru ita taja wa kanta.
KABEER
Kwanan sa hudu a Asibiti aka sallameshi ya dawo gida,a ranar da ya dawo yaje gidansu Aleeya ya ƙarbo wasiyyar da Saude tace sahibarsa ta bar masa,sai nuna sa ake ana cewa mahaukaci ya samu lafiya wasu kuma har musabaha suke masa tare da addu'ar Allah bi da lafiya.
Batare da ya buɗa wasiyyar ba ya kaita ma'aji mai kyau ya ajiyeta,safiya na wayewa ya tada ballin sai an sake yin jana'izar Aleeya,da kallo kawai kowa ya bishi domin abun nasa azeemun ne,wace jana'iza za ayi bayan wacce aka mata da ta mutu,sunyi iya kokarinsu sun fahimtar dashi cewa ja'iza ba'a yinta sai da gawar mamaci kuma gawar Aleeya ta daɗe a kabrinta don haka bazai yu ayi mata jana'iza ba,sai cewa yayi tunda baza'a iya sake yin jana'izar ba ai a sake ansar gaisuwa, a kuma yi mata addu'a.
Rasa abun ce masa suka yi domin lamarin nasa yafi karfinsu yayin da tunani ya cika zuciyarsu mussamman Ummu da Abbansa da suka san gaskiyar cewa Aleeya tana raye bata mutu ba,taya za'ayi ansar gaisuwar mutumen da bai mutu ba,wannan wace irin kaddara ce.

YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...