page 61&62

212 26 7
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab Sardaunerh*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          *⚜️©J.A.W📚🖌️*

*Page* 61~~62

Da sauri Salmat tayo wujina tana cewa,

"dafatan baki ji ciwo ba Add...

Maganar ta ce ta datse a lokacin da tayi arba da  goshina yana zubda jini ta cikin liqab ai da sauri ta daga liqab ɗin tana cewa,

"jini kuma? Adda goshinki na fitar da jini..

    Lokacin da Kabeer ya faka machine ɗinsa ya matso kusa dasu domin ya bada hakuri a dai_dai lokacin kuma Salmat ke  dagewa Aliya liqab dinta ta hanata amma Salmat taki bari tana cewa,

"jini ne fa ke juba a goshinki Adda amma kice baza'a cire wannan abun ba"

"Fatabarakallahu ahsanul haliki" shine abunda Kabeer ya furta a lokacin da yayi tozali da kyakkyawar fuskar Agla,bai dawo daga duniyar kallon fuskanta ba yaji sautin muryar ta mai taushi tana cewa,

"bafa wani ciwo naji ba Salmat,kawai kaina ne ya dan bugu da wannan dutsen"

Tafada a lokacin da ta saki liqab dinta ta dage goshin da hannu daya ya yin da take nunawa yarinyar da ke tare da ita dutsin.

"juriyar tsiyane ke gareki wlh Adda,da nice yasen sai an kwasheni da mota wurin nan domin bazan tashi ba ehhe,ko da yake mai machine ne ya bugeki ɗan air kawai kilama ya tserewarsa kar a sashi biyan kudin magani dana diyyar jininki da ya zuba"
Inji Salmat tana jan tsaki

Tsaye ya yi yana kallon Salmat dake zuba ko uffan bai ce mata ba.

Hakama Aliya da ta mike ta ganshi kusa da su ya zuba mata idanu suna hada ido ya yi sauri ya juya yana kallon Salmat.

Juyowar da Salmat za tayi tayi ido hudu da Kabeer sai tayi shiru.

Hakuri ya basu yana cewa ba da gangan bane don Allah su yi hakuri,cikin sanyayyar muryarta tace,

"shikenan ba komi"

"wane ba komi Adda!
ya buge ki kice ba komi,tab yasen to ni ban hakura ba sai ya biya kuɗin magani ehhe"

"Salmattt.."

"wace Salmat!garama ki yi shiru da bakinki Adda domin ni bazan hakura ba,abu sai kace yar sadaqa !
ya buge ki har jini ya fita sannan daga ya bada hakuri kice kin hakura ba batun ya kai ki chemist a dubaki a baki magani? a'a sai wani cewa yi hakuri"
Tafada tana kwaikwayon muryartai
"cikin ma ba'ace ya biya diyya ba,kilama diseases sun shiga"

   Ji ya yi yarinyar ta kara burgeshi har cikin ransa komi nata ya yi masa gata bata da hayaniya, surutun da Salmat ke yi ya tsayar da tunaninsa ya koma saurarenta domin shi abun ma dariya ya bashi sai yaji duk bacin ran da maryama tasa masa yana gushewa ,kuma shi bai ga laifin yarinyar ba domin gaskiya take faɗa.

"ok Kanwar mu kar kisamu damuwa wannan shine abunda kike bukata ko?

"eh"

"ba chemist ba Asibiti ma zankaiku adubata domin bazan so wani abu ya samu Addarmu ba"

"ni dai bance ba chemist ma ya isa ehhe,kuma Addata ce ba ta ka ba"

"to naji,bazan so wani abu ya samu Addar...ummm wa ma?

"ohho"

"nama tuna,Addan Salmat"

Waigowa Kabeer da Salmat su kayi da niyar yiwa Aliya magana amma wayam ba Aliya Kabeer ya dubi Salmat yace,

"to ina Addan ta ki ?"

"nima bansaniba,kilama tayi tafiyarta"

"ai duk laifin ki ne kika tsaya surutu gashi kin sa ta tafi ko sunanta ban sani ba"

"wai lafina,jimin ba wan Allah ni mi na yi,ai duk laifin kane"

"tou naji,mu tafi na sauke ki kinga sai na kai Addan naki chemist din"

cikin kasa da murya kamar wacce Aliya zataji tace masa,

"Kasan Allah,tunda tace ta hakura komi zakayi baza ta yadda aje chemist dinnan ba domin ba ta son magani ko kaɗan"

"Allah?"

"to karya zan maka,ko nasa ka ne da zan ma ka karya"
Salmat ta fada tana bata fuska

"sorry yar kanwata"

"ba wani daɗin baki,nidai muje ka saukeni yadda kace,ko man machine ɗin ka na kona na rage haushin mai napep din da ya ki shiga da mu ciki har kayi sillar buge Addata"

"da naga wannan mai napep din da sai nayi masa kyauta saboda yayi silar haduwata da kyakkyawan fure"

"mi kace?"

"cewa nayi da naga wannan mai napep din da na mazga masa mari domin bai kamata ya sauke kyakkyawan yara bisa hanya kuma gefen titi ba"
yafada yana murmushi

Machine din ta hau tana cewa,
"yara kam suna bayan uwayensu"

"ok naji ƴan mata"

ko kala bata ce masa ba illa nuna masa kwanar da zaya shi da tayi"

Duk yadda da Kabeer ya so yaja Salmat surutu tunda ya lura yarinyar parrot ce amma taki ta tanka masa.

A bangaren Salmat kuwa tunani take yadda za su kwashe da Adda ita da mama Kareema idan taji abunda ya sai da ta.

Dai_dai gidan da Salmat ta nuna masa ya faka har ta wuce ba godiya ya tsaidata,

"in badamuwa cewa nayi kimin magana da mai gidan don Allah"

har Salmat ta so taki amma da tayi wani gajeren tunani sai tace,

"ok badamuwa"

**********

Tunda naga ba saurarata Salmat za tayi ba na kama gaba,na lura ko wanda ya tsaya saurarenta shima ba ya da aikin yi ne.Duk da inajin ciwo a kafana amma na ɗaure har na isa gidan mama Kareema.

Ina yin Sallama Ramlat ta fito daga parlon su tana cewa,

"Oyoyo oyoyo,oyoyo Addarmu"

Haka mama Kareema itama ta fito ta tarbeni cikin farin ciki da kauna ya yin da suke tambayata ina Salmat ko ba tare muka zo ba na ce,

" a'a tana saman haya yanzu zata karaso"

mama Kareema ce ta lura da yadda nake taka kafana da zamu shiga parlo aiko arikice tayo kaina tana cewa....✍️✍️✍️

Zeesardaunerh ce

          ( ~Y'ar karamar su babbar su~👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

   comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋

WASU MATAN✔Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz