Page 37&38

194 25 0
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y

*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ

*Follow this link to join my* *WhatsApp group:* https://chat.whatsapp.com/Cd03QGzs8Wq2OR69JnNWuT

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk

*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/

*Page* 37~~38

   Bangaren Suhailat Kuwa ta raya daren ne tana charting sai da bacci b'arawo ya saceta gabanin subahin,dama ita bata bacci a dare saida safe domin dare lokacin charting ne na MANYAN MATA.
              Safe kuwa lokacin baccin tane sannan rana lokacin yawo da d'aukar wanka.Ita rayuwarta a tsare take,komi ta gama tsarashi ta yadda zata gudanar dashi (lol Suhailat Sarkin tsari🤣).

       Kiran sallar subahin ake tayi ako ina,muminai na kwarai suna hanzari domin su gaida Ubangijin su ya yin da baccin WASU MATAN yake k'ara dadi suna ji kamar kada a tada su,to hakanne ya kasance a wurin SUHAILAT,DR.AYSHA,MARYAMA Da kuma d'ai-d'ai kun mutane.

          Bangaren MARYAMA Kuwa baccin ta take sha cikin kwanciyar hankali ya yin da take mafarkin Kabeer ya k'ara dawowa hannunta sai yadda tayi da shi.

Kwankwasa kofar d'akinta Kabeer Ya yi amma shiru Suhailat Bata farka ba,dama ya san halinta na rashin yin salla a kan lokaci.

     D'akinta ya shiga da sallama a bakin sa,rashe-rashe ya cimmata tana baccinta hankalinta kwance sai murmushi take ko a jikinta kamar ba kiran sallah ake yi ba,bubbuga hannunsa ya yi akan hannunta amma bata farka ba saboda tsabar nauyin baccin da ke gare ta.

Makewayin(toilet)dake cikin d'akin nata ya nufa,ruwa ya d'iba akan tafukan hannayensa ya zo ya yar fa mata su a fuska,firgigit ta farka,wani kafurin mashahurin tsaki ta ja a lokacin da tayi ido biyu da Kabeer Wanda ya watsa
mata ruwan.Bai bi ta kanta ba ya juya ya fita yana cewa,
"ki tashi lokacin sallah ya yi"
tare a jan kofar.

       Tsaki ta kuma ja ya yin da ta k'ara shigewa cikin bargonta ta kwanta ta na cewa,
"ban ga damar yiba"

      Bayan ya dawo daga masallaci misalin bakwai saura(domin sai da rana ta fito sannan ya dago daga masallacin),wanka yayi ya shirya,dama duk lahadi yana hutawa ne sai ya barwa abokinsa kemis(chemist)d'in ya kular masa da shi.

Yunwa ce ke kwakular y'an hanjin sa dan haka ya shiga motar sa kirar civic ya nufi Runjin Sambo gurin mahaifansa.

   Cikin lilwantaccen harabar gidan yayi pakin(parking),cikin gidan ya shiga da sallama,ba kowa a tsakar gidan,part d'in mahaifiyarsa ya nufa.Kutsa kansa ya yi cikin palon tare da sallama ,zaune ya riske ahalinsa suna karin kumallo(breakfast)Alhaji Sa'id Wato mahaifinsa sai Hajiya Aisha mahaifiyarsa wato (Ummu)tare da k'annensa Batul Da Fatima.Da gudu su Batul Su ka zo inda yayan su suna oyoyo kamar yara kanana.Rumngumesu ya yi yana amsa ina kwana da suke yi masa .

WASU MATAN✔Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz