👩👩👧👧 WASU MATAN 👩👩👧👧
@2022~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
Story and Writting
by
Zainab Sardaunerh🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚
{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo⚜️©J.A.W📚🖌️
بسم الله الرحمن الرحيم
Da sunan Allah mai rahama mai jinkaiYa ALLAH YADDA NAFARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA KA YARDA NA KAMMALA SHI CIKIN KOSHIN LAFIYA.
SADAUKARWA
WANNAN LITTAFIN SADAUKARWA NE GA FADILA SANI BAKORI,HAFSAT ZUBAIRU SAMBO(Autar mama)AMINA MUHAMMAD BASO, MUMMYN SHUKURA,ASIYA MUHAMMAD,MAMAN AMATULLAH,MAMAN NUSAIBA,RAHMA KOISE,SISTER MIE AND HABIBTY NASMAH LOVE U ALL GUYS♥️♥️♥️
GODIYA
GODIYA MARA MISALI GA PHARTY BB,UMMU MAHIR,MOM ISLAM,UMMU ABDALLAH DA KUMA DAUKACIN MEMBERS NA JARUMAI WRITTER'S ASSOCIATION,MY DEAREST FAN'S SON SO FISSABILILLAH💓💓💓
BOOK 2
Page 35&36"Ina kika shiga ne Adda? mun dawo amma bamu gan ki ba"
"neman ku naje yi"
"ayya da baki wahalar da kanki ba,sai da muka ce miki abu ne zamu karbo mu dawo ba zamu jima ba"
"ban ji bane"
Amina tace "okey muje ciki ga su Rahama chan sun shigo.
HABIBA
Ta shiga ko kwanto waye ya yi mata wannan d'an karen dukan haka!
Duk wani sashe na kashi dake jikinta ciwo yake mata.A gurin da aka musu dukan ma sai da wani bawon Allah ya zo ya riskesu a gun ya taimaka musu.kwananta uku a Asibiti amma ba wanda ya zo du'binta daga cikin malaman Islamiyyar su sai wasu daga cikin yan ajinsu da sauran azuzuwa da suke mutunci da su.
A nan ne ma take samun labarin cewa Aleeya na Asibiti tun wanchan ranar sannan kuma cikin wad'anda suka je du'binta har da sahibinta Malam Nura.
Abun ya matukar ķona ranta ba kad'an ba,a kansa har sa'bani ta samu da mahaifinta kan ta nace sai an fito dashi daga police station batare da ya kwana achan ba amma duk da hakan ko tambayar ta bataji ance ya yi ba ballantana yasan halin da take ciki sai ma damuwar da ya nuna akan rashin sanin dalilin da ya hana Aleeya zuwa makaranta.
Wai dame yarinyar ta fita ne da ko kad'an baya ji baya gani indai akanta ne!Me yasa ba zaya so ta ba kamar yadda ta nuna tsananin sonsa ba.
Du'banta takai gun mama Kareema da ke sharar bacci,garin ya yi shiru ko ina tsit;tsaye take gun window na dakin tama kallon sararin samaniya da taurari WAYE WANNAN MUTUMIN? shine abunda yake mata yawo a Kwakwalwarta,kallon da yake mata na d'auke da sakon da ta kasa fuskantar sa,me yasa yake da muradin ganin fuskarta?wannan ne haduwarsu ta uku meyasa take jin chanjin yanayi da sauyin bugun zuciya a duk lokacin da suka kasance a tare?
yana yin da take ji na nuni da shine wannan Mutumen da ya shigo room d'in ta ya d'aukar mata wasika..WAYE SHI !A dai_dai wannan lokacin Haidar yana zaune a farfajiyar gidan sa saman resting chair idanuwansa na sama kamar mai ķi day'ar taurari,yana cikin Compuse a kwanakin nan,tambaya daya ce ke trending a mind d'insa " WACECE ITA "
Muryarta...Idanuwanta...gefen fuskarta na dauke da abun da brain di'n sa ya kasa aminta dashi, he's thinking me yasa bai cire wannan abun na fuskarta baki daya da yanzu an wuce gurin koma wacece zai gane..
Kwayar idanuwanta na d'auke da wani abu ko na ce wani sirri wanda kalilan ne ke da shi a cikin mutane masu muhimmanci a rayuwarsa.

YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...