👩👩👧👧 *WASU MATAN* 👩👩👧👧
@2021~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤
*Story and Writting*
by
*Zainab Sardaunerh*💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl
_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_
*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk
*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/
*Follow me on whattpad*
@Zeesardaunerh*Page* 57~~58
CIGABAN LABARIN
Da safe muna karin kumallo inna na bawa baffa labarin barawon da ya shigo jiya,baffa sauraronta kawai yake baice mata komi ba yana shan kununsa.
"malam kanajina kayi shiru"
"mi kike so nace miki ne Saude"
"Haka ma zakace ko, don ba kuɗin ka ya ɗauke ba"
Murmushi Baffa yayi ya dubi inna Saude yace,
"ai ke ma naga ba kuɗin ki bane!kuma naga waɗanda aka ɗauke wa sunce sun yafe,to miye na tada maganar"
"nima dai shi nagani BAFFA...
Wata hararar da inna Saude ta watsa mata yasa ta hadiye kingin maganar bata shirya ba,"Salamatu wlh...
Salmat ta katse ta da cewa
"Afuwan inna nayi shiru bazan kara magana ba,ko yanzu laifin baki na ne da baya iya yin shiru"Kyafci inna tayi ta tashi daga gurin da take tayi gun pampo, domin sharewar da BAFFA ya yi mata ya bata haushi sosai.
Sallama muka yiwa Baffa ya amsa tare da yi muna addu'a,karawa gaba nayi nabar Salmat tana fadawa Baffa wata magana bansan mi take cewa ba ta jima kafin tazo inda nake tana cewa mutafi,harara na galla mata cikin liqab dina Ina cewa,
"ai na'aza achan zaki tabbata"
"dá kuma zaki ganni anan yanzu,tunda azawa ne kika yi sauke tun bai tafasa ba"
"lallai yarinyar nan kin rainani, sai na saita ki zakiyi hankali,ni da ke ne"
Na fada ina kwafa, murmushi Salamat tayi tana tafiya tana cewa,"inna mun wuce amana addu'a"
Sallama na yiwa inna nima nabi bayanta.
Muna tafiya tana bani labarin cewa,
"inna ba ita ce tace akaiwa Baffa kuɗi ba nice kawai nakai masa ajiya da kaina""Dalili"
na tambaye ta"domin nasan amshewa kawai zatayi baza ta bamu ko kwandala ba"
"ta isa ne shiyasa"
"nima bance bata isaba ba ai"
"ok kuɗin naki ne baza ki bata ba sai kin tada mata hankali?"
"hakan da nayi shi zayasa tabar maganar kuɗin"
"Hmm ok kin kyauta"
nace mata ya yin da na dauke kaina daga kallonta ina mai cigaba da tafiya"baki tambayi mi zanayi da kuɗin ba"
"da kika tashi ai watar da plan dinki na sani ne"
"A'a"
"ok abar maganar"
"ai to Baffa ya sani"
"tambayar ki na yi ne?"
"ba ke kika tambaye ni ba amma yadace ki sani shiyasa,bawai da gangan na hanawa inna kuɗin ba a'a kawai ina so ne kiyi amfani dasu wurin yin JAMB ɗinkin kin ga lokaci ya yi kusa.kuma idan baki da JAMB ko nursing baza'a ɗauke ki ba, sai inbari inna ta cinye kuɗin ga banza ga kuɗin mun samu abunda muka jima muna rokon Allah ya kawo muna kuɗin kafin wannan lokacin na JAMB ya yi kisamu ki zana,ga waec na matsowa kuma sai an bincike ku bada kuɗi shiyasa kawai nayi wannan karamin acting domin nasan hakan kawai zai sa inna tabar maganar kuɗin.
"Allah ya taimaka "
"ameeen"
Salmat ta fad'a tana wucewa zuwa ajinsu,yau sun makara shiyasa ma basu taras da su Amina da bilkisu ba sun wuce tun ɗazu.***********
"Whattt?"
"tsaya ma wai,ni fa ban fuskanta ba Dr.Abdull what are trying to said(mi ka ke ko karin cewa ne)"
"Abunda kunnuwanki suka jiye miki"
"keep joke a side zuciyata na iya bugawa, please ka gayamin gaskiya"
"dama ina miki karyane"
"No impossible wlh,hakan bazai ma yiwu ba"
"kinsan Allah kin bani dariya wlh, domin yanzu haka da wuya A.M ya kasance a Abuja kinga yau juma'a yana yiwa ya kasance ya jima da wuce India kuma dawowarsa ba nan kusa ba"
Tsayawa kallonsa tayi tamkar Tv ta rasa abunda zata furta,gabadaya tarasa kalmomi a bakinta,juwa kawai tayi ta wuce cikin motar ta ta kifa kanta a stiyarin motar ta lula duniyar tunani;tun ranar talata take faman nemanrA.M har a yau jum'at.
A koda yaushe zata zo ta tsaya lokacin shigowar sa asibiti amma baza ta ganshi ba hakama lokacin tashinsa kuma ta yi ta kiran wayarsa amma baya ɗagawa duk abubuwa sunbi sun jagule mata takasa hakuri saida ta tuntubi Dr.Abdull ashe wai ma A.M baya kasar bama garin ba bai sanar mata ba ita ya bari da wahalar zuciya da nemansa.
Ajiyar zuciyata ta sauke a ranta tana tambayar SHIN MINE NE MATSAYINA AGUNSA_ ? _MIYA ƊAUKE NI NE ?MIYASA YAKE AZABTAR DA ZUCIYATA DA RUHINA!
Ina bukatar waɗannan amsoshin daga bakin ka,zan jira ka har ka dawo kuma bazan daina sonka ba domin sonka numfashi na ne kuma jininane ko mutuwa sai dai ta ɗaukeni da soyayyar ka_. _zanyi jinyar zuciyata har ka dawo Aliyu domin wannan karon bazan bika ba amma zan jira ka!zan jira ka.Jan motar ta tayi ta wuce gida ranta na kuna zuciyarta na begen sahibinta.
( Allah baki hakuri da juriya mrs wahala 🤣🥺)
*********
Ko a yau kacha-kacha sukayi da Maryama, ya taka mata burki na kwarai ya fada mata magangannun da suka soya mata rai da zuciya domin ya lura iskancinta kara yawa yake amma zai yi maganin tane yana ganin shawarar abokanin sa zai ɗauka kila tayi hankali.
Wani lokacin yana mamakin wai ma ya akayi ya aureta?ina ya ja jibowa kansa mugun iri irin wannan ?
Sam Maryama bata da tarbiya kuma ita da kunya da sunyi hannun riga sam Maryama bata dace da macen auran shi ba,ya hakan ta kasance? amma ba mai bashi amsa...✍️✍️✍️Zeesardaunerh ce
( Y'ar karamar su babbar su👧🥰🤩)
# _comment_
# _like_
# _share_Comment and vote d'inku shike Karamin kafin guiwar typing💋

YOU ARE READING
WASU MATAN✔
Short Storyبسم الله الرحمن الرحيم WASU MATAN Littafi ne da ya kunshi halayen matan mu na yanxu ko nace matan zamani,halaye masu kyau da ma akasin su. Wannan littafi ya kunshi Kishi,kiyayya,tausayi,dama sauran su. INA ROKON UB...