Page 27&28

189 31 0
                                    

👩‍👩‍👧‍👧 *WASU MATAN*  👩‍👩‍👧‍👧
          @2021

~Mallakar Zeesardaunerh~💜🖤

*Story and Writting*
           by
*Zainab sardaunerh*

   بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai 📚

         _________________      
       ______
🅙︎𝗮𝗿𝘂𝗺𝗮𝗶 🅦︎𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿𝘀 🅐︎𝘀𝘀𝗼𝗰𝗶𝗮𝘁𝗲𝗱📚🖊
https://www.facebook.com/101679598253281/posts/101680068253234/?app=fbl
_Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa illmantarwa, nishadantar tare da fadakarwa da jama'a bisa harshen hausa_

                 🏔🅙︎🅦︎🅐🏔
*Follow this link to join my* *whatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/LXIF4UAUqeGCWONjQCrG4Y

*Follow this link to join my* *WhatsApp group* : https://chat.whatsapp.com/J7fqJ9AqzNTGfSryVEm4dZ

*Follow this link to join my* *WhatsApp group:* https://chat.whatsapp.com/Cd03QGzs8Wq2OR69JnNWuT

*Join me on Telegram*
https://t.me/joinchat/yZ0tHN29JA4wMzZk

*Join me on Whattpad*
https://www.wattpad.com/

*Join me on facebook*
https://www.facebook.com/groups/465546087828286/permalink/465546091161619/

*Page* 27~~28

Cikin muryar da ke nuna bacin rai da hasala take cewa"bansani ba..!koma inda ka fito..'
cikin dan hanzari ya matso kusa da ita tare da fad'in"Umma lafiya dai ko?"
cikin tsawa har su mama na jiyota take cewa"nace bansani ba ka koma inda ka fito"
"kiyi hakuri Umma Idan na bata miki rai"
"naki nai hakurin,nace nakiyi dan  babanka,tashi ka fitarmun a daki ka koma gurin wad'anda suka fini gareka"
"subhanallah, Umma ya kike fadar wannan kalma..ni ba wacce tafimini ke a duniya domin ke uwa tace har abada banda kamar ki"
"kasan da hakan ka ke bijirewa maganata?ai na d'auka ka chanza wata uwar ne"
"Allah baki hakuri umma amma ni bansan na sallake umurninki ba,ina mai kara neman a fuwarki"
"ina ko zaka sani tunda an riga an shanyemini kai,ana kokarin rabani dakai"
"Umma zato zunubi koda ya zamto gaskiya..ni bansan me mama tamiki ba da baki kaunarta,ko ke kanki umma kinsan mama mutuniyar kirkice"
"dallah rufemin baki!
nice zaka fadawa wai mutuniyar kirkice dan ka renani"
"a'a bahakan nake nufi b.."bai ida maganarsa ba ta tare hanzarinsa da cewa "mi kake nufi to"
shiru yayi dan bayasan tana fada yana fada hakan bai dace ba,ci gaba tayi da balbalin jidalin nata,shi kuma yayi zaune yana sauraranta har tagama sannan ya sake bata hakuri , fita batunsa tayi (saboda duniya ta tsani tana yiwa mutum fad'a yana bada hakuri, shiyasa ta ke cewa su Firdausi Munafukai bcox da ta fara hayagagarta na neman fada mama ta share ta sai ta koma kansu to abunka da bahaka suga mahaifiyarsu na yiba sai su dinga bata hakuri shine koyarwar mamansu,ako da yaushe tana ce musu koda suke da gaskiya mutum yace sun masa laifi to su bashi hakuri)
        Kan bacin ran da take ciki ko maganar da tayi niyar yi masa mantawa tayi.
  Cikin rashin sakewa da maganar da zai mata yace"to ni umma zan wuce,kuma Azeema Tace tana gaida ke"
kara tamke fuska tayi "Allah ya bada sa'a,ita kuma bana amsawa   ai tasan gidan zata iya zuwa ta gaidani amma saboda sabar munafunci da ta gada a wurin uwarta ace ina matsayin Uwar mijinta ta kwashe wata biyu rak ba tazo ta gaidani ba"
"Abubuwa suka yi yawa umma amma insh'allah zata zo"
"bana bukata"
"Allah ya huce zuciyarki ni dai na tafi kar na makara ana jirana"yace tare da fita daga dakin domin tabass idan yatsaya korafin umma bazai kare ba,itafa da kanta tace masa shida Azeema bata kaunar sake ganinta agidan in har wai inda take tazo to bata bukata,ba yadda baiyi da itaba amna ata fir tace kar ta sake ganin kafar Azeema a gidan.

    A bangaren mama Hawwa kuwa Abubakar na shiga dakin Umma ta juyo da kallonta kan Aisha,rarau da ido Aisha Tayi tareda game hannunta biyu wuri guda alaman ban hakuri,kyafci kawai mama tayi tana cewa"Allah ya ce ceki wlh,sbd kin rainani kike cewa ya tambaye ni ko?atunaninki sai na fada masa karya, nace masa maganar ki gaskiya ce"
"umm mama gaskiya kin fison yaya Ab damu,gidan nan ma nidaya ce ba kyaso"
"ya fiku jin magana ta shiyasa,ke kuma ba kyaji idan nace karkiyi sai kinyi"
"Allah mama ina jin maganarki wlh,kawai dai abunda Umma take miki ne banaa iya jurewa"
"ai idan kika tanka mata in tanayi nima wani lokacin zaki tankamin domin duk d'aya muke,yadda nake mahaifiya a gareki hakan itama domin matar baban ki ce"
"Hmm walle umma ba daya kuke  ba"
Buge mata baki umma tayi har saida tace"wash Allah na wayyo babana umma ta ciremin lips dina"
"dallah masa ki bani guri maraji kawai,ke baza a fada miki abu kice to ba ko?duk saina yanke bakinnnan da baya jin magana"
matsar hawaye ta dinga yi ana cikin han ne Abban Khaleel ya fito yana cewa mama "mama na tafi kasuwa amun addu'a"
"to Abubakar,ubangiji Allah ya tsareka gabanka da bayanka ya bada abunda a ka je nema"
"Ameen ameen mamana nagode"ya fada yana fita daga gidan.Umma Hadiza da tayo hanyar waje domin ta gani shin ya tafi ko ya tsaya,amma kaf duk maganar da Abban Khaleel yayi a kunnenta sannan kuma taji addu'ar da mama tayi masa,tsaki tayi ta koma kan kujerarta ta zauna tana tunanin mi za ta yiwa  mama Hawwa'u ta kona mata raine,a ganinta komai tayi mata bata nuna taji balle ya b'ata mata rai,wani tsakin ta koma ja cinkin ranta tana cewa "kenan duk magangannun da ta fadawa Abban Khaleel tana daga murya dan mama taji kenan duk a banza!hmmm ta sauke numfashi ta nufi kuryar dakin ta.

Lokacin da ya isa kasuwa ma ya taras da mutane da dama na jiransa,ciki ya shiga ya ci gaba da harkar kasuwancinsa duk da ransa baya masa dad'i in ya tuno halin mahaifiyarsa.

Salmat bata jima ba ta kawomin kayan magin muka cigaba da girkin a tare shiyasa ma aikin yayi gudu.
      Inna Saude na gani bata hanata ba saboda bata mana sanya indai fannin girkine cewa take "girki shine mace"shiyasa ma take bari salmat na d'an temaka min.
      Amma a bangaren gyaran gida to bata yarda Salmat Ta tayani ba duk da cewa kuwa ta iya,cewa take" yarinyace bata isa fara irin wannan ayyukan da nake yi ba"sometimes bana cewa komi,to mima zance ,indai zanma inna Saude ayyukan da ta d'auramini kamar nice matar gidan to zamu zauna lafiya da ita.Ko a da ma da muke samun sabani da ita dan kawai Bappana yace "wannan ayyukan sunmin yawa" lokacin bakina shekara shabiyar amma tace "atafir in ya na so mu zauna lafiya nida ita to kawai ya barni nyi ayyukkan"ba dan rainai yaso ba ya hakura, yasan cewa wuya b'ata kisa,kuma horar dani ne take domin halin rayuwa,Allah kad'ai ne yasan ina ne zan zauna in nayi aure.

Bayan mun kammala tuwon ya rage saura miyar dake kan murhu idan ta ida inna Saude Ce zata sauke,dama hakan mukeyi wani lokacin ,wanka naje na fara yi sannan salmat tayi,mu ka yi shirin islamiyya.har muka fito a gidan muka nufi islamiyarmu inna Laure bata koma gidanta ba.Kamar kullum kowa ajin sa ya nufa,Salmat Da Bilkisu Suka nufi ajin su nikuma da Amina muka nufi namu.
   Da'aka tashi kowa ya nufi gidansu.

     Haka rayuwa ta ciga ba da tafiyaa bangaren su Aliya Da ga aiki sai zuwa school and islamiya,fadan inna Saude na nan ba abunda ta sauya Salmat Kuwa bata fasa tsokana ba.

    A kwana a tashi ba wuya a wurin Allah,yaune ummar maryama ta cika  kwana biyar da tafiya nijar gurin bokan su,kuma har yanzu zaman doya da manja ake a cikin gidan tsakanin maryama da kabeer,cikin ma yana d'aurewa ne domin d'an maryama bata fahimta bane a cikin ayyukan da suka yi kan kabeer din ba wanda ya warware illa na rabashi da mahaifansa da sukayi ,har yanzu akwai zazzafar soyayyar maryama acikin zuciyarsa tana azarzalarsa amna da yardar ubangiji in yayi addu'a ya tofa a ruwa yasha sai abun ya lafa masa abunka da sihiri.
Maryama ma ta jiga ta domin dama itace keson kabeer din shi ba ita ya keso ba,gata kuma ta kasance cikin jinsin mata masu yawan bukata wannan shine dalilin da yasa ta jikata da yawa Adalilin d'adewar da ummanta ta...........................................✍️✍️✍️

    *Zeesardauner ce*

         ( ~Y'ar karamar su babbar su~ 👧🥰🤩)

# _comment_
# _like_
# _share_

*comment and vote d'inku* *shike karamin karfin guiwar* *typing* 💋

WASU MATAN✔Where stories live. Discover now