Tuwon madara

189 11 5
                                    

TUWON MADARA

INGREDIENTS:
1.Madaran gari rabin loka
2.Sugar gwangwani biyu
3. Leda

PROCEDURE: A samu ruwa kamar rabin kofi a zuba a tukunya sai a juye sugar, a barshi yayi ta dahuwa har sai yayi kauri. In kika dangwala zaki ga yana yin ďanko kamar na aya mai sugar.
Sai ki ďauko madarar kina juya wa kina zubawa, idan ya shige duka shikenan in kuma bai shige ba sai ki bar sauran. Amma kada yayi qarfi sosai kada ki ce dole sai duka madarar ki ta shige.
Sai a juya bayan tray a shimfida leda a kwashe kafin ya fara yin brown, kada kice zaki barshi bayan kin juya, yana hade wa ki sauke. A samu mara ko muciya (kneading stick) a sa shi yayi plat dai-dai kauri ko faďin da kike so. Shikenan sai a yayyanka shape ďin da ake so.
Akwai tuwon madara mai kwakwa plz idan akwai wacce ta iya ta koya mun ta comment. Saboda ina ta tunanin a cikin madarar ake zubawa kafin a zuba ko kuwa a sugar ne.
Ni fa bana son baki na ya zauna shiru ba ya aiki Nafi son tuwon madara akan gullisuwa, kefa?

Kece Mowa Where stories live. Discover now