Chapter 3&4

425 26 3
                                    

*YARINYA MAI TAƁAR GAZA*

     Typing✍️.

STORY AND WRITING
           BY
*Zainab Habib [Mom Islam]*

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

Telegram links  https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Wattpad momislam2020

FREE BOOK🥰

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*.

Page 3 & 4

  Shima da gudu ya bisu amma ya kasa kamasu , haka dai ya haƙura ya dawo kan dogon bencin da yake zaune yana maida nunfashi .
Na shiga uku kazar dubu biyu shegiyar nan ta zunduma , cewar Lawali  harda ƴar ƙwallar sa yana tuna ɗan jarin nasa dabai taka kara ya karya ba .
Su Aisha basu tsaya ko inaba sai a shagon wani mutumi mai siyarda  goro , sanin shidai bashida abinda zasu cuceshi kuma ko sun zo baya korarsu yasa suke yada zango anan .
suna zama suka fito da kazar lokacin mai shagon ma ya rufe ya tashi yace " musu insun gama su shigar masa da buhunsa cikin rumfa ,
Amsawa sukayi da to
Suna shirin fara rabo sukaji hirar wasu samari suna cewa "
Ai wlh yanzu kazar Lawali tazamo wa ƴan mata masifa sai dai amare suci dan wlh duk budurwa ko saurayi yaci kazarnan to ranar saiya gane bashida wayo .
Haɗa ido su Ummi sukayi gabansu ya fara faɗuwa dukda basusan aure ba ,sunajin labari a gurin ƴan matan islamiyarsu sunsan wani abin daga ciki ,
ƙudun dune kazar sukayi Aisha ta miƙawa Ummi tace "barin samo leda zanzo in gaya miki inda zamu kai.
Jikin Ummi banda rawa babu abinda yakeyi, gashi har ana kiran sallar magrib Aisha bata dawo ba , idanunta duk sunyi ja  tsabar tsoro,
Hango Aishan da tayi ne tana tahowa hankalinta ya kwanta ,
cewa Aisha tayi , ke Ummi Lawali yakusa kamani hmm badan Allah y temake ni ba aida nashiga uku ,
inayin kwana na janyo leda a shagon Hambali kawai ya taho da gudu yana shirin cafkemin mayafi , tana maganar tana maida nunfashi .
Ganin fuskar Ummi da alamun fushi yasata dakatawa da bata labarin tace " lafiya kuwa Ummi ?Hawaye ne suka zubo daga fuskar Ummi tace " yanzu ina komawa gida wlh Ummana sai ta dukeni gashi dare yayi ,
Dariya Aisha tasa kana tace " aiko duka baya kisa a daki fata abar fata karma kiji tsoro yanzu zomuje kawai ,
Ta miƙawa Ummi baƙar ledar tace " sako kazar anan muje kiga ,
Ummi ta saki ranta amma yawunta na tsinkewa , kasa haƙuri tayi tace " Aisha ina zamukai kazar ? nidai wlh a raba abani tawa ,
Aisha da tafi Ummi wayo tace " lallai kinason a kasheki a gida wanan kazar tanasa hauka , zaro ido Ummi tayi kana tace " taɓɓ gara da kika faɗamin yanzu wa zamu kaiwa ? Aisha ce ta ƙyal ƙyale da dariya tace "  budurwar yaya Zakari Fiddausi ...!

Muje zuwa fans ina gwada yanayin karɓar littafinne inkunason typing mai yawwa to kuyi comments inji daɗi 🥰.

MOM ISLAM

YARINYA MAI TAƁAR GAZAWhere stories live. Discover now