52 & 53

122 16 2
                                    

*YARINYA MAI TAƁARGAZA*

*Zainab Habib (Mom Islam)*

*Wattpad @momislam2020*

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 52-53*

Harma ya hango ranar auran su kasancewar in zaiyi misali yana ajiye Aisha a matsayin babbar mace , Ammi ni zan fita  Khamis ya faɗa, to a dawo lpy my son , Ammi taci gaba da duduba kayan sbda taga abinda babu .
Washe gari tun safe Afnan da momynta suka iso kana ganin fuskar Afnan kasan bata cikin kwanciyar hankali ,a palo suka yada zango ƴar aikin gidan ta cika gaban su da kayan  ciye ciye , fitowa Ammi tayi cike da farinciki ta dubi momyn Afnan tace " munata shirye shirye ,dariya momyn Afnan tasa tana cewa" munada bidiri ai zuciyar Afnan kamar an buga mata guduma tsabar baƙinciki da tasan wanan maganar zata zo ta tarar da batayi gigin zuwa gidan ba , amma tunda ta faɗa wa momynta dalilin dawowarta gida babu damuwa komai zai dai daita amma tasan akwai ƙura a gaba sbda koda sau ɗaya Khamis bai taɓa nuna alamun kulawa da ita ba .janyo akwatunan momyn Afnan tayi ta fara duddu ba kayan kasancewar Ammi tabar gurin yasa Afnan matsowa tace " wlh momy wanan kayan ba ƙaramin kashe kuɗi sukayi ba ,hmm momyn Afnan ta nisa tare da cije leɓe tace " wanan uban kaya kamar wacce ta fito daga gidan wani hamshaƙi? indai ko ina nunfashi sai kin auri Khamis wlh wanan alƙawari ne na ɗauka . farinciki na ya baiyyana a fuskar Afnan ,jin motsin tahowar Ammi yasa su yin shiru sukaci gaba da duba kayan ,Ammi na isowa momyn Afnan tace " oh my sister kinyi aiki fa Allah ya sanya alkhairi amen Ammi tace " kana ta nemi guri ta zauna sukaci gaba da tattauna abinda zai wakana.
Washe gari da yamma Khamis ya shirya zuwa gurin Aisha wani lallausan yadi ya sanya mai tsadar gaske wanda ya fito da ainihin kyansa gashin kannan yasha gyara hannayesa suna ɗauke da tsadaddun zobuna wa inda suka ƙara ƙawata kyansa fitowa palo yayi yana ƙwalawa Ammi kira , da sauri Ammi ta fito tana washe baki tace " kai my son karfa kasa Aisha tace " da wancan da wanan akwai ban banci suka kwashe da dariya , Ammi sai ma ranar da na kai mata chocolate kinga murna harda rawa cemin take wai balarabe , dariya Ammi ta ƙara sawa tace " ai kana kama dasu shiyasa , to Ammi ayi min adu'a zan tafi hira ,ya rufe fuskarsa , cike da kulawa Ammi ta dubesa tace " my son Allah ya tsaremun kai a duk inda kake. amen Ammi Khamis ya faɗa kana wuce, kai tsaye parking spice ya nufa ya ɗauki motarsa ya fice yana jin wani farinciki , driving yake yana murmushi shi kaɗai yasan inda yake ji a ransa , yana isowa unguwar yai parking a ƙofar gidan su , yaro ya hango da bazai wuce sa'anta ba ya aikesa ya kira masa Aisha , bayan yaron ya shiga bai kai ga cewa " komai ba sai gata ta fito da uban gudu ta rungumeshi , dariya yaron yasa yace " Aisha wanan ɗan uwanku ne? dariya Aisha tasa tace " kai wanan saurayi na ne baka ganshi kamar balarabe ba ,shidai Khamis na tsaye yana jin hirarsu hanunsa a na Aisha gyaɗa kai yaron yayi tare da cewa " kinji daɗi natafi aikana ya wuce " da gudu , ko ka goyani kokuma in koma gida wlh ,Aisha ta faɗa tana cuno baki , murmishi Khamis yayi da har dimple ɗinsa ya loɓa yace " my Esha zan goyaki amma ba yanzu ba ko kinaso mutane suyi miki dariya? girgiza kai tayi tace " to ina tsaraba ta , bugar goshinsa yayi da tafin hanunsa alamar mantuwa ya dai daita nutsuwarsa da cewa" zan siyo miki amma gaya min me kikafi so , alewa da chocolate da tuwon madara ,Aisha ta faɗa tana tsalle ,tsayawa kallonta yayi yasan she is very young amma a hakan yake da buƙatarta , tana ta surutanta bai kulata ba dan bai san tanayi ba , taɓosa tayi tana cewa " balarabe ciromin waccan ƴar bebin ta cikin motarka , sai a lokacin yaji abinda take cewa" taɓɓ Khamis ya faɗa a cikin ransa , me zakiyi da ita? wasa harda goyo kuma in ɗinka mata kaya , dariya Aisha ta basa dan har ga Allah tana sashi nishaɗi , leƙawa ta cikin motar yayi ya ciro mata babyn ya miƙa mata ,tsalle ta doka tace " kai balarabe ina sonka sosai ta rungume babyn , wani daɗi ne ya kama Khamis a dole kalmar so ta fito daga bakin masoyiya, rugawa gida tayi da gudu ta leƙo tace " balarabe in zaka sake zuwa ka taho min da kayan ƴar bebi dan Allah ta ƙara da gudu , ya daɗe a gurin yana dariya daga ƙarshe ya tada motarsa ya bar anguwar.
Tunda Ummi ta koma gidan yaya Zakari kewar Aisha ke damunta shiko yayan kwata kwata Aisha ta fice masa daga ransa.
Yunwar da ta addabeta ne yasa ta fita kitchen dan bataci abincin dare ba , ƙwai ta fasa har guda goma ta tsiyayo mai da maggi da albasa ta hau suya , lokacin yaya Zakari da anty Fiddausi na zaune tana kukan amai ya dameta , jiyo ƙamshin suyar ƙwai yasa ta tashi daga zaman da take tace " itafa ƙwai zataci kuma soyayye,  ya fara jin bacci ya fito ya nufo kitchen ɗin  jin kitchen ɗin ya gaure da ƙamshi kuma na ƙwai yasa shi dube dube kuma gashi risho da zafi , bai gama shan mamaki ba har sai da yaga babu ƙwai ko guda ɗaya alhalin yasan jiya da ragowar guda goma , a hanzarce ya dawo ɗakin anty Fiddausi haskata yai da fitilar wayarsa kasancewar yanzu suka ɗauke yace " naga babu ƙwai fa ina aka kai ?" wlh ban sani ba nikam, ni da nake ɗaki kwance ko fitowa banyi ba , mamaki ne ya kuma kama yaya yai ƙwafa yace " koma dai menene wataran Allah zai haɗani da mai satar nan .
Ummi na ɗaki zaune ta sa tiren ƙwai tana ci tana gyɗa kai daga ɗakin tana jiyo surutun su yaya amma tayi burus , sai da ta cika cikinta fam sanan ta tura ragowar gefen jakarta , goge hanunta tayi da zanin gado ta haye ranta fesss bacci mai nauyi yai awon gaba da ita.
Washe gari Ummi sai fama da tusa take da ta zauna zataji tusa ,suna zaune da anty Fiddausi taji wani uban wari ,toshe   hanci anty Fiddausi tayi tace" haba Ummi kamar kinci ƙwai? wuli wuli da ido Ummi ta shiga yi tana  shirin tashi ankara da alamun rashin gaskiya yasa  anty Fiddausi lura da ita , zo nan anty Fiddausi ta ƙwala mata kira , ƙin zuwa tayi ta ɗauki buta tare da shigewa bayi , tana shirin yin fitsari taji gudawa ta taho , zaro ido Ummi tayi tana cewa" na shiga uku wlh na mance ƙwai na sani gudawa , kuka ta fara a bayn gida tare da cewa" yanzu wazai siyamin maganin kashi ?" haka ta miƙe ta jiƙe da zufa tayo waje ,anty Fiddausi dake zaune bata tashi daga inda take ba ta daka wa Ummi tsawa , a firgice Ummi ta saki tusa tana jin gudawa na shirin zubo mata tayi bayi da gudu tana kuka , dariya ma abin yaso bawa anty Fiddausi hakan sai ya tuno mata da nasu kashin da sukayi , ganin shiru shiru Ummi bata fito ba yasa anty Fiddausi miƙewa ta nufi ɗaki ta kwanta .
Washe gari .
Zaune Aisha take ta haɗa kayan wasanta da ƙyallaye tana yankawa da reza , mama dake zaune kusa da ita ta girgiza kai dan tana tausayin Aisha kasancewarta yarinya ƙarama , lafiya mama kike kallo na ?" Aisha ta faɗa tana yiwa ƴar bebinta rawa , lafiya Aisha mama tace " kana ta miƙe hawaye na zuba a fuskarta ta nufi ɗaki.
Aisha taga kukan da mama ta keyi bata bita ba ta cigaba da zama har shigowar malam , kasancewar yanzu malam basa faɗa da Aisha , yawwa malam ga mama can a ɗaki tana kuka na tambayeta tace " wai tsire takeson ci , Aisha ta faɗa tana jujuya ƴar bebi , zaro ido malam yayi kana yace " tsire ko to inma sawa kuɗina ido takeyi tun wuri ta fasa dan wlh ba kuɗin banza gareni ba , dariya Aisha tasa tace " malam wasa fa nake maka , kinci gidan ku malm ya watsa wa Aisha daƙuwa , turo baki Aisha tayi tace " amma fasa auran bazan aureshin ba ta murguɗa baki , tsugunawa malam yayi cikin muryar lallashi yace " habba Aisha na karki ƙara faɗar hakan banaso zomuje in siya miki tsire kici , da sauri Aisha ta miƙe ta nufi gurin malam ya riƙe mata hannu suka fice , da fitarsu waje wasu tsofaffi suka fara gulmar su malam suna cewa " wlh auran jari zeyi mata dubi ƴar yarinyar da zai aurar taɓ ,karab a kunnen malam amma burinsa kar Aisha taji duk da ba lallai tasan ko me suke nufi ba , haka dai suka wuce zuciyar malam babu daɗi  ya nufi gurin mai tsire , Aisha ta mance da sun taɓa zuwa satar tsire ita da Ummi, gaisawa malam sukayi da Lawali bayan ya amsa yace " malam kazo  siyan tsire ne ?" eh malam yace " na ɗari biyar zaka bani jikin lawali na rawa ya fara zuge tsire ,hango Aisha da yayi ne yasa shi tsayawa yana nazarin kamar itace tayi masa sata ita da wata yarinya , tabbas ita ce lawali ya faɗa a fili , sarai Aisha ta gano komai amma batada damuwa tunda akwai malam , malam wanan ɗiyarka ce ?" Lawali ya tambaya eh malam yace "yana washe baki masha Allah Lawali ya faɗa yana yiwa Aisha kallon inna riƙeƙi zakisha wuya, bayan Lawali ya gama sawa malam ya miƙa masa , kuɗin malam ya basa kana suka wuce , suna isowa gida malam yaba Aisha leda ɗaya yace " ƴar albarka kici ki ƙoshi ki samma mamanki ɗan kaɗan , maƙe kafaɗa Aisha tayi tace " nidai ni kaɗai zanci ka bani in kai mata a naka ai inaji kace wa Lawali ya  sa naka da yawa , zaro ido malam yayi yace " duk wanda ya aureki wlh ya aurarwa kansa sai kuma yai shiru , mama da ta fito domin ɗora girki ta gansu da leda a hannu , ko saurarar su batayi ba tunda Aisha yanzu ba jin maganarta takeyi ba , ko yazo bazan fita ba yasin Aisha ta faɗa tana cuno baki , ganin abin zaiyi masa yawa yasa malam shigewa ɗaki yabar Aisha a gurin.
Ummi ta gala baita bata ma iya fitowa wunin ranar yaya Zakari a gida yayi shi kasancewar baya  jin daɗi sosai  , lura da rashin jin motsin Ummi yasa ya leƙa ɗakin nasu , ganinta yayi kwance rufe da bargo sai rawar sanyi take ga wani uban wari da yayi masa sallama , innalilahi Ummi Ummi ....ya kira sunan ta da ƙarfi , shiru bata amsa yasa shi shafa fuskarta jikinta yayi sanyi ga wani irin nunfashi da take fitarwa da sauri ya fice ya nufi shagon siyarda magani na nan anguwar tasu ya kira mai chemist ɗin , tare suka taho cikin sauri suna shiga ba'a tsaya ɓata lokaci ba aka sanya mata drip, bayan yasa magunguna a ciki yayi wa yaya Zakari sallama yace " in ya ƙare ka kira number ta , to yaya Zakari yace " jiki a sanyaye , fitowa anty Fiddausi tayi ta nufo ɗakin ranta a ɓace babu ko sallama ta bankaɗo labule tana ƙarewa yaya Zakari da Ummi kallo , cikin masifa tace " andai ji kunya ka rasa wacce zaka so sai ƴar cikinka , da mamaki yayan ke kallonta dan da farko bai fahimci me take nufi ba amma yanzu kam ta fahimta , ki nutsu Fiddausi , bazan nitsu ba kazo ka ɗorata a cinya kamar wata matarka koni ynzu baka yimin haka , anty Fiddausi ta faɗa tana riƙe da ƙugu , dariya ma taso bashi banda hauka da yarinya ƴar shekara goma sha ɗaya za'ayi kishi aiko sai da ya dara ya kwntar da Ummi yaja hanun anty Fiddausi sukayi waje , kai tsaye ɗakinsa ya nufa da ita ya zaunar da ita kan katifarsa , kina nufin son Ummi nake ko me ?" idanun anty Fiddausi na fitar da hawaye tace " eh man inba so ba ai naga ko shiga ɗakinsu bakayi , shitttt....ki fahimceni badan larurarki ba babu abinda zai sa na ɗauko Ummi tausayinki da nake ji yasa hakan me zanyi da Ummi ? ki kiyaye bana son jin wanan zancen ya ƙara fitowa daga bakinki , kingane ko ?" gallah masa harara tayi ta fice tana magana ciki ciki.....!

Fans kuyi haƙuri na aihu ne shiyasa kuka jini shiru .

YARINYA MAI TAƁAR GAZAWhere stories live. Discover now