chapter 34

193 21 1
                                    

*YARINYA MAI TAƁARGAZA*



*Zainab Habib [Mom Islam]*

*Wattpad @momislam2020*

*AREWA WRITER'S  ASSOCIATION*

*Page 34*

Mamakin hali irinna Aisha anty Fiddausi keyi , shikam yayan da ya gaji da kwanciya ya miƙe ya dafa bango ya nufi ɗakin su Aisha , zaune ya sa mesu suna ta shan tea , suna ganinsa suka gai shesa bayan ya amsa yace " Ummi kuzo ku kira mana likita a chemist ɗin ƙofar gidanan , to suka ce kana suka miƙe dan zuwa kiran , hijab suka ɗauka suka fito , tun a hanya Aisha ta fara tunani inhar wanda ya bata maganin kashi ne to bazata bari yazo gidan ba dan asirinsu zai tonu , Ummi da kejin surutan Aisha itama tsoro ne ya kamata dan tafi Aisha tsoro , suna zuwa bakin chemist ɗin suka tsaya ganin wani yaro yazo wucewa yasa Aisha tarar shi tace " dan Allah akwai wani shagon siyarda magani bayan wanan ? eh yaron yace " ga shican na gefe mai farin fenti , tafiya sukaci gaba da yi suna surutunsu , suna isowa suka samu akwai mutum ɗaya duban Aisha Ummi tayi tace" maganin kashin zamu kuma siyowa , Aisha da  kamar jira take tace " kice dai mu kashesu mu huta kawai inba haka ba kina ganin ko tafiya basa iya yi , cikin tsananin tsoro Ummi tace " idan asirinmu ya tonu fa , tsalle Aisha tayi ta cukumo wuyan hijab ɗin Ummi tace " da naci uwarki babu mai tonawa sai ke shi yasa na dena shiri dake , haƙuri Ummi ta shiga bawa Aisha daganan suka shirya mai chemist ya leƙo yana ganin kamar suna shirin faɗa yace " in faɗa zakuyi ku tashi a nan kuyi gaba , gurinka aka aiko mu Aisha tace " tana murguɗa masa baki , togani cewar mai chemist "wai kazo ka ƙarawa yayana da anty na ruwa sun kwana suna gudawa ko tafiya basayi nice nayi musu girki ma sunanan a palo kamar an zuba shanya , tunda tafara magana yake kallon bakin tsiwarta , wane gida ne ? mai chemist ya tambaye ta nuni tayi masa da hannu , yace " gani nan , komawa gida sukayi ita da Ummi suka nufi ɗakin anty Fiddausi , har yanzu suna zaune babu wanda ya tashi daga inda yake ga kuma kiɗa na tashi , kashe waƙar Aisha tayi ta dubi yaya Zakari dake binta da ido tace " gashinan zuwa , to yayan yace " suka fice ita da Ummi , Aisha ce ta hau buga ciki tana kiran yunwa  , to muje mu ɗumama shinkafar nan mana , Aisha dake nufar hanyar kitchen tace " wlh ƙwai zamu soya yau ɗinnan sai dai suji ƙamshi , ɗibo ƙwai tayi guda bakwai da magi da mangyaɗa , ta ɗauko abin suya tana gama suyar ta juye musu a plet Ummi tace " barmin mangyaɗan zan soya dankali , to yi sauri ki fere cewar Aisha , Ummi na ferewa Aisha na suya haka gidan ya kaure da ƙamshi har waje , ƙwala mata kira yaya Zakari yayi tana jinsa tayi shiru a hankali suka kashe risho suka koma ɗaki , ana zuwa aka hau rabo suna ci suna shirin muguntar da zasu yiwa su yaya da zarar sun warke, sallamar da sukaji ne yasa Aisha dake bakin ƙofa ta leƙo dan taga ko waye , tana ganin sa tace "ka shiga suna ciki , haka ya wuce ya samesu a kwance yaya Zakari a ƙasa Fiddausi a kan kujera, bayan sun gaisa yayi musu ƴan tambayoyi ya ciro kayan aikinsa ya fara sanya musu ruwa na tafiya da gudu , yana zaune yana jiran ƙarewarsa yasa musu wani , wanan da yasa ne yake tafiya a hankali , ficewa yayi yace " yanzu zai dawo , Aisha na gama ci ita da Ummi suka tara kwanukan a kitchen harda najiya basu wanke ba , dawowa ɗaki sukayi suna shawarar inda zasu je yawo....!

*MOM ISLAM*

YARINYA MAI TAƁAR GAZAWhere stories live. Discover now