38 & 39

155 17 3
                                    

*YARINYA MAI TAƁARGAZA*



*Zainab Habib [Mom Islam]*

*Wattpad @momislam2020*

*AREWA WRITER'S  ASSOCIATION*

*Page 38 _39*

Ɗakin malam ta nufa kasancewar mama ta shiga ɗaki raba abinci ta nufi gurin ajiyarsa , cikin sa' a ta hango algara rar da yake naɗe kuɗi , ɗaukowa tayi taga kuɗi da yawa ita kanta sai da ta tsorata da ganin wanan kuɗi , mama.... Aisha ta ƙwala kira , na am mama tace "tana daga ɗaki ta fito da sauri , kina inane Aisha ? mama ta tambayeta , gani a ɗakin malam zaro ido mama tayi tare da ɗora hanunta a baki tana salati ta nufi ɗakin malam hango kuɗi a gaban Aisha tana ta taraww yasa mama kiɗima tace " a ina kikaga wanan uban kuɗin Aisha ? a gurin ajiyar malam Aisha taba mama amsa , maza ki mayar dashi mama tace " idanunta na shirin zubar da hawaye , ganin mam na shirin kuka yasa Aish share hawaye tace " mama wlh sai mun ɗibi kuɗinnan tunda bashida tausayi , mama tana mamakin magana irin ta Aisha intayi wata maganar kai kace babbar mata ce , nidai babu ruwna kitafi ki barni da masifar shi gara mu jira Allah ya bamu kowa yayi na gari dan kansa, mama ta juya tabar Aisha da tulin ƙuɗi a gabanta , ƙirga dubu biyar tayi tasa a hula ta tattara sauran tsabar sauri bata sani ba tabar dubu biyu a gurin ta mai da kuɗin ta fito , ganin mama bata gurin yasa ta ficewa da gudu ta nufi shago , malam dake zaune kan tabarma da carbi a hanunsa ya girgiza kai tare da cewa "yarinya sai kace aljana nidai banyi murna da dawowarki ba dan fitina zaki haddasa mana , kai tsaye shagon da ake siyarda kayan abinci ta nufa tace " a bata shinkafa mudu huɗu da kuma magi leda biyu da mangyɗa kwalba ɗaya da manja da wake mudu ɗaya , sai da taga kuɗin ya ƙare duka sanan ta haƙura ya zuba mata a bako daƙyar take tafiya tana jan kayan , ware ido malam yayi tare da ƙwala mata kira yace " meye a cikin wanan bakon kayan abinci Aisha ta faɗa tare da shigewa ciki , farinciki ne ya kama malam a fili yace " mun sami sabil kai masha Allah , tana shigo da kayan takai ƙarƙashin gado ta ɓoye , mama dake kallon ikon Allah tama kasa cewa komai sai da Aishan ta fito tace " badai kuɗinsa kika ɗauka kikayo siyayya ba na faɗa miki banason tashin hankali Aisha haka wancan lokacin yazo yana ta yimin masifa kidinga gudun magana , sai da mama ta gama faɗanta Aisha tace " dubu biyar na ɗauka wlh zaro ido mama tayi cikin fargabar abinda zai je ya zo tace " Aisha kice yau bazamuyi bacci ba a gidannan wato kin mance ko waye malam ko ? Aisha da ko a jikinta tunda ba tsoronsa take jiba tace " to ai mama iya kaci ya dokeni ke bazai iya dukanki ba , naji amma ai da wani faɗan gara duka ya kikeso inyi Aisha ? Aisha dai batace komai ba ta nufi inda mama ta ajiye mata abinci ta fara ci hankali kwance, tun daga zaure malam ke kwaɗa sallama mamaki ne ya kama mama dan taji muryar tasa kamar anyi masa bushara da aljannah ,wlkslm mama tace " tana jiran shigowarsa yau kuma hadaya muka samu ne naga Aisha da cefane fal jaka , murmishin yaƙe mama tayi tace " ban sani ba , nima kaji muna furci dan karma insa albarka to shikenan ina Aishar ,tasowa Aisha tayi daga inda take tace " malam gani , waye ya baki kayan da nagani a bako ?kuɗinka ne naɗiba dubu biyar Aisha ta faɗa babu alamar tsoro ,kutumar uba malam yace " ya faɗi ƙasa sumamme da gudu mama tayi randa ta ɗibo ruwa tana ta yayyafa masa amma shiru babu nunfashi salati ta shiga yi tana kuka tana cewa "malam ka tashi dan Allah haba malam , malam kam ko motsi bayayi dariya Aisha tasa tace " malam akwai son kuɗi kawai in ɗibo miki dubu biyu a ɗakinsa mu kaisa asibiti ,takaici ne ya kama mama gashi batada kuɗi sisi bata magani , kodai tabi shawarar Aisha ne wata zuciyar tace "ki barshi zai farka wata zuciyar tace " ki ɗauko kuɗin karfa a rasa rai , jeki ɗibo dubu biyu muga abinda Allah zaiyi tana shiga taci karo da ragowar kuɗin da ta bari kwasowa tayi tana cewa " mama ai har nabar wasu a ƙasa ma , mama bata tsaya kulata ba ta fita waje ta nemi temako aka ɗora malam wani ya hau bayansa mama ta tari mashin suka hau ita da Aisha suka nufi asibiti , da isarsu akace kuɗin kati ɗari biyar babu inda mama ta iya haka ta bada kuɗin suka kuma buƙatar dubu biyu , dubu ɗaya da ɗari biyar mama tace " za'a ciko ragowar , basu musa ba suka bashi gado tare da temakon gaggawa , tun 2:30pm suke abu ɗaya har 4:pm shiru sai can sukaji ya nunafasa yana surutai yana cewa " kuɗina kuka ɗiba yanzu kuɗina kuka ɗiba ? likitar da ta fahimceshi tace " wanan bawon Allah anyi masa sata ne ta tambayi mama , ko ɗaya mama tace " tare da miƙewa ta shige bayin ɗakin dage gefe , tana fitowa ta tada sallah tana idarwa tace wa Aisha tayi alwalah , bayan Aisha ta fito mama ta bata tabarma tayi sallah , suka zauna jiran tsammani, alurar bacci sukayi masa cikin lokaci kaɗan bacci mai nauyi yai gaba da shi , zuwa ƙarfe biyar ya farka alhmdulilh ya sami sauƙi aka rubuta musu sallama ,likitan yace " subar ɗari biyar ɗin , godiya mama tayi masa suka nufi bakin titi malam kam babu bakin magana jiki yayi laushi , suna isa gida akayi masa shinfiɗa a tsakar gida yai alwalah yai la'asar , ya koma ya zauna Aisha na fitowa ya tuno abinda ya faru , cikin faɗa yace " ki tattara kayanki ki koma wlh banison zamanki a gidannan zaki iya kasheni , inalilahi mama tace "wacce irin kalma ce haka malam gaskiya ka dena yo inba kasheni takeson yi ba ina ita ina kwasar min kuɗi , Aisha dake shirin zama tace " nifa kwana uku zanyi in tafi ɗazu ma da kuɗinka aka kaika asibiti , uwaki mama ta wurga mata daƙuwa , a zabure malam ya kalli Aisha yace " ba dan kin nuna ba ina aka san da kuɗin ? wlh inga kafin kibar gidannan sai nayi miki duka ,ya juya ga mama yace " kekuma waye yace " ki ƙara ɗaukar min kuɗi ? mama dake shirin tashi tace " ka samu nunfashin ka ya dai daita dole ka fara wata magana ta daban , nayi ɗin malam yace " cikin masifa , wucewa mama tayi ta barsu shida Aisha yana gallawa Aisha harara , malam na kawar da ido Aisha ta sa dariya jiyo sautin dariyar yayi yace "kinyiwa idi dan uwarki ƙanin mamanki mai huɗa , miƙewa Aisha tayi ta nufi waje tana dariya dan malam ma dariya yake bata musamman ma yau , Ummi ce ta ƙwalawa Aisha kira , na'am Aisha tace " ta fice da gudu , samun Ummi na yin alewar gyaɗa tayi da sauri Aisha ta ƙaraso tana cewa " zamu tafi da shi gidan yaya ne? eh Ummi tace " ai kuɗin da yaya ya bamu wanda kika miƙo min lokacin da zamu hau mashin shine nake yi mana wanan , lallai yau da masifa Aisha ta riƙe ƙugu , maman Ummi ce ta fito tana cewa " bazamu ga masifa ba insha Allah , meyasa zaki ɗaukar mata kuɗi ? maman Ummi ta tmbayeta, ita ma fa zata sha ko barta kawai mama , gwalo Aisha tayi mata tare da cewa " woooo ba yau zamu tafi ba ta fice ta dawo gidansu , lokacin malam ya lallaɓa zuwa masallaci , bayan sunyi sallah sai ga malam ya shigo tun daga zaure yake surfa masifa akan kayan da Aisha ta siyo mama dai na jinsa tayi burus tasan matayi yake nema , ƙarasowa yayi ya banƙaɗa labulen mama yace " ina kayan kuɗina ai sai a bani in gani tunda ta iya sata ta kawo  miki ke kuma ki karɓa , ni ƴata bata sata dan haka karka ƙara wanan furucin , ah lallai dole tayi abinda taga dama zaku fito da shi ne ko sai ranku ya ɓaci daga ke har Aishar.......!

*MOM ISLAM*

YARINYA MAI TAƁAR GAZAWhere stories live. Discover now