chapter 31 & 32

208 22 1
                                    

*YARINYA MAI TAƁARGAZA*



*Zainab Habib [Mom Islam]*

*Wattpad @momislam2020*

*AREWA WRITER'S  ASSOCIATION*

*31_32*

Ke dallah babu mai cin uban mu cewar Aisha cika kular tayi fam da abinci ta nufi ɗakin anty Fiddausi , anty Fiddausi na ganinta tace " kan uba wlh yau zakuci ƙaniyarku sabuwar kular tawa ? caɓ ana haka yaya Zakari ya shigo , ganin Ummi zaune a kichen ya leƙa kasancewar an kawo wutar nepa  me kikeyi anan cewar yaya Zkari  , cikin tsoro Ummi tace " yanzu muka gama abinci ina jiran Aisha ne , kamar ance leƙa kitchen yana leƙawa yaga ƙatuwar tukunyar da aka ɗora ga kitchen ɗin kamar anyi wasan ƙasa yayi biji biji, bai yi magana ba ya shige ɗakin anty Fiddausi , samu yayi tana yiwa Aisha faɗa , neman guri yayi ya zauna kana yace " ai ga aika aika can tashi kije ki gani maganin mai lalaci kenan , ƙin tashi tayi ta cigaba da cin indomie n ta Aisha na tsaye tana zaro ido , ɗaukar lemun tayi ta cika ƙaramin cup ta shanye takuma tsiyayo wani zata sha yaya Zakari yace " ina nawa karfa ki shanye , ga shinan anty Fiddausi ta miƙo masa jug ɗin , har Aisha zatayi magana ta fasa gudun kar ta jawa kanta duka , ficewa tayi tunda babu wanda ya kulata , kitchen ta koma ta sami Ummi ta cika roba da abinci tana ta kai loma tana shirin amai , wlh wanan abincin duk wanda ya cishi inhar cikin babu kyau to sai yayi gudawa , cewar Ummi , zuciya ce ta ɗebi Aisha tace " ai nagama yi miki komai tunda na dafa kikazo kina zagina , ta murguɗawa Ummi baki , miƙewa Ummi tayi tace " nidai na ƙoshi ga kwano ki zuba , wata uwar harara Aisha ta zabga mata tare da cewa " gobe zance yaya ya kaiki gidanku , har ƙasa Ummi ta sunkuya tana bawa Aisha haƙuri to na haƙura amma ki dubomin ƙai ƙayin nan ki ajiye mana shi a kusa , to Ummi tace " jiki na rawa a dole batason komawa gida ,
zuba abincin Aisha tayi tana masifa ita wlh bazata zama baiwarsu ba garama su nemi ƴar aiki.
9:pm Aisha da Ummi sunyi bacci tun takwas hira yaya Zakari suke shida anty Fiddausi da gudu anty Fiddausi ta miƙe tana cewa ka biyoni da ruwan ploshin me zakiyi , bata gama bashi amsa ba ta saki tusa mai wari , toshe hanci yaya Zakari yayi yana mata masifa , kasancewar toilet ɗin a kusa da ɗakinsu take yasa shi jin ƙarar kashin nata ji kake ɓirrrrrr cikin yaya Zakari ne ya murɗa shima ya fito da gudu yana salati , tunowa Fiddausi na bayi yasa shi cewa " wlh inhar baki fito ba inna shigo janyoki zanyi , ba shiri ta fito badan ta gama ba , yana shiga ya saki gudawa shima saki nasa ɓirrrr kafin ya nunfasa Fiddausi ta ƙwalara ƙara tare da cewa " kayimin rai ka ka fito dan girman Allah , yaya Zakari da ya keta wuli wuli da ido yace "ke kibari in gama bazan fito ba kema ai kin daɗe, kafin ta yi wani yunƙuri bata zata ba taji saukar abu kamar fitsari a jikinta , tana duba wa taga ashe gudawa ne , zaro ido tayi tana cewa " hankalinka ya kwanta nayi a wando inba so kake in mutu ba to ka fito kamar ka shiga ɗakin bacci , ko kulata bai yi ba shikam cikinsa ma murɗawa yake gakuma wani sabon kashin , yana gamawa ya kora kashin ya fito, a guje ta shige tana ihu kamar ba dare ba , ta ɗau mintuna kana ta tsarkake jikinta ta fito ta nemi kayan sawa , tana shiga bedroom ɗinta ta sami yaya Zakari yayi ruf da ciki yana zauke nunfashi , ƙara sowa tayi tama kasa zama tsaɓar zafin da ta keji tace " my Zak cikin dauriya yana nishi yaya Zakari yace " kirani da ZAKARI NA kawai yau ba love ka tashi ka ɗoramin koda wani abun ne insa a baki na wlh yunwa nakeji , tsaki yayi kana yace " ke gara ke ma yunwa kike ji nikuwa ɗuwawuna ya ɗaɗe ko juyowa banajin zan iya...!

Abban Islam babu lafiya shiyasa kuka jini shiru 😢👏.

*MOM ISLAM*

YARINYA MAI TAƁAR GAZAWhere stories live. Discover now