Babi na 2

380 14 0
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*NANA AMINATU*💧
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

*RUBUTAWA:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝🏼‍*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*P.W.A✍️*

*DAGA MARUBUCIYAR:*
_MEEMA FARUKH_
_MALAMA LADI_
_NAFEESAT_
_DOCTOR'S FAMILY_
_JARUMAI_
_LABARIN DEEBIZAH_
_ABUL KHAIRI_
_BRR. IBRAHIM KHALIL_
_RAUDHA._

*AND NOW:*

_NANA AMINATU._










*BABI NA___2*

Tun tafiyan Inna Habiba sai kuma ya zamana Inna Rakiya ta koma kan ɗiyar ta, duk wani tsana da take yiwa iyayen ta sun koma kanta, ta tsani ta buɗe ido taga baƙin fuskar AMINATU, shiyasa kullum ranan duniya sai ta zane mata jiki saboda tsaban tsana da tayi mata, da zaran Man Abba ya fice a gidan zata soma kirɓan ta tana saka ta aikin wahala, idan bata yi ba da bulalan ta na inji shi take zulala mata tayi ta jibgar ta kamar jaka, a lokacin Shekarun ta be fi bakwai ba amma babu azaban da ba ta sha wajen Inna Rakiya, gaba ɗaya jikin ta yayi shatin bulala

Da fari Yusuf ya so sanar wa Man Abba da ya fahimci azaban da AMINATU take sha, kasancewar sai ya tafi makaranta take jibgar ta, kuma tace mata, "idan ta sake ta faɗa musu sai ta yanka ta". To tsoron ne yasa bata taɓa sanar musu ba, sai da wani rana ya dawo makaranta ba'a biya mishi kuɗin school fees ba, ya zo ya cidda Inna Rakiya ta ɗaure mata ƙafafu da hannu tana ta jibgar ta, ita kuma ta haɗa majinu shaɓe-shaɓe a fuskar ta tana ta tsandara kuka babu halin sosa wa

Da gudu ya zo ya ƙwace ta shima yana kuka yana cewa, "Haba Inna me tayi miki zaki kama ta kiyi ta dukan ta kamar jaka haka?"

"Uban ka tayi min, ka bani ita ko in haɗa da kai inci uban ku tare wlh".

Still yana kuka yana ƙara ƙwaƙume AMINATUN a jikin sa yace, "wlh sai dai ki haɗa dani Inna bazan bayar da ita ba".

"Au haka kace dan uban ka?" Ai ko sai ta hau jibgar su tare

Suka maƙure waje ɗaya sai kuka suke yi, shi Yusuf ya dage yana ta kare AMINATU ana samun shi

Sai da tayi musu lilis tare kafin tace, "kuma wlh idan Abban ku yazo ka sanar mishi wlh tallahi sai na lahira ya fi ku jin dadi, ita wacce kake karewan zan ɗauke ta in saka ta a rijiya ta mutu kowa ya huta, daga ranan baza ka sake ganin ta ba bare ka kare ta".

Yusuf dai be ce komi ba sai shashsheƙan kuka yake yi yana sake ɓoye ta a jikin sa, tuni jikin AMINATUN yayi zafi rau saboda azaba

Ita kuma ta wuce ta bar su nan ta soma haɗa wuta don ɗaura girki, tana yi tana mitan, "dole ne ma ta koya mata girki tun yanzu, don bazai yiwu ace ita tana zaune ƙatuwa da ita ba tana mata girki, shegiya ƴar iska me baƙin fuska". Haka tayi ta sababi kamar bata san cewa AMINATUN yarinya ce ƙanƙanuwa ba.

Ƙarshe dai Yusuf shi ya ɗauke ta ya kai ta ɗaki saboda jin jikin ta yayi zafi, sai kyarma take yi, haka yana kuka ya fito da yaga Inna Rakiya ta shige ɗaki ya ɗibi ruwan ɗumi yaje dashi ya soma gasa mata jiki, ga shi jikin duk yayi shatan bulala da tsoho dana yanzu, har da ciwuka. Kuka sosai yake yi babu daman ya sanar wa Abban su tunda ba ya nan, kwanan sa biyu kenan da tafiyan sa Legos

NANA AMINATU 2022Donde viven las historias. Descúbrelo ahora