🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*NANA AMINATU*💧
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️*RUBUTAWA:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝🏼*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*DAGA MARUBUCIYAR:*
_MEEMA FARUKH_
_MALAMA LADI_
_NAFEESAT_
_DOCTOR'S FAMILY_
_JARUMAI_
_LABARIN DEEBIZAH_
_ABUL KHAIRI_
_BRR. IBRAHIM KHALIL_
_RAUDHA._*AND NOW:*
_NANA AMINATU._
*BABI NA___4*
Sai da Man Abba ya ja numfashi kafin yace, "Yusuf ba wai ina ƙin maganar ka bace, a'a sai dai don ka gane AMINATU ɗiya ce a wurin ɗan uwa na ɗaya tilo da ya rasu ya bar Ni, ita kaɗai nake gani na ji sanyi a raina, ina ganin ta tamkar ɗan uwa na Umaru ne, shiyasa bazan iya bari ta tafi nesa da mu ba, ko ba komi mu ne dolen ta, yanzu mahaifiyar ta tana can tana aure a Jigawa, bamu san wani rayuwa zata yi a can ba duk da kasancewar ta Uwa ce a wajen ta, amma shi mijin fa idan ba ya son zaman ta ai akwai cutuwa a wajen ta, nan kuwa ko Rakiya ta so ko ta ƙi nan ne dangin AMINATU, kuma bata da yanda zata yi da ita tunda tana da gado a cikin gidan, bata isa ta kore ta ba tunda gidan uban ta ne, na san wata rana komi zai wuce ai wuya ba ta kisa, da kanta Rakiya sai tayi dana-sanin muzguna mata a rayuwa, wata rana sai labari wlh. Ka kwantar da hankalin ka don Allah kaji?"
Shiru Yusuf yayi ba a son ransa ba da jin zancen Abban nasa
Dafa sa Man Abba yayi ya ce, "na san abinda kake tunani, haƙuri dai zaka yi Yusuf, komin daɗin daɗewa wata rana dama AMINATU zata tafi ta bar mu, dole zata yi aure ka ga kuwa babu ita babu musgunawar Rakiya".
"To amma Abba waye zai aure ta bayan har yanzu babu wanda ya taɓa zuwa wajen ta da sunan yana son ta? Ya ci ace AMINATU yanzu tayi aure tunda ta isa kuma ba karatu ne take yi ba, me zai saka Abba tayi ta zama tana shan wahalan Inna? Gwara ayi mata auren zai fi".
"To ban da abun ka Yusuf ai sai tana da masoyin, har yanzu babu wanda ya taɓa zuwa gida na da sunan neman AMINATU, yanda take ma ba na jin akwai wanda zai zo wajen ta, Rakiya ta hana ta ta gyara kanta bare har wani ya ji sha'awan zuwa wajen ta da sunan zai aure ta, kuma Ni bani da wanda zan ba shi ita har ya kula min da marainiyar Allah".
"Abba idan babu damuwa Ni na amince zan aure ta, zan auri AMINATU domin in fitar da ita ƙangin Inna, don Allah Abba kar kace a'a". Yusuf yayi maganar idanun sa dake cike da hawaye a kan mahaifin nasa
Sosai Man Abba ya nuna fara'an sa, da sauri ya ce, "da gaske kake yi ko wasa Yusuf?"
"Wlh Abba da gaske nake yi zan aure ta".
"Masha Allah Allah yayi maka albarka, Ubangiji ya saka maka da mafificin alkhairin sa, Yusuf bazan iya misalta maka farin cikin da nake ciki ba, insha Allahu baza ka taɓa taɓewa a rayuwa ba kai da zuriyar ka, Allah ya maka albarka Yusuf".
Yusuf cikin murmushi ya amsa mishi da, "Amin Amin Abba".
Sai gaba ɗayan su suka yi shiru na ɗan wani lokaci
Kafin Abba kuma yace, "Duk da haka ba na jin AMINATU ta tsallake bala'in Rakiya, kuma ba na tunanin ma zata yarda da wannan auren, amma ko ta ƙi ko ta so da yardan Allah sai an yi shi, sai dai matsalan muddin kuna gidan nan haka AMINATU zata ƙare a wahalan Rakiya, dole sai dai ku zauna a wani wajen Yusuf".

YOU ARE READING
NANA AMINATU 2022
FantasyMaganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a w...