Babi na 14

169 16 1
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
   *NANA AMINATU*💧
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

*RUBUTAWA:*
      _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝🏼‍*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

*DAGA MARUBUCIYAR:*
_MEEMA FARUKH_
_MALAMA LADI_
_NAFEESAT_
_DOCTOR'S FAMILY_
_JARUMAI_
_LABARIN DEEBIZAH_
_ABUL KHAIRI_
_BRR. IBRAHIM KHALIL_
_RAUDHA._

          *AND NOW:*

              _NANA AMINATU._

        *HADITH*
LADUBBAN SALLAMA
....... ﺃَﺑَﺎ ﻫُﺮَﻳْﺮَﺓَ ﻳَﻘُﻮﻝُ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ : )) ﻳُﺴَﻠِّﻢُ ﺍﻟﺮَّﺍﻛِﺐُ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻤَﺎﺷِﻲ ﻭَﺍﻟْﻤَﺎﺷِﻲ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻘَﺎﻋِﺪِ ﻭَﺍﻟْﻘَﻠِﻴﻞُ ﻋَﻠَﻰ ﺍﻟْﻜَﺜِﻴﺮِ )).
{ ﺭﻭﺍﻩ ﺑﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ }
....... Aba Huraira (R A) yana cewa: Manzon Allah ( S A W) yana cewa: " Wanda yake kan abin hawa yayi ma mai tafiya da kafa sallama, mai tafiya da kafa yayima Wanda yake zaune sallama, 'yan kadan suyi ma masu yawa sallama"
Allah ka bamu ikon kiyayewa.















*BABI NA___14*

               Kuka Inna Rakiya ta fashe da shi tana face majina da gefen zanin ta, cikin kukan take cewa, "yau Ni Rakiya naga abun da ya fi ƙarfi na, yau Ni Yusuf Ni kake faɗawa haka a kan wannan la'ananniyar ƴar taka? Har kake cewa zaka tafi ka bar min gidan? Kaicona Ni Rakiya! Allah wadaran naka ya lalace, amma wlh Habiba ta cuce Ni ta gama da Ni, yo me ake yi da irin su irin bala'i? Allah ya isa tsakani na da ke Habiba bazan taɓa yafe miki ba kin raba Ni da ɗana, kuma wlh idan ka bar gidan nan baza ka taɓa ganin daidai ba Yusuf, muddin ka kuskura ka bar gidan nan Allah ya isa ban yafe maka ba."

Yusuf wanda har ya gama tarkato kayan shi sai shima ya saka kuka saboda baƙin cikin da yake cin shi, yau ya gaji ya kai maƙura, kawai zama yayi a bakin ƙofan ya dinga rusa kuka tamkar wani ƙaramin Yaro

Su kansu sai da jikin su yayi sanyi saboda ganin yau Yusuf yana kuka duk a dalilin abun da Inna take mishi, yau ya kai maƙura

Inda NAANA da Salisu tuni sun nufi wajen sa suna kukan su ma. Basu taɓa ganin Mahaifin nasu a wannan halin ba sai yau

Shiyasa NAANA hankalin ta ya fi tashi matuƙa, hannu ta saka a jikin sa tana faɗin, "Baba don Allah ka dena kuka don Allah kaji, wlh zan bar gidan idan Inna ba ta son zama na amma don Allah ka dena kuka, zuciyata ba ta min daɗin ganin ka a haka, Baba don Allah kayi haƙuri." Kuka sosai take yi itama tana son rarrashin sa

Ɗago kai yayi yana kallon ta idanun sa jawur yace, "baza ki tafi ko ina ba Minal, muddin idan kin bar gidan nan sai dai mu tafi tare, ban san meyasa Inna ba ta ƙaunar ki ba? ke ƴata ce amma ba ta son ki, baki yi mata komi ba amma tunda aka kawo ki duniyar nan ta tsane ki, haka mahaifiyar ki ta mutu a cikin ƙunci da azaban mahaifiyata, baku yi mata komi ba kawai saboda ƙiyayya, to yanzu ke ɗin yarinyata ce wacce na haifa amma har yanzu ta kasa canza ƙiyayyar da take yiwa Mahaifiyar ki, ta maida shi a kanki, ya take so in Yi da rayuwata? na gaji na gaji! ina baƙin ciki da kasancewa ta a raye ina ganin abubuwan da Inna take miki, a kullum buri na in faranta mata amma ita kullum sai dai ta baƙanta min, ban san sanda Inna zata so ki ba a duniya, ban sani ba..." dole yayi shiru a lokacin sabida kukan da ya ci ƙarfin sa. Sai kuma ya tashi da sauri ya fice jin har an soma tayar da Sallan magriba

NANA AMINATU 2022Where stories live. Discover now