🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*NANA AMINATU*💧
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️*RUBUTAWA:*
_NAFISAT ISMA'IL LAWAL_*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝🏼*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*DAGA MARUBUCIYAR:*
_MEEMA FARUKH_
_MALAMA LADI_
_NAFEESAT_
_DOCTOR'S FAMILY_
_JARUMAI_
_LABARIN DEEBIZAH_
_ABUL KHAIRI_
_BRR. IBRAHIM KHALIL_
_RAUDHA._*AND NOW:*
_NANA AMINATU._
*TO FA... BABBAN MAGANA... NESA TA ZO KUSA KENAN....*
*Albishirin ku masoyana masoyan littattafai na.... Nesa ta zo kusa... Ƙasaitacce kuma fitaccen littafi na da ya fito muku a sabuwar shekara, salon na daban ne domin Ni kaina ban taɓa yin littafin da ya ɗaukar min hankali kamar wannan ba, iya basirata da ƙwarewata duk na bazar dashi a cikin wannan littafin. _ƊAN SANDA👮🏻_ kai daga jin sunan ma kun san akwai badaƙala a cikin sa, ƴar uwa ko ɗan uwa kar ka bari kar ki soma a baki labari ki nemi naki kawai ki ga cakwakiyar da ke ciki, ke da kanki zaki san tabbas littafin yayi, tabbas ya ci kuɗin sa domin sai Abu me kyau ake iya cire kuɗi a siya... A kan farashi me sauƙi ɗari biyun ki zai biya miki buƙata domin samun farin ciki a zukata... Tirƙashi _ƊAN SANDA_ labarin wani murɗaɗɗen saurayi ne da ke cike da burin ɗaukar fansa, ya hana kansa sukuni sai ya zaƙulo waɗanda suka kashe mishi Mahaifi, inda kuma gefe ɗaya yana tare da maƙiyan sa ba tare da ya sani ba, Matarsa ita ce ke da burin ganin bayansa, itama zuciyarta cike take da burin ɗaukar fansa, ta sha alwashi sai ta ga bayansa zata haƙura, dalilin da yasa ta shiga aikin ƴan Sanda kenan... Shin mene ne yayi mata da zafi haka?... Tirƙashi ƙa-ƙa ƙa-ƙa ƙa-ƙa muje zuwa FAN'S kar ku soma a baku labari ku nemi naku.. littafin zai zo a watan Mayu a kan farashi me sauƙi 200 kacal. 👌 Domin ƙarin bayani ku tuntuɓi wannan Numban only WhatsApp 07065334256 ko kuma 08146470539. sai na ji ku.*
*BABI NA___52*
Duk kukan da NAANA take yi daga Falo; amma Aneesa bata ji ta ba, tunda ta shiga cikin ɗakinta t.v ta kunna ta gyara zamanta a kan sofa ta hau yi tana faman yatsina fuska, bata sake tunanin wata NAANA ba har zuwa can almost 30minutes wanda alamu yasa ta ji kamar ana buɗe Gate, hakan yasa ta tashi ta leƙa ta window, ilai kuwa Sooraj ne ya dawo gidan. Sakin labulen tayi ta juya cikin bedroom ɗinta, ta sake gyara fuskarta tare da shafa turare sannan ta fito tana ɗan sauya takun tafiya, amma koda ta buɗe ƙofan a nan ta ganshi durƙushe a ƙasa cikin tsananin tashin hankali yana jijjiga NAANA da ba ta numfashi ko kaɗan, ga jini da ya gama wanke wajen gaba ɗaya har bushewa ya soma yi. Ita kanta ta tsorata da ganin jinin kamar an yanka dabba tsaban yawan shi, shiyasa ta daskare a wajen ko motsin kirki ta gaza, tana ganin sanda ya ɗauke ta ya fita da sauri amma ta gaza bin bayan shi, jikinta yayi sanyi duk da ba wai tausayi ta bata ba. Ta jima a wurin ma bata iya motsawa ba, daga ƙarshe sai ta shige ɗakin ta ba tare da tayi tunanin gyara wajen ba.
Shi kuma Sooraj kai tsaye asibitin da take aiki ya wuce da ita, tunda can ya fi kusa da su, gani yake yi tamkar ya rasa ta shiyasa gaba ɗaya ya gama fita a hayyacin sa, ko tsayuwa ƙafafun sa ba sa yi sabida tsaban ruɗewa, jikin sa sai rawa yake yi ya rasa me zai yi ya samu sukuni, tunda ya kai ta ya haɗa kai da bango yayi shiru ko numfashi me ƙarfi ya gaza yi; saboda gani yake yi tamkar idan ya shaƙi iska me ƙarfi za'a iya ce mishi NAANA ta mutu, to; bare kuma yayi ƙwaƙƙwaran motsi. Sun ɗauki tsawon lokaci da shiga da ita but ya kasa sanar da kowa a gida, yanda yake jin tashin hankali bazai iya sanar da mahaifin ta ba har sai ya ga halin da take ciki

YOU ARE READING
NANA AMINATU 2022
FantasyMaganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a w...