Babi na 55

181 12 7
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
     *NANA AMINATU*💧
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

*RUBUTAWA:*
      _NAFISAT ISMA'IL LAWAL_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝🏼‍*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

*DAGA MARUBUCIYAR:*
_MEEMA FARUKH_
_MALAMA LADI_
_NAFEESAT_
_DOCTOR'S FAMILY_
_JARUMAI_
_LABARIN DEEBIZAH_
_ABUL KHAIRI_
_BRR. IBRAHIM KHALIL_
_RAUDHA._

          *AND NOW:*

                  _NANA AMINATU._
















*BABI NA___55*

              Kamar yanda aka tsayar da ranan Litinin wanda za'a yiwa Inna Rakiya aiki, hakan ne ta kasance, an yanke mata ƙafa ɗaya yanzu sai jinya da take yi. Tana samun kulawa dai-dai gwargwado kuma yanzu jikin da sauƙi tunda har tana iya gane mutane sosai, zafin ciwon ya tsaƙaita mata

Tunda ta soma dawowa hayyacin ta take tambayar Baba, "Wai Ina Mijin Maama ta sa musu albarka? Har yanzu bata gansu ba?"

Shi ne ya sanar mata, "ai ba shine ya biya kuɗin ba, mijin NAANA shi yayi mata komai, ba don shi ba da tuni tana gida a mawuyacin hali domin shi kanshi be san inda zai samu maƙudan ƙuɗin nan ba."

Tunda ta ji hakan kuma sai bata ƙara yin magana ba. Daga baya ne kuma take tambayar, "Laure ta ƙi zuwa ta gaishe ta."

Bai sanar da ita abun da ke tsakanin su ba, don ya san halinta a kan Laure ƙila tace ya dawo da ita, shi kuma wlh bazai dawo da ita ba, auren su ya gama ƙarewa. Canza zancen ma yayi bai bari ta ci gaba da maganar ba

Kasancewar jikin Maama yayi tsanani domin ciwo ne sosai ya rufe ta, shiyasa Baba ya hana ta fita, tunda Inna ta soma samun sauƙi bata ƙara zuwa asibitin ba, magani kawai yake siyo mata tana sha idan tace mishi, "ga ciwon da take yi." Nan kuwa ita kaɗai ta san abun da ke damun ta, halin da take ciki ba ya misaltuwa kuma ta kasa sanar da kowa, kullum kuka take yi ta rasa yanda zata yi, ga shi tana tsananin jin tsoron Baban ta yanzu bare ta fita ta je ƙauyen Umman su ta faɗa mata halin da take ciki. Still har yanzu ruwan da ke fita a ƙasanta yana nan yana fita, yanzu kuwa har ya canza ƙarnin da yake yi sai wari da ke fita, ba dama ta zauna sai ta jiƙa wajen, shiyasa take saka tsumma tayi nafkin, bata tashi shiga tashin hankali ba sai ranan da ta shiga bayi tana yin kashi taga yana fitowa da tsutsotsi ƙanana-ƙanana, kuka ta dinga zabgawa ta rasa inda zata sanya kanta, nan fa jikinta ya sake rikicewa ta shige ɗaki tana ta kuka

A haka Salisu ya shigo gidan ya tarar da ita, ga Hanifah kwance a gefen ta itama tana nata kukan, ɗaki ya gume da wari. Shi ne ya kira Baba a waya ya sanar dashi abun da ke faruwa

To dalilin da yasa Baba ya dawo kenan saboda jin Salisun na kuka, domin ba kaɗan ba Maama ta ba shi tsoro da tausayi a halin da ya ganta, gaba ɗaya ta gama fita hayyacinta. Haka Baba ya zo ya tarar da ita shima, hankalin sa ya tashi gaskiya shiyasa yace, "Salisu ya je ya samo musu keke napep su wuce asibiti."

Babu jimawa ya dawo. Sai da taimakon su sannan suka shigar da Maama napep ɗin sannan suka wuce asibiti, aka bar Salisu da tsaron Hanifah a gida.





                 ******

             Bayan likitoci sun amshe ta aka soma bata taimakon gaggawa

NANA AMINATU 2022Where stories live. Discover now