page 38

319 22 0
                                    

L A L A T A [38]

Writing By: _SADNAF_

Copy ALBISHIR NOVELS
Whatsapp number 08163840712


              Ciki takoma tanufi dakinta ta kwantar, tana tunanin maganar da el Bahrain yamata,hawaye masu zafi ne suka zubo mata wani irin nadama  yakuma rufeta,allahuma inaka afuwun tuhibul afuwa fa afu anna,Allah Ka yafemin nayi kuskure,tace tana fashewa da kuka,tana Daga kwnce tana ta istigifari har sai data tafara jiyo kiraye kirayen sallah ta mike dan tayi alwala tayi sallah


Yusrah kua  tun lokacin data gama waya da tasleem, take ta zuba tsaki,dan gani take yana nan raina mata hankali tasleem zatayi,ganin ankusa minti talatin bai kira ba yasa ta dauki wayarta Takara kiran el Bahrain, jin wayar sa akashe ne yasa ta wurgar da waya,wani irin takaici da kishi suke rufeta,  hawaye suka zubo mata,dan gani  take el Bahrain baya Santa da yana Santa ba abinda zai hana yakirata dan da tasleem Ce bazai taba mata haka,hawaye masu zafi ne suka kara zubo mata,zuciyarta namata zafi,mikewa tayi ta dauro alwala tazo tafara nafilfili dan tasamu saukin abinda takeji azuciyarta,adduoi tayi Sosai  ta roki Allah dayasa Santa azuciyar el Bahrain,yakuma rage mata kishin dake damunta, sai wajen karfe biyu da rabi taje ta kwantar,washegari tana idar da sallahr asuba takara gwada wayar el Bahrain taji still akashe,ajiye wayar tayi tabuga uban tagumi kamar wacce akayiwa rasuwa,tana tunanin watakila ma baiyi sallar asuba ba,hajia Ummi Ce tashigo dakin da sallama,Yusrah ta amsa tana gaisheta,amsawa tayi ta ajiye kofin hanunta,yau Amarya kike fa naga kin buga tagumi,murmushi tayi tana murza zoben hanunta,ga wani tsumi nan ki shanye,ki shiga wanka kifito indauko miki waccan kayan ingaya miki yanda zakiyi amfani dasu,dan hajiya luba takirani tace karfe takwas zata zo ta dauke ki,shanye tsumin tayi ta mika mata kofin,hajiya Ummi ta mike tayi waje, wanka tashiga tafito ta mayar da kayan jikinta,tana zama hajiya ummi Takara shigowa da wata yarta abiye da ita,ta rike faranti,ajiye ledan viva bag din tayi, yarta kuma ta ajiye farantin hanunta tajuya ta tafi,yauwa gashi ki karya,inyi miki bayani yanda zakiyi amfani da kayan nan,bude flasks din tayi tadauki fork tafara cin indomien hajiya ummi taringa fito dakayan tana  mata bayani,akarshe kuma tayi mata nasiha akan zaman aure ta tashi ta fita,karfe takwas dai dai aunty luba tayi parking akofr gidan tafito ta shiga cikin gidan,apalo ta Tarar da hajiya Ummi nakaryawa,gaisawa sukayi,hajiya Ummi takira Yusrah,suka fito atare,masha Allah kanwartawa tayi min kyau aunty luba tace tana kallon Yusrah,zubewa tayi akasa ta gaisheta,ta amsa da murmushi afuskarta,hajiya Ummi kin gyara Yusrah gaskia kinga yanda fatarta ke sheki,ai yau Amarya take,dariya hajiya Ummi tayi tace nidin ta wasa Ce,ai indai da kudi zan maka gyara,to mu bari mutafi dan mijinta nasan anjima zai zo daukarta to hajiya luba sai yaushe,aa ai zamuyi waya dafatan kin hada mata abubuwa, sosai ma duk namasu bayanin yanda zatayi amfani dashi,to shikenan mungode sai munyi magana,suka yo waje hjiya Ummi tarakasu,tun acikin Mota Anty luba tafara tambayar Yusrah el Bahrain yakirata,tayi mata karya da yakira ta,shawarwari tayi ta bata nayanda zata zama mowa agurin el Bahrain har suka isa gida,sawa tayi Yusrah takara wanka tayi kwalliya kafin el Bahrain yakaraso,kwalliya tayi da wani Jan less mai manya Mayan flowers din baki takashe dauri tafito tazauna afalo su hajiya sukayi ta tsokanarta da yau el Bahrain bazai ganeta ba,ganin har karfe goma sha daya bai zo ba yasa Anty luba tafara masifa tana cewa yana can wajen tasleem yamanta da Yusrah in banda rashin adalci mai yahana yazo yadauki Yusrah tundazu yau dai Sunday ballantana yace sai dayaje office sanan yazo daukarta,daukar wayarta tayi takira layin el Bahrain taji akashe,tayi tsaki tacigaba da mita, sai da hajiya ta mata magana tayi shiru,Yusrah kua sunkuyar dakanta tayi dan bataso suga hawayen  dakake kokarin zubo mata.

El Bahrain kua sai dyayi sallahr azahar yakarasa gidansu direct palonsu ya nufa yayi sallama,hajiya ta amsa,Aunty luba kuma sai girgiza kafa take tana harare harare,sai yanzu Ka ga daman zua daukan Yusrah,haba Lubabatu kya Bari mugaisa tukuna Kafin kifara jera masa tambayoyi,ran el bahrain kua bakaramin baci yyi,daurewa yayi ya durkusa ya gaishesu,hajiya ta amsa,babana sai yanzu,ee wlh hajiya ban tashi ba sai sha daya,shiyasa kinji ko hajiya sai sha daya ya tashi yana can wajen tasleem ya manta dawata Yusrah,gaskia hajiya kiyi mishi fada yaringa adalci atsakaninsu,kashe wayarsa ma yayi dan kar akirashi,tashi ki shiga ciki zan mishi fadan,mikewa tayi tayi hanyar dakin,hajiya ta dawo da kallonta kan el Bahrain nasiha tayi mishi sosai tace yarike Yusrah da amana dan marainiyace,yace insha allahu tashi tayi ta nufi daki dan takira yusrah tzo su tafi,zua tayi ta tarar da aunty luba,tana ta bata shawarwari,tace ta fito su tafi,ta Mike, Aunty luba ta kwasar mata kayan sukayo waje,har wajen dyayi parking aunty luba ta rakata, sai da suka ja motar suka tafi ta koma ciki,el Bahrain kua tunda tahau motar bai kalli inda take ba dan wani irin tafasa Zuciyarsa keyi, Yusrah jitayi gabdaya jikinta yayi sanyi data ga yanda ya daura fuska,daurewa tayi tace yaya ina wuni,juyowa yayi ya watsa mata wani mugun kallo dayasa hantar cikinta kadawa.

                Juyawa yayi ya cigaba da tukinsa har suka karasa gida yana zuba tsaki,Yusrah kua hawye ne ke Neman zubo mata dan batasan mai tayiwa el Bahrain,horn yayi mai gadi,ya bude mishi gate yashigar da motarsa ya fito Daga motar yayi bangaren Yusrah,bude motar tayi itama ta fito ta share hawayenta tayi wajen tasleem,tasleem da tunda ta idar da sallah,ta shiga kitchen ta Dora musu launch, bayan tagama tafito tayi wanka,tasa cassette din bikinsu tana kallo,jin kara bude gate ne yasa ta mike taje ta leka ta window, taga el Bahrain ne ya dawo,ganin yafito Daga motar ransa abace,ne yasa takoma tazauna tana tunanin mai ya batawa el Bahrain rai,shigowar Yusrah da sallama ne yasa ta saki murmushi,Aunty Yusrah kindawo,itama kirkirar murmushi tayi tace,ee nadawo Aunty, sannu dazua,yauwa Aunty,yasu hajiya suna nan kalau sunce agisheki,ina amsawa,dama zua nayi ince miki mun dawo,to Yusrah sanunku da zua,ga abinci nan nayi mana ki tafar muku dashi,kai Aunty sannu dakokari,to kizo muje muci abincin duk da bawani yunwa nakeji ba,ee kije ganinan zua, daukar farantin tayi,tayi waje,tasleem tabita da kallo irin wanan kyau haka sai kace Amarya tasleem tace aranta,Yusrah na ajiye farantin abincin dakinta takoma ta canza kayan jikinta zua kana nan kaya,tafito ta zauna apalo tana tunanin mai tayiwa el Bahrain yakejin haushinta,dan a Iya saninta babu abinda tayi mishi hasali shi yamata laifi,tasleem Ce ta shigo da sallama ta amsa da murmushi, zama tayi akasan carpet din,ta dago ta kalli Yusrah, ina  nocsol md din,tab sabon salo wani sabon suna yaya yasamu kenan tace aranta,yana dakinsa bari nakirashi,ta mike tayi hanyar dakin shi gabanta nafaduwa,tura kofar tayi hade da sallama,yana zaune akan gado sai girgiza kafa yake, amsa sallamar yayi batare da ya kalleta ba,sunkuyar dakanta tayi tace yaya kazo muci abinci,ke zo nan,dagowa tayi tana kallonshi,badake nake bane kika tsaya kina kallona,kusa da gadon taje ta tsuguna kirjinta na bugun uku uku,Yusrah mai yasa kika rainani ne,dan kinga ina wasa dake ko,dagowa tayi idanta cike da hawaye tace yaya mai nayi,Yusrah harni zance miki ban yarda ki kwana, kisa Aunty luba takirani tace min kwana zakiyi,yaya wlh bance mata zan kwana ba,ita tace na kwana,Anty luba keda iko dake ko ni, umarninta zaki bi ko nawa, Yusrah kinga bansan munafirci arayuwata,dan da baki cewa Anty luba zaki kwana ba babu yanda zata kirani, tace min zaki kwana banasan kana kanan maganganu,mai kikace mata nayi miki da hartake cewa inringa adalci atsakaninku,yaya wlh, dakata nagama magana,Yusrah Allah yasan Ina Iya kokarina dan naga nayi adalci atsakaninku,dan kinje kin gaya wa aunty luba bana adalci atsakaninku keda Allah, kuma wanan hanyar dakika daukarwa kanki na munafirci ba hanya kika dauka mai kyau ba,sanan Daga yau karki kara yarda ki bijirewa umarni na in bahaka ba wlh sai anji kanmu dake, kinji nagaya miki,tunda yafara magana take kuka,kitashi mutafi inkin ga dama ki share hawayenki in baki ga dama ba kicigaba da kukan abokiyar zamanki tagane halin dakike ciki, goge hawyenta tayi da sauri Dan ta tuna maganar aunty luba,bandaki tashiga ta wanko fuskarta,tadawo tasameshi atsaye,ya rike hanunta sukayi waje, tasleem kua ganin yanda suka Dade basu fito ba yasa ranta yadan sosu,dan aganinta wanan wulakanci ne,duk abinda zasuyi sa Bari insunci abincin tabar bangarensu sai suyi,amma dasu shanyata subarta azaune,ganin sun fito hanunsu arike dana juna ne yasa takau dakai, heartbeat so sorry mun barki kinata jiranmu,ina bandaki ne shine ta tsaya jirana,murmushi tayi tace bakomai, Yusrah zuba musu abincin tayi suka fara ci,Yusrah sai juya cokali take takasa cin abincin, dan wani kullutu ne ya tsaya mata awuya,duk abinda takeyi el Bahrain na kallonta,ahaka suka kammala cin abincin,tasleem tayi bangarenta Yusrah takwashe kwanukan takai kitchen,tawuce  dakinta,el Bahrain kua bangaren tasleem yayi,yaje yasmeta tana yanke farcen kafarta,heartbeat yamukayi dake dazu,dagowa tayi tace yamukayi na manta wlh tunamin, bakince zaki zo kitayamu hira ba,ee hakane mantawa nayi wlh bari nagama yankan farcen ganinan zua,to muna jiranki yajuya yatafi,kicibis sukayi da Yusrah tadauko Leda Daga cikin motar sa,kau dkansa yayi yashige,tabi bayansa,hanyar dakinta tayi,yakira sunanta,ta tsaya, mai wanan aleda? kayana ne tace cikin rawar murya, kau dakansa yayi yacigaba da kallo,dan yadauka wani kyautar tasamo dan ya musu warning akan duk wacce akayiwa abun alheri taringa sanwa Yar uwarta hakan ne zai kara shakuwa atsakaninsu dan bayasan rowa, Yusrah kua tana shiga dakinta ta dafe kirji tana godewa  Allah da asirinta bai tonu ba. Ajiye ledar tayi adrawern mudubinta.

LALATADove le storie prendono vita. Scoprilo ora