L A L A T A [42]
Writing By: _SADNAF_
Copy ALBISHIR NOVELS
Whatsapp number 08163840712El Bahrain kua bangaren tasleem sukayi ya watsar da ita akasan carpet, yaringa kallonta da rinanun idansa dasuka ja kamar gauta,wani irin bakin ciki da kishi suna ratsa shi,takawa yayi yaje gabanta,ya ruko kafadarta,tasleem uban me kikajeyi awaje mai yahadaki da izzadeen dahar zai rungume miki kafa yace atsawace yana girgizata, su su su Fateema naje rakawa tace cikin muryar kuka,da iznin wa kika fita,tasleem ina miki kallon mai hankali nadauka ko waje nace kifita ke kadai bazaki fita ba dan kinsan gidan izzadeen yana kusa damu,shine kika fita purposely bada iznina ba har izzadeen ya Iya taba miki jiki baki dauki dutse kin fasa masa kai ba,kokarin magana take yace shhhh tasleem kinsan ya nake ji azuciyata kua,izzadeen yatabamin jikin danake mugun so fiye da komai kika tsaya kina kallonsa tasleem, mai yasa zaki min haka yace yana girgiza ta cikin tashin hankali,dan Allah kayi hakuri nayi kuskure ban taba tunanin zanganshi ba wlh da ban fita ba,tazame ta durkusa dan Allah Ka yafemin,shigowar Yusrah da sallama ne yasa suka juya suna kallonta,takaraso gurin el Bahrain ta ruko hanunsa taja shi suka fita waje,tasleem ta kwantar akasa taringa birgima tana kuka,yusrah kua dakinsa na bangarenta takaishi ta zaunar dashi akan gado ta durkusa agabansa ta dafa gwiwarsa,tace yaya dan Allah dan annabi kayi hakuri Allah ya huci zuciyarka,bansan mai yafaru ba amma nasan koma mnene bakaramin Abu bane,dan Allah kayi hakuri idan ma aunty tasleem Ce ta bata maka rai nima na ari bakinta nabaka hakuri dan nasan bazatayi abunda zata bata maka rai dagangan ba sai dai in kuskure aka samu,girgiza kafa el Bahrain keyi kawai yana hango yanda izzadeen yarike kafafuwan tasleem zuciyarsa wani bakin ciki ne yakara rufeshi zuciyarsa na masa zafi,mikewa yyi yakara yin bangaren tasleem kai abu kamar wasa fa yazama gaske, dan el Bahrain daya koma sama kuma damko tasleem yayi yana mata fada kamar zai daketa,abinka da Wanda yake da hakuri bai Iya zuciya ba ganin tana ta bashi hakuri,kamar kara zugashi take ne yasa ta fusge jikinta Daga rikon daya mata tayi waje dagudu tayi hanyar gidan izzadeen ,el Bahrain yabi bayanta shima da gudu,Yusrah da ganin yanda sukayi waje da gudun ne yasa itama tabi bayansu,tana gab da shiga gidan el Bahrain yakamota,ta fusge tafara magana cikin kuka,Ka kyalleni tunda bka yarda dani ba,inje insamu izzadeen ya kasheni tinda burinsa arayuwa ya gani abakin ciki,bansan mai yasa izzadeen yake min haka ba,kai danayi tunanin Ka yarda dani kafi kowa sanin halina kai ma gashi Ka murzawa idanka toka,izzadeen dake zaune akan kujerar Palo da kumburarriyar fuska suhaima na Dana mishi fuska da ruwan zafi,muryar tasleem dayake jiyowa ne yasa ya mike yayi hanyar waje,tasleem kua tana hangoshi tayi wajensa dasauri,el bahrain yasha gabanta, yajanyo hanunta yaringa jan hanunta sukayi waje Ka cikani inje ya kasheni ya huta tunda burinsa arayuwa yagani cikin bakin ciki,bai cikata ba har sai da suka koma bangarenta yasa ta adakinta ya kullo kofar,yayi waje, Yusrah data biyosu ta rabe ajikin kofa, tana ganin sun wuce takarasa gurin izzadeen dake tsaya da suhaima, tace wai mai ke faruwa ne izzadeen,mai yahdaka da Anty tasleem ko inda take bai kalla ba yawuce yakoma ciki, yusrah kua ganin haka ne yasa ta juya tare da cewa Allah yakyauta,kicibis sukayi da el Bahrain abakin kofa,ke kuma uban me kikeyi anan,jiki narawa tace bakomai tanufi cikin gidan,el Bahrain kuma yashiga ciki,direct Palon yashiga yaje ya Tarar da izzadeen daya dafe kansa da hannu biyu,izzadeen nazo namaka warning da Babbar murya kafita Daga harkar tasleem, idan bahaka ba wlh abinda zanyi maka nan gaba sai yafi Wanda namaka yanzu.
Kadai ji nagaya maka dan bantaba tunanin akuyancinka yakai duk da tasleem tana da aure karinga bibiyarta ba, izzadeen bakasan halina ba,wlh akan tasleem zan Iya kisan kai,enough kamal,enough of all this nonsense Izzadeen yace atsawace yana mikewa,look kamal let me tell you,dan kaga nama shiru bashi yake nunawa ina tsoronka ba,what's so special agurin tasleem dazan ringa bibiyarta,to bari kaji ingaya maka tasleem na Dade da sata akwandon shara tunda sai Dana gama abinda nakeso da ita na baka sauran,and tunda hankalinka baya jikinka idonka ya rufe akan tasleem wlh wlh wlh sai na kwace tasleem din Daga wajenka,sai narabaku,takarfi da yaji ko bajima ko ba Dade wlh,dan nasan tasleem dan batada option ne yasa ta aureka bawai dan tana sanka ba, in banda ma rashin hankali irin naka har kana da bakin zua kayi min magana akan tasleem,bayan kasan butulci kayimin da cin amana,Ka auri wacce nayi dating, kai wlh inka bani haushi ma har Yusrah sai na rabaku na auresu duka biyun inga ta tsiya dan baka san halina bane I can do anything to have what I want,tunda yafara. Magana el Bahrain yaji kamar kirjinsa ya fito dan bacin rai jin yace zai rabashi da tasleem ne yasa kirjinsa fara dukan uku uku,haka kace ko? ee haka nace,to Allah yabaka saa,ameen izzadeen yace yana jifanshi da mugun kallo da kumburarun idansa,OK we shall see el Bahrain yace tare da juyawa ya fita,izzadeen yayi tsaki yace dan iska kawai zaka san Ka tabani,suhaima da tunda suka fara musayar maganganu tasaki baki tana kallonsu har sai da el Bahrain yafita tadawo da kallonta kan izzadeen, tab izzadeen ashe kai bakaramin dan iska bane,yanzu matar abokinka kake nema,lailai Kai rikakke ne a yan iskan amma in bahaka ba inakai ina Neman matar aure, ni danasan abinda yafaru kenan wlh da mun barshi yamaka ido daya,muga ta inda zaka Iya kallon matar wani,izzadeen cire takalmin kafarsa yayi ya jefata dashi ta kauce,dan ubanki ba gwarani akanki ba matar wani na bi,ke da kika shigowa mutane gida da cikin shege ba fa Yar iska kawai,gaka babban,nufarta yayi aguje ta kwasa da gudu ta shige daki ta kulle,zakici ubanki xaki fito kisameni ya juya yayi hanyar dakinsa.

YOU ARE READING
LALATA
RomanceLabarin Tasleem data had'u da mayaudari har ya rabata da martabarta ta diya mace a karshe ya juya mata baya