PAGE__10

80 7 0
                                    

_Page 10_💎

*SAI DAKE!*🫀
_written by_
*BILLY S FARI💎*

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

Zaku iya samun Complete documents ɗin wuɗannan littafan nawa.

*FILHUB* N500
*WASU MAZAN* N300

_Sai kutura ta wannan account lambar, 0434776437| Gt bank Balkisu sani ƙaura, ko kuma katin waya da shedar biya ta wannan lambar 07040402435_.

_Domin samun wannan littafi Complete zaku iya zuwa wattpad sai ku danna wannan link https://www.wattpad.com/story/281979031?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=h1hTYUDmeeoMp11b3lTkCiCDDLppuAl%2B6kbyiK4cGXQ5e2Fg7YLuARy9Dcp%2BEVPxUXJImhmoAGRg72rOwrncWtECkGHwwVNmdJ%2BFopJSUVlXXQah7ciB4BN9KGwZqXho_
______________________________
Dole itama ta gyara kwanciyarta ta kwanta saboda ba tada wani zab'i daya wuce mata hakan, tasan gaskiya Abban Enaya ya fad'a mata don manyan mutanennan da suka saka siyasa agabansu ba wani mutunci ne dasu ba, yanzu ne zata saka kanta cikin lamarin da niyar taimakonsa sai reshe ya juye da mujiya, don haka sai ta kakkab'e komai aranta tare da yimasa addu'a akan ALLAH yayo masa mafita ita kuma Waheeda ALLAH ya saka mata ga duk wanda ya zalince ta, sauqinta ma ALLAH ya kareta da akayi gwaje gwajen da za'ayi alhamdulillah babu wata cuta data kamu da ita, haka tayita tunane tunane har bacci ya zo ya yi awon gaba da ita.

*** *** ***

Sosai Ra'ees ya samu bacci har wucewar bayan sallar la'asar sannan ya farka, lokacin Momy na nan falo zaune tare dashi bata jima da sallame sallah ba, ganin ya fara motsi da qafafuwansa yana qoqarin tashi ya sa tayi saurin tasowa had'e da taimaka masa ya zauna daidai yana dafe kansa gefen da gwaggo ta buga masa tab'arya saboda zugi da wajen keyi masa, hannu Momy ta d'aura awajen fuskarta d'auke da damuwa ta ce.

"Da zafi ko yaron Dady?"

'Dan murmushi ya yi cike da qarfin hali don ya kawar mata da damuwar daya gani kwance akan fuskarta had'e da cewa, "Ba sosai ba Momy, ina so naci abinci yunwa nake ji sosai" murmushin itama tayi cike da jin dad'in yanda ya amsa mata, koba komai ta tabbata ya samu sauqi tunda har ya nemi abinci, shafo kansa tayi izuwa kuncinsa tana fad'in.

"Sannu ko! ALLAH yabaka lafiya." Ya amsa da amin ita kuma ta miqe ta nufi inda telephone ɗin dake falon ta kira, wannan karon Easha ce ta d'aga, ta ce tafad'awa mama Kareem ta had'owa Ra'ees abinci ta karb'o ta kawo mata sannan ta katsiye kirin had'e da dawowa inda yake ta zuba masa idanuwa tana nazartarsa saboda dogon tunanin da taga ya fad'a.

"Ra'ees, Ra'ees.." ta kira sunansa har sau biyu bataga ya amsa ba, a na ukunne da zata kira tad'ora hannunta saman kafad'arsa had'e da cewa.

"Ra'ees lafiya kuwa? Tunanin me kakeyi haka?"

Shiru ya d'anyi kafin ya nisa tare da dafe kansa yana son bayyanawa mahaifiyar tasa sirrin zuciyarsa, saboda barin kashi ciki baya maganin yunwa, shi yanzu har ga ALLAH ba damuwarsa qazafi ko sharrin da akayi masa bane, damuwarsa kawai shine taya za'ayi yaga Waheedarsa har ya bayyana mata soyayyarsa? taya zata sauraresa har ta iya fuskantar cewa a halin yanzu sai da ita zai iya rayuwa?, taya zata karb'esa hannu biyu tare da gane cewa bashi ya aikata mata hakan ba?, Wud'annan abubuwan sune sukafi damunsa kuma suka tsaya masa arai.

"Ra'ees wai bada kai nake magana ba?" Momy ta sake fad'a tana kallonsa had'e da ɗaure fuska.

"Amm..kiyi haquri Momy, Babu abunda ke damuna yanzu sai tunaninta."

"Tunaninta? Ita wace?"

"Waheeda!" Yabata amsa ataqaice yana lumshe idanuwa,

Amsa sallamar da Easha keyi Momy tafarayi had'e da karb'ar tiren dake hannunta ta ajiye anan ƙasa gabansa sannan ta ɗago tana kallonsa, gaisuwa da ya jiki da Easha ke yimasa yake amsawa kafin ya maido hankalinsa ga Momy dake faɗin.

SAI DAKE.!Where stories live. Discover now