PAGE__67

112 5 0
                                    

💎 _page 67_💎

*SAI DAKE!*🫀
       _written by_
*BILLY S FARI💎*

© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

_follow me on my Wattpad @Billysfari9 https://www.wattpad.com/story/281979031?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=h1hTYUDmeeoMp11b3lTkCiCDDLppuAl%2B6kbyiK4cGXQ5e2Fg7YLuARy9Dcp%2BEVPxUXJImhmoAGRg72rOwrncWtECkGHwwVNmdJ%2BFopJSUVlXXQah7ciB4BN9KGwZqXho_
______________________________
_*JAMILA, SALIHA ALIYU, NAJIDA ALIYU, ASIYA ALIYU (UMMU SAUDA), XEEE, UMMU MUSHFIQ, MAMN HANIF, BABEEY, QAWATA😜(UMMU SAFWAN), UMMUL ADNAN, MMAN SSSS* Kai dama sauran wud'anda ban ambata ba dake group d'in SAI DAKE, Ina miqo gaisuwa tare da fatan alkhairi agareku, tabbas kud'in na dabanne awajena, kin nuna mani karamci da halacci wajen bibiyar wannan littafi duk da tafiyar hawainiyar da nakeyi batare da kun nuna qosawa ko gazawarku ba, wannan shi ake kira da girman mutuntaka, ina alfahari daku akoda yaushe kuma zanci gaba dayi har iya bugawar lumfashina naqarshe, ngd sosai ubangiji yayi maku sakayya da mafi qololuwar ni'imarsa wato aljannah fiddausi🤝 SON SO NAWAN NI KA'DAI💃💞😍_
    💎💎💎💎

Shire shire Momy keyi na musamman acan qauyen mahaifin Waheeda, don kusan kwana biyu kenan kullum sai taje domin gyara wajen da za'a gudanar da taron, azahiri taron taya Waheeda murnar cika shekaru ashirin ne Amma a bad'ini, tsuntsu biyu ne Momy ke son jifa da dutsi d'aya, Taya Waheeda murnar had'uwa da dangin mahaifinta da kuma nemawa 'ya'yanta biyu auren Waleeda da Waheeda, Wanda tuni suka gama tsarin ita da Dady cewa bazasu baro qauyen ba bayan angama shagalin bikin saida tabbacin aure ya shiga tsakanin Waheeda da Ra'ees, Musaddeq da kuma Waleeda, wannan yasa Dady gayyatar abokansa guda biyu da kuma uncle qanensa awajen taron don abun yaje yanda suka tsara,

Waheeda kam murna ba'a magana, kusan kullum cikin yiwa Momy zancen take wai bataga ana shire shire ba kuma gashi kwana d'aya ya rage, yauma kamar kullum, Momy na zaune tana waya da mai d'unkin da tabawa kayan da zaya d'unkama Waheeda dasu Enaya saiga Abbiey ya shigo da gudu Waheeda na biye dashi, da yake dama sun gama wayar saita jayeta ga kunnenta had'e da kallon Waheeda data ja burki a gefen madubi tayi tsaye ganin Abbiey ya b'uya abayan Momy,

"Yau kuma me qanen aunty Waheeda yayi mata naga ta biyoshi aguje" Momy ta tambaya tana qoqarin jawo hannun Abbiey daya b'uya a bayanta, sinne kai qasa Waheeda tayi had'e da aikamasa harara taqasan idanuwa yana dariya yace,

"Momy ALLAH Abbiey ya renani, wai ni yake cewa amaryar birthday" zaro idanuwa Momy tayi tana kallonsa had'e da cewa,

"Kai, waya fad'a maka haka?, Bazaka dena tsokanar auntynka ba ko?, Kasan halin Ra'ees kar da kuma jan kunnen da yayi maka, amma shine bazaka dena ba ko, ai shikenan bari ya dawo zan fad'a masa tunda bakaji, qyalesa dota, zansa yayanki yayi maganinsa"

Momy na rufe baki Ra'ees nayin knocking tare da turo qofara ya shigo bakinsa d'auke da sallama, wani irin tattausan murmushi ya saki ganin Waheeda had'e da gaida Momy lokaci d'aya kuma idanuwansa nakan Waheeda,

"Yaya Ra'ees sannu da dawowa, an wuni lafiya?" Tafad'a awayance tana miqawa Abbiey hannu daya gama tsorata ganin Ra'ees d'in don su gudu, d'auke idanuwansa yayi daga kallon da yakeyi mata zuwa inda yaga tana miqa hannu, ganin Abbiey yayi da gudu ya nufi wajenta tariqe hannunsa sukabar d'akin tana dariya, cikin d'aga murya momy tace,

"Ina kuma zakije dashi, dawo mana tunda baya jin magana yanzu ayi maganinsa" Momy taqare maganar itama tana dariyar yanda suka fice d'akin kamar walqiya,

"Hmmm yaran can basa jin magana Momy, ALLAH ke kike qyalesu suyita sawa mutane ciwon kai"

"Naji d'in, ai nakusa tattarasu gaba d'aya na miqa maka nahuta"

SAI DAKE.!Where stories live. Discover now