PAGE__42

113 5 0
                                    

💎 _page 42_💎

*SAI DAKE!*🫀
       _written by_
*BILLY S FARI💎*

© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

_Follow me on Wattpad @Billysfari9 https://www.wattpad.com/story/281979031?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=h1hTYUDmeeoMp11b3lTkCiCDDLppuAl%2B6kbyiK4cGXQ5e2Fg7YLuARy9Dcp%2BEVPxUXJImhmoAGRg72rOwrncWtECkGHwwVNmdJ%2BFopJSUVlXXQah7ciB4BN9KGwZqXho_

    💎💎💎💎

Wayar Easha ce tayi qara acikin aljihun jikkarta data dawo makaranta Waheeda tayi saurin zuge zip d'in aljihun had'e da ciro mata, daidai lokacin tagama cire rigarta ta uniform tana qoqarin d'aura towel ta kalli Waheeda had'e da cewa,

"Waye?"

Screen d'in wayar Waheeda takalla tare da kallonta sannan tace,

"Dr. Umar ne"

"Manta dashi don Allah" Easha tafad'a tare da zame wandon uniform d'in nata tanufi toilet, har ta aza qafarta bakin toilet d'in zata shiga wayar ta qara d'aukar qara lokacin Waheeda na qoqarin ajiyeta, wani irin tsaki Easha ta sake ja cikin b'acin rai had'e da cewa,

"Don ALLAH sisynah kashemun wayar nan gaba d'aya, ALLAH ina gab da had'a Dr. Nan da Yaya Musaddeq" taqare maganar cikin b'acin rai kamar zatayi kuka, dariya Waheeda ta tuntsire da ita kafin tace,

"Tab! Yau ina ganin inda ake hantarar masoyi harda sukai qararsa, to banda abunki aunty Easha ina laifin wanda yace yana sonka? Aidai ko yane yafi maqiyinka ko?"

"Mtsss..Waheeda bana so, miqon wayata nakashe kafin yasake kira tunda ke bazaki kashemun ba"

"ALLAH yabaki haquri bari nakashe, wlh ALLAH aunty Easha sai nabaki mamaki duk ranar da Yaya Safwan d'ina yadawo, shine mutum nafarko bayan iyayena, Gwaggnah, Enaya tah da kuma su aunty da bazani tab'a mantawa dashi arayuwa, ya soni tun bansan meye soyayya ba, ya laqanta mani kalmomin so abakina tun bana fahimtar me suke nufi saidai na ajiyesu a kwakwalwata da kuma zuciyata, amma kinsan me aunty Easha?, Wlh yanzune nake gane duk wani tasiri nasu da kuma ma'anarsu azuciyata, yanzu ne nake jin yanda ya yayi nasarar tusamun sonsa da qaunarsa cikin hikima, ada nayi tsammanin cewa shaquwace kawai tsakanina dashi, amma yanzu nafahimci sonsa nakeyi sosai, sonsa nakeyi fiye da tunanina, saidai kash hakan baida wani tasiri ko muhimmanci yanzu don bansan ina zan samosa ba, ina yaje, awane hali yake? duka ban sani ba, abu d'aya na sani, shine duk inda yake ina aransa kuma dani yake kwana dani yake tashi kamar dai yanda yake awajena, don haka kidena yiwa Dr nan walaqanci Aunty Easha, wlh ALLAH lokaci zaizo dake da kanki zaki so sanin halin da yake ciki, takowane irin hali yanzu ina so nasan ya yaya Safwan d'ina yake?, Ina so yasan wane irin matsayi nabashi yanzu azuciyata, amma bansan lokacin da hakan zai faru ba"

Baki sake Easha ke kallon Waheeda jin yanda take tsaro kalamai, har ga ALLAH da wanine ya fad'a mata tayi hakan bazata yarda ba duk da takanyi zancen Yaya Safwan d'in a lokuta barkatai amma tazata shirmene da kuma qurciya, don ba Waheeda ba ko ita bazatace tasamu dama ko fuskar fara soyayya ba balle ita, Sam Yaya Musaddeq baya barinsu shiyasa ma takeyiwa Dr.umar haka saboda yace ba'a had'a taura biyu a baki, soyayya da kuma karatu, shiyasa ta zab'i karatun ta ajiye soyayyar har saita kammala karatunta kamar yanda yace kuma su Momy da Dady sun goya masa baya akan hakan, to ya akayi Waheeda tasan so har yayi qarfi azuciyarta haka,

Kamar Waheeda tasan abunda take tunani tayi dariya had'e da cewa,

"Bafa abun mamaki bane aunty Easha, koda nazo gidan nan anriga da andasa mani soyayya a zuciyata, da ita narayu kuma na tabbata da ita zan mutu indai ta Yaya Safwan d'ina ce"

SAI DAKE.!Where stories live. Discover now