💎 _page 62_💎
*SAI DAKE!*🫀
_written by_
*BILLY S FARI💎*© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
_follow me on my Wattpad @Billysfari9 https://www.wattpad.com/story/281979031?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=h1hTYUDmeeoMp11b3lTkCiCDDLppuAl%2B6kbyiK4cGXQ5e2Fg7YLuARy9Dcp%2BEVPxUXJImhmoAGRg72rOwrncWtECkGHwwVNmdJ%2BFopJSUVlXXQah7ciB4BN9KGwZqXho_
💎💎💎💎
Yauma kamar kullum, kwance yake a rigingine saman makeken gadonsa ya qurawa pop d'in saman d'akin nasa adamuwa, azahiri zakace shi yake kallo, amma a bad'ini tunani yakeyi, da gudu Abbiey ya turo qofar d'akin nasa tare da hayewa saman jikinsa yana fad'in,
"Yaya Ra'ees wai kazo inji Dady kayi baqi" ganin bai tanka saba yasa Abbiey sauka daga saman ruwan cikinsa daya haye ya koma gefe yana kallonsa had'e da kiran sunansa, zaro idanuwa yayi ganin hawaye na zararowa ta gefen idanuwansa had'e da zurawa da gudu yayi wajen Momy dake kitchen tana had'owa Dady drinks da ruwa dake can guiding zaune tare da baqin dake son ganin Ra'ees, Waheeda kuma na zaune nan falo tana yanke akaifa, yanda ya shigo da gudu yana kiran sunan Momy yasata fitowa daga kitchen hankali tashe, "Kai Abbiey, lpy kuwa?" ta tambayesa had'e da riqo hannuwansa,
"Momy Yaya Ra'ees ne"
"When, meya sami Ra'ees d'in?"
"Momy ya mutu baya motsi kuka yake" wani irin d'ago kai Waheeda tayi cike da razana har rezar dake hannunta tana yanke farcenta na qafa ta yanketa,
"Washh.." tafad'a da qarfi had'e dayin 'yar qara tana riqe yatsan da jini ya soma zuba sosai, amma duk da haka bai hanata kallon Abbiey tace,
"Abbiey qarya bakyau fa!, meye ya sami Yaya Ra'ees ne halan?"
"Wlh aunty Waheeda kuka yakeyi, Kuma ina yimasa magana yaqi amsa min"
Tasowa yayi tana d'ingishi da qafar ta nufo wajen da take tsaye, don tuni ita Momy tabar wajen tunda ta riga da tasan kwanan zancen, labarin gizo baya wuce qoqo,
Mangaro kan Abbiey Waheeda tayi had'e da cewa,
"Kadena wannan fatar wa yayanmu, shikenan don kaga hawaye a fuskarsa yaqi yimaka magana sai kace ya mutu? Very fair yeyee boy"
Daidai lokacin Momy ta fito d'auke da qaton try data had'o drink's da ruwan aciki, da sauri Waheeda na d'ingishi da qafa ta miqa hannu zata karb'a tana fad'in,
"Kawo na kaimasu Momy" kamar ance Momy ta dubi qafarta ganin d'ingishin da tayi taga yatsanta na jini,
"Subhanallahi dota, meya sameki haka?" Tafad'a tare da ajiye trayn agefe tana kallonta, Aryana ta qwallawa kira tare da riqo hannun Waheedar ta zaunar akan kujera,
"Aryana d'auki abun nan ki kaiwa dadynku yana gueding shida baqi" tafad'a tare da wucewa d'aki ta d'auko first aid, spirit tafara cirowa ta zuba mata a qafar ta saki wata irin qarar da tasa Ra'ees dawowa daga tunaninsa da gudu yayo falon na Momy, wani burki yaja abakin qofar falon tare da qarasowa wajen ya durqusa kamar yanda Momy tayi tana sake saka mata cincinbale da kad'a awajen, fuskarsa kamar zaiyi kuka ya kalli momy had'e da cewa,
"Momy meya sameta ne" tare da maida kallonsa ga Waheeda da har 'yar qwalla tayi saboda zafin sifirit,
"Yaya Ra'ees wai don nace kamutu ne shine tana yankan farce taji tsoro ta yanka qafarta.." kafin ya rufe baki ta d'auki throw filon dake kan kujera ta jefesa dashi tana maka masa harara, "Kai ko? Bari na kamaka"
Murmushi Momy dake rufe first-aid d'in tayi don ita kanta taga lokacin da hakan tafaru, kawai bata zata tajimu bane shiyasa ta basar tayi kamar bata ganeta ba, kallon Ra'ees tayi tare da cewa,

YOU ARE READING
SAI DAKE.!
Historical FictionSAI DAKE.! Qagaggen labarine Mai cike da tarin darussa da kuma qayatacciyar soyayya da zata zamuku da wani salo na zazzafar qauna, SAI DAKE..! labarine daya had'a zuciya biyu a waje d'aya bisa wanzuwar qundin qaddarar kowanensu.