PAGE__66

84 2 0
                                    

💎 _page 66_💎

*SAI DAKE!*🫀
       _written by_
*BILLY S FARI💎*

© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

_follow me on my Wattpad @Billysfari9 https://www.wattpad.com/story/281979031?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=h1hTYUDmeeoMp11b3lTkCiCDDLppuAl%2B6kbyiK4cGXQ5e2Fg7YLuARy9Dcp%2BEVPxUXJImhmoAGRg72rOwrncWtECkGHwwVNmdJ%2BFopJSUVlXXQah7ciB4BN9KGwZqXho_
______________________________
_*OUM IMAN, SADIYA ZANGO (MEAMAH)* Yau gaisuwar takuce mai cike da fatan alkhairi agareku, bakina kad'ai bazai isa yafid'i irin tarin mutuntakar da kuke da ita agareni ba, FILLAH ina jin dad'i aduk sadda nayi arba da comment d'inku, hakan ke qara mani karsashi wajen yin sabon update domin nima na faranta maku, ku d'in nawane na hannun dama kuma na musamman, amincin ALLAH ya tabbata agareku da dukkanin ahalinku baki d'aya, ngd sosai sosai, jazakumullakhu bikhair wa arju anyajalallahu min ahalil jannah💞🤝_
         💎💎💎💎

Ra'ees kaine babba acikin 'yan uwanka kuma uaine zaka iya hawan kujerar da nake da ita a cikin gidan nan aduk lokacin da akace bana nan ko kuma bana duniya, alhamdulillah abubuwa sun faru da yawa na rayuwa, wud'anda darasine acikin tamu rayuwar kuma faruwarsu ya zamo alkhairi ga dukkanin mu, bazan hanaka siyasa ba tunda kanada sha'awar ta, amma ina so kasani kafin kima, daraja da kuma martabarka sukai yanda ake so acikin siyasa saika zamo mai taushin hali, na farko kenan, abu na biyu sai hankalinka ya gama kammala yanda ake buqata shine ka ajiye iyali, na uku kuma kazamo mai neman kusanci da ubangijinka sosai saboda ya dafamaka ga rahamar mulkinka, mulki abune mai wahala, sannan duk wanda aka bawa shi to ba qaramin nauyi aka d'ora masa ba sai ya maida hankali sosai, bisa haka nake so kafin nan da wata d'aya da za'a gudanar da zab'e kafiddo da yarinyar da kake so, Ina so gaba d'ayanku ku uku na saukar da nauyina na qarshe akanku domin nasamu natsuwa, na sani Aryan baida matsala yafidda wacce yake so kuma tuni kowa yasan da maganar kai da d'an uwanka Musaddeq ku kuka rage, saboda haka ina son kowanenku ya nemo izini daga wajen iyayen wacce yake so idan kunada domin muje anema masa aurenta, ku nake sauraro.

"Dady ni babu wacce nake so gaskiya sai Waheeda, kuma Momy tasan da hakan ba tun yau ba" yaqare maganar had'e da ajiye wayar hannunsa yana gyara zamansa akan kujerar tare da kallon Momy, cikin jinjina rashin kunya irinta Ra'ees Momy tayo masa daqquwa had'e da cewa,

"Gidanku, idan nasan da hakan ba tun yau ba, ita Waheedar na sonka ne?, Kajimun yaro" taqare maganar tana kallon Dady dake murmushi yana kallon yanda Ra'ees ke faman sissinne kai qasa yana Sosa qeyar kansa,

"To kaji abunda Momynka tace, don haka ni bazan nema maka auren Waheeda ba har sai na tabbatar kaje kanemi soyayyarta kuma ta amince, wannan shine"

"Amma Dady 1month fa kace?"

"Eh do your effort, ina Musaddeq?"

"Na aikesa ya amso mun saqo wajen qawata hajia Nana ruqayya"

"To idan ya dawo ki isar da saqona wajensa, nagaji da kallonsu haka zabga zabga acikin gidana ba mata, ko ya kika ce?"

"Hakane, to meye amfanin zaman nasu a haka, ALLAH dai ya tabbatar mana da alkhairi kawai, qwara su d'aga nima nasha iska" duk sukasa dariya in banda Aryan da gaba d'aya hankalinsa baya kansa saboda kiran wayoyin Barrister Safwan da yaketa famanyi suna ringing ba'a d'aga ba, koda ya sake kira sai kuma yaga ansabmashi line busy, ma'ana ana amfanin amsa wani kiran da wayar, d'an dakatawa yayi na mintota kafin ya sake gwada kiran karo naba adadi, tana shigo suka jiyo ankwala wata irin qara daga can ya b'angaren part d'in Momy wanda hakan yasa ya kasa cewa komai suka fita aguje suka nufi part d'in gaba d'aya, gogan naku da har ya gama gano sautin qarar na Waheeda ne tuni ya nufi wajen d'akinta kai tsaye yana qoqarin bud'e, wata irin tsawa Momy ta daka masa da tasashi saurin jaye hannunsa daya d'ora akan handle d'in zai bud'e, tayi hakanne saboda batasan awane yanayi zai iya riskar waheedar ba aciki, qoqarin bud'e qofar tafarayi lokacin data qaraso wajen amma sai tajita a rufe, cikin rud'ewa ta shiga bubbuga qofar tana kiran,

SAI DAKE.!Where stories live. Discover now