💎 _page 52_💎
*SAI DAKE!*🫀
_written by_
*BILLY S FARI💎*© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
_Follow me on Wattpad @Billysfari9 https://www.wattpad.com/story/281979031?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=Billysfari9&wp_originator=h1hTYUDmeeoMp11b3lTkCiCDDLppuAl%2B6kbyiK4cGXQ5e2Fg7YLuARy9Dcp%2BEVPxUXJImhmoAGRg72rOwrncWtECkGHwwVNmdJ%2BFopJSUVlXXQah7ciB4BN9KGwZqXho_
💎💎💎💎
A taqaice dai sister Asma'u bata bar asibitin ba sai misalin qarfe tara nadare, lokacin har inspector Ahmad ya farka, tare suka je wajensa ita da sista zarah da har lokacin tashinta yayi, qin barinsu 'yan sanda sukayi su shiga ganinsa har saida ta nuna masu i.d card d'inta sannan ta tabbatar masu da kowace sister Asma'u sannan suka shiga, ba kowa wajensa sai mahaifinsa da mahaifiyarsa da kuma mahaifiyarta ita sister zarah d'in, yana kwance kan gadon an nannad'e kansa da fuskarsa da bandej, sai wasu wurare dake da miki da aka lallaqa masa plista awajen, hannunsa kuma na laqe da qarin jinin da akeyi masa da take jininsa ya zuba sosai, haka ma har lokacin akwai sauran wata na'ura aqirjinsa, cike da tausayawa sista Asma'u takallesa tayi masa sannu haka ma itama sistar zarah tayi masa sannu tare da addu'ar samun sauqi sannan tacewa mahaifiyarta ita zata wuce gida lokacin tashinta aiki yayi, sai da tayi ajiyar zuciya sannan yace,
"To ALLAH ya kiyaye kuma ya kaiki lafiya, agaida yaran"
"To umma zasuji, ALLAH yaqara sauqi"
"Amin ya ALLAH, sannu sista Asma'u, mungode sosai kema ALLAH yayi maki albarka yasa kigama lafiya, ALLAH ya albarkaci zuriarki ya karesu aduk inda suka shiga, mungode mungode sosai ALLAH ya yawaita mana irinku aduniya"
"Amin umma" sister Asma'u tafad'a tana maijin dad'in wud'an nan addu'o'in da tayi mata, Nan mahaifin inspector Ahmad da mahaifiyarsa suma suka qara yimata godiya had'e da saka mata albarka, da nema mata kariya ga dukkanin abunqi aduniya, wannan karon har jawaye tayi saboda Jin dad'in addu'o'in don batada buri aduniya irin taga ta faranta ran wasu zukata har yakai ga sun bita da kyawawan addu'o'i, sun jima aciki kafin suyi sallama sista zarah ta d'auketa da motarta takaita har gida itama taqara mata da godiya, murmushi tayi had'e da cewa,
"Bakomai sista zarah, ai wannan yiwa kaine da kuma qasata, ke kanki ina yimaki godiya, badon kin bayyana a wannan gab'ar a matsayin 'yar uwar inspector Ahmad ba da bansan yanda zan kwashe da case d'in nan ba, kin san halin mutanen namu 'yan sanda, sai kaga sun maida cibi yazama qari"
"Hakane, ALLAH yasa mudace, bari natfi nasan akwai gajiya atattare dake kada nasake tsaidaki"
"To saida safe nagode" .
Koda sister Asma'u tashiga gidansu dake can g.r.a quarters ta tadda har bahijja da Shu'uba sunyi bacci, Enaya da subai'a ne kad'ai zaune afalo suna zaman jiranta, tare suka rugo suka rungumeta tayi murmushi had'e da cewa,
"Ina yarana? Ina dai sunci abinci kafin suyi bacci?"
"Eh sunci, Abbanmu ma yakira mun gaisa yace mutabbatar idan kindawo ankulle ko ina kuma anyi addu'a, wai kuma gobe shima zaizo, halama Mamy meke faruwa?" Subai'a tafad'a tana karb'ar mayafi da glass d'in data cire a hannunta, murmushi tayi had'e da girgiza kai kafin tace,
"Babu komai Subai'a, kawai Abbanku baya so muna nisa dashi"
"Mamy amma ai shi yace muzo, shi sai jibi zai biyo bayanmu"
"Eh, ya canza shawara ne" har zata sake cewa wani abu Enaya ta dalla mata harara, ba shiri tabar wajen ita kuma tace,
"Mamy da gaskiyar Abbanmu fa, wlh ni tun d'azu atsorace nake"

YOU ARE READING
SAI DAKE.!
Historical FictionSAI DAKE.! Qagaggen labarine Mai cike da tarin darussa da kuma qayatacciyar soyayya da zata zamuku da wani salo na zazzafar qauna, SAI DAKE..! labarine daya had'a zuciya biyu a waje d'aya bisa wanzuwar qundin qaddarar kowanensu.