proloque

2K 128 13
                                    

PROLOGUE
#Surayyahms

*FITAR RANA...*
_......faduwarsa_

Alhamdullahi rabbil Aalameen.This is a short, hopely amazing story of a witty-smart girl wasimé  Aliyou in her love_hate relationship with her biggest critic yet wildest fantasy,i hope u'did enjoy it.thanks!😘

BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM.

6:15pm Bunu: Shammo cluster,east language of kainji,toro L.G.A bauchi state.

Lokacine da almuru ya ƙeto gab gabotawar sallahn magriba. wata ƙibabbiyar matace wacce a shekaru bazata haura sama da arba'in ba, kalar fatar jikinta ɓaki kirin ta ƙife irin fallen zanin atamfar dake jikinta akanta tayi lullubi dashi har saman idanunta tamkar wacce bataso a kalli tsananin munin fuskarta, dauƙe take da man fetur da kuma ashana ahannunta, ta tsaya a ƙofar wani matsaikaicin gida ginin blo dayajima sosai duk ya balangwaje ya tsofe ginin ya karsashe wanda ana taɓa bangon ƙasane kawai ke zuba.

Daga cikin gidan Babu abunda ke tashi acikin dan tsurkukun dakin nasu sama da zautaccen bugun sautin wahalallaleyar numfashin mace wacce amonsa tayi kama da kamar ranta ake zarewa acikin tukikin ciwon naƙuda mai azabtarwa da kuma radadi,ita kadai sai murƙususu takeyi acikin dakinta tana tauna laɓɓanta tana wayyo Allahnta amma kashh!! shiru kakeji babu wanda ya kawo mata doƙi.

Bisa Kallo daya kayiwa matar zaka fahimce cewa bazata wuce kimanin shekaru arbain da takwas a haife ba,murmurarreyar mace ce mai ginannen jiki wanda duk da alamun wahala da talauci dayayi mata naso ajikinta da kangon dakinta bazai taba hanaka kallon kyakkwar surar halitta da Allah yay mata ba.,ba kuma ina nufin tsantsar kyauna kwatantacin siffar ƴayan aljanu ba,a a, .ina nufin itama baqace sidik original melanin beauty, mai dauke da natural skin na matanmu na mutan _biu(a jahar maiduguri)_ tabbas matar nan ta mallaki sulbabben sheqin fatar su mai kyau da daukar ido,game da dirarren shape da baƙin suman kai dai dai cikon misali.

Har kwatankwacin Misalin tara na dare amma haryanzu shiru,iska ne ya cigaba da kadawa sakamakon yanayin damina ne duhun inya rufa har ba a iya kallon hasken tafin hannu.

Matar can tana waje,mai naƙudar nan itama tana cikin gida tana kkrin fidda nishi,kuma Dukkansu basu rusuna akan qudurorinsu ba.

Duk wani addua daya fixgo kanshi cikin bakinta da zucyarta yinshi kawai takeyi danta samu saukin azabar naƙuda datake sha ajikinta dan kuwa yau Shekarunta 30 kenan da yin aure a duniya amma bata taɓa samun haihuwa ba sai a wannan ƙaron da jiki ya riga ya ragwabe tsufa kuma yaxo mata rayuwa ya kuma musu tsanani ita da mijinta malam hassan(aliyu) denge a hannun muguwar amaryasa Anmuna.

Maimunatu garba,
wacce akafi sani da Anmunah mayya yar gidan garba maye ta kasance tamkar wata mujiya ce acikin alummar shammo ta kabilar ribinawa a jihar bauchi, kasancewar zargin da akeyiwa mahaifinta nacewa shi mayene Shekara da shekaru bacin duk wani alamu sun nuna hakan amma rashin ƙwakkwarn shaidu shi ya hana a gurfanar dashi.Qaddara shiya janyo aure tsakanin anmuna da malam hassan mijin badiatu wanda tunda suka ƙafa alƙalmin tarihin zaman auren su basu taba sabawa juna ba,mutane ne masu tsantsar hkuri da juriya tare da takantsantsan da rayuwarsu gameda kyakkwar zuciya,a tunanin su kawo anmuna cikin zamantakewar su zai iya jawo musu albarkan haihuwa bayan tsawon shekaru da sukaja basu samu ɗa ko ƴa ba,anmuna takai shekaru sama da arba'in babu wanda ya taba taya aurenta sabida halin mahaifinta na maita,acikin tsangwama tay rayuwarta,malam hassan da badiatu ne kawai suka tausaya mata, amma sai abun yazo musu da sabuwar qaddara wanda basu tabayin tsammanin cin karo dashi ba.

Dan kuwa tunda anmuna ta shigo cikin gidan su da sunan aure yau shekaru goma kenan malam hassan da matarsa badiatu suke cikin tasƙon rayuwa mai tsanani.

Duk wani albarkan Rayuwarsu saida tayi fatali dashi,ta talautasu ta muzanta su,tayi zaman diris akan dukiyarsu sannan ta sassaka musu ciwuka kala kala ajikinsu.

FITAR RANAWhere stories live. Discover now