friends

499 43 3
                                    

*FITAR RANA...*
_......faduwarsa_

BISMILLAHIRRAHMANIRAHEEM.

No.10

Daga club bai tsaya akoina ba ya nufa gida,nan ma ya samu koina shiru alaman har sunyi bacci,wutar falon ya kunna snn ya cire rigar sanyinshi ya aje akan cushion,bude fridge yay ya dauko ruwan sanyi sosai baidamu da ya zuba a kofi ya soma kwankwada kamar daman kishin ruwan ne ya damesa.

Komawa kan kujera yay ya zauna ayayin da wata Nannauyar ajiyar zcya ta kufce masa gabaki daya Ya rasa abunda yake masa dadi,ya rasa mesa zciyarsa ta kasa samun sukuni musmn tunda saheeb ya soma shiga rayuwar wasime,lumshe idanunshi yay ahankli yana tuna blowing masa kisses din da saheeb yay dazu,tun a lkcin yakejin sauyin bugun numfashin sa saidai wann karon baya tsammanin fushi yakeji akanta ko akan saheeb din Wani abu daban yakeji mai kama da fargaba, yasan waye abokinshi saheeb ciki da bai,tarbiya yay masa ƙaranci.su irin rayuwar turawan nan aka dora rayuwarsu akai komi kawai yinshi sukeyi babu kulawa da right or wrong ko wani hakkin addini,har cikin ranshi yasoma jin kamar baison alakar wasime da kowa ma sbida aynxu mutane sun dawo abun tsoro!

Ya dade acikin wannan tunanin can sann ya miƙe ya haura sama ya nufi cikin dakinshi,a hnkli ya bude kofarsa ya shiga snn ya kunna wuta,wani ajiyar zcya ya sauke tare da karewa dakin nasa kallo,direct gaban wani reading table ya zuzzzuba tarkacenshi his phones nd evrything yay freeing knsa,drawar wajen ya bude da wata key ya dauko wani bunch of keys snn ya fito waje ya kulle main door yabi ya lelleka sashukan iyayensa yaga komi normal ya kashe wutar falonsun,harya kama hanya zaiyi sama ya duba bilti saikuma aransa yaji kamar bazai iyaba.

Haka ya dinga yi kwana biyu,zai duba koina a gidan to make sure evrything is gud amma sam sam baiya iya kaiwa dakin su wasime  ya kuma rasa kwakwran dalilinsa nayin hakan

And sometimes haka zai dingajin kamar yana sha'awar kallon fuskar yarinyar amma haryau dai bai tabbatar da cewa a zahiri ma hakan yakeji aransa ba,shide kullum ransa a bace ne.barinma da saheeb ya soma isarsa da hirarta basa waya na scnds guda bai tambaye lapiyarta ba.

Kwana biyu haka in saheeb ya samu time yabiyo ta gidan su haka zaiganshi ya lodo ma wasimé kayan kwamulashe ice creams chokolates biscuits,su wasimé kuwa tuni harta sake jiki dashi hirar kauyensu dana kawayenta kullum tana basa haka zaita dariya yana kulewa kamar sabon kamu.

Yanzu inta gansa a gidan da gudunta take zuwa tamasa oyoyo shikuma ya dagata sama, kota tahau kan cinyarsa ta zauna kota riko hannunsa suna hira suna dariya sosai,har cikin ran taheer bason hakan yakei ba shisa kwata kwata baya yarda su zamna a inuwa guda dashi,Mostly in saheeb ya zo saidai suzauna a falo shi yana can sama a dakinshi,zaman su a daki ma tuni ya soke snn duk magiya duk roko haka ya hana saheeb fita koina da ita.

After few months Ana washe gari sallah. bilti ce ita kadai ta sako wata atamfar classic mai kyau tana ayyukanta a kitchen
Wasimé ta shigo duk jikinta a jiƙe da fitsari da alaman yau bata samu daman yin wankin ba sakamakon ruwan su daya dauƙe "kallo daya bilti tayi mata cikin girgiza kai tace,tab ashe wata baxataje koina ba kenan, yanzun nan fa yaa saheeb dinki yazo kuma ya roki yayanki akan zakuje wajen wasan yara (amusement park)
da kannensa gobe.

"baki buɗe cikin yanayin murna tace "kice Allah?bakinta taji an buge ta riƙo bakin da sauri tana yamutsa fuska"..bilti tace bana hanaki cewa hakan ba?zanmiki karyane?kamar zatay kuka ta girgiza kai tana zumburo baki..bilti tace"kyaji dashi..kika yarda taheer yasan kina fitsarin kwance zaki gane kurenki..

cikin sauri har kirjinta na daka tsalle ta langwabar da wuya sigar magiya tace "bilti toh dan Allah karki fadamai kinga jiyama ya min ihu waidan naje debo ruwa a famfon waje..kumafa aikana malam musa yay yace in debo masa ruwan alola.

"Bilti bata kulata ba,ta dada matsowa kusa da ita tace "toh waishi meyasa baison yara?
batare da ta kalleta ba tace wa kenan? Dan shiru tayi kamar me nazari akan wani abu,can snn ta furta ahankli tace "Ɗahiru mana! Da mamki bilti ta kalleta jin yadda ta furta sunansa gatsau babu saƙayawa"kada kai kawai bilti tay tace"shiya gaya miki haka?kanta ta girgiza alaman a'a kafin tace "yaa saheeb ne ya gayamin!kuma ai gaskiya ne..yo inba haka ba toh meyasa kullum ya ganni a waje saiya koreni"
saiyace min wani "get out" .kullum saiyace min get out..kuma fa kawu Qasimu ma ranar yace mishi ya dinga koyamin karatun boko Kin tuna?
..cikin tsareta da ido bilti tace eh na tuna kila ya manta ne.wasime kije ki cire kayan fitsarin nan surutun nan naki ya isheni haka,batay wani gardama ba ta fita abunta tayi hanyar waje

FITAR RANAWhere stories live. Discover now