desires

504 42 4
                                    

FITAR RANA 13

A fannin su wasimé kuwa tunda ta zamu shiga cikin hadaddiyar hummer jeep din saheeb ta ƙasa aje duwaiwakanta waje guda
Tayi juyi nan tayi juyi can
Komi ma acikin motar ya gama tafiya da imaninta dan kuwa bata taɓa tunanin zata shiga irin wannan babban motar ba.

Shikuwa saheeb baƙaramin dadi yakeji ganinta a kusa dashi ba dan komi nata na burgeshi hatta kayan data saka yau saida yaji aransa inama ace ƙanwarsa ce ita da yanajin duk fadin duniya babu wanda zai kaita gaye da kwalliya da kuma saka tsadaddun kaya..ko ayanzun ma ya qudira aransa cewa he might sumhow take responsibility of her needs,fitinar taheer ne kawai bai shirya fuskanta yanzu ba dan sosai yasan abokin nasa da iya nuna iko akan iyakarsa.

10:40am dot suka iso bakin kofar gate din wani katafaren gida mai tsayin gatanga da babban gate da aka ƙawatashi sosai da bishiyoyin ƙawata muhalli da kuma furanni.

wannan shine babban guest house din da mahaifinshi ya mallaka masa acikin Wata kerarriyar estate da ake cewa millenium zone B inda ma bakasafai zakaga middle class anan ba duk dai gidajen masu hannu da shuni ne a layin irinsu.

security ne baja baja a bakin kofar gidan wanda suna ganin dosowar motarsa suka tashi tsaye suka tsatsaya,ganin mutane tsatsaye da bindigogi yasaka wasime ta koma kan seat dinta taxauna a hnkli snn ta nitsu ta cigaba da kalle kalle.
Gate daddaya daddaya har sau uku aka bude musu kafin suka iske asalin harabar main house din Komi na gidan bugun girma ne masha Allah baki a bude wasime take lekowa da fuskrta waje zcyarta kamar zai diro yay tsalle waje tsabar mamakin datakeji acikin aranta,gani tay kamar wani aljanan duniya aka kawota,ganin ababen duniya da idanuwanta basu taɓa cin karo da shi ba hakan yasa taji kamar ta zauce dan murna, kallan sa tay da wasashen hakwara.
Snn Tace"Nan ne gidan naku?Yana murmushi yace "eh mana...toh sauƙo muje ciki.
batagama rufe baki ba taga harya bude side dinshi ya fito yayo ta side dinta,Bude mata kofar motar yy snn ya riƙo hannayenta tare da taimaka mata ahankli harta samu ta sauƙa, idanuwanta ta gwalo waje cikin tsananin rudewar girma da kyaun muhallin,a yanayin kauyanci da yarinta Tace

"Wayyo Allah na..
Ji katoton gida.....
Ahe anan kake zama yo shiyasa mana bakason daɗewa a gidanmu

Dariya ne ya kufce masa ganin yadda tayi maganan with so much ignorant sai kalle kalle takeyi abunta, jawo hannunta yy suka nufi ciki.

A bakin kofar wani katafaren palo suka tsaya snn ya danna door bell, after like 4mints mai aiki tafito sanye da blue uniform tazo ta bude mai kofa tana dan murmushi,"ure welcome sir.Babu yabo babu fallasa yace "thank u susan."Cikin sauri wasime tace ma mai aikin ina kwana anty?Murmishi mai aikin tay saidai Kafunta amsa saheeb ya wani hade ransa tare da cewa  wasime"wayace miki ki gaisheta toh? ido kawai ta tsura masa cikin rasa mezatace tuno da cewa bilti ta gargade ta akan ta rika gaishe da babba...

Yace "wann Mai aiki nace u dont have to greet her kinji?..ai itace zata gaishe ki bake zaki gaisheta ba.."da wutsiyar ido wasime ta dan sace kallon mai aikin ganin ta babba wuce sa'arta,abun saiya kuma dore mata kai yo shawarar wa zataji kenan na bilti ne kona saheeb?,mai aikin bataji dadin hakan dayay ba amma tasan bata isa ta nuna ba, murmushi tay ta gaida wasimen kawai ta wuce ta tafi tabarsu a tsaye awajen.

"Beauty Karki ƙara gaishe da kowa saina umarce ki

Kanta ta gyada mishi a hankl hade da binshi cikin wata ƙerarrayiyar royal falo daya shige dasu ciki mai niimtaccen sanyin A.c da kuma dadin turarrukan wuta masu sanyin qamshi tana biye dashi abaya har suka iske gaban wasu lumtsa lumtsan cushions milk colour da gold wanda girman su da yawansu kawai yakai acike manyan faluka uku harma ayi ƙari dasu,ga wani babban tv plasma mai girman iya dungu to dungu.

Akan daya daga ckin lumtsatsun kujerar ya dorata ta zauna,"snn ya zauna agefenta yana mai kallon cikin kwayar idanunta dasuke matukar kawatar dashi cikin wani sanyin yanayi mai rikitarwa.

FITAR RANAWhere stories live. Discover now