last

1.3K 61 23
                                    

FITAR RANA 20

ALHAMDULILLAHI.

tun bayan ficewar Taheer a gidan basu karajin duriyarsa ba,Yau duk son wasime dayin wasa da kayan wasanta yaci tura sakamakon tsami da kafarta da hannyenta suka dingayi Baki kirin din haddarin Dake sama ya sakata bacci yau da wurwuri.

Sai wajajen Sha daya da rabi na dare taheer ya dawo bai kula kowa ba ya nufi dakinsa ya kimtsa kansa snn ya sauko kasa,  kitchen ya nufa ya dauko clean plate nd spoon snn ya wuce dakinshi,ledan shoping din daya shigo dasu ya jawo gabansa ya bubbude su,"wani mayyar kamshin chicken wings da soyayyen irish potatoes wanda aka soyashi da ruwan kwai  take suka gauraya wajen da qamshi mai dadi,zuzzubawa yay a plate snn ya budi dayan ledar stater ne na fresh apples,beeries nd apricot blend aciki,a nitse ya zauna yaci abincin shi harya koshi daram snn ya mike yay clearing wajen yaje yay wanka
Ya saka riga da wandon shi na bacci light blue in colour pjamas marar nauyi mai lausassar launi.

Switch dake jikin bango ya danna, wutar dakin ya koma dim marar haske sosai,hayewa yy kan gadonsa ya kwanta yana maida ajiyan zuciya nan da nan bacci mai nauyi ya daukesa.

3.0ck midnight sharp ya farka idanuwan sa suka sauka aka agogon bango,wani irin sanyi ke ratsa gangan jikinshi saboda ruwan Sama da ake kwazawa kamar da bakin kwarya.

Yafi minti goma akwance ya nannade jikinshi da bargo cikin wani yanayi,batare da yay wata motsi ba..sai can daya tuno da cewa wannan lokacin fa mai tsadace ga bawa awajen mahalincinsa snn ya hakura ya diro kasa daga kan gadonsa a kasalance ya nifi toilet yay tsarki snn ya dauro alwala.

Karfe ukun dare kusan lokacine da ubangiji dakanshi yakan sauko sama yanamai tambaya shin ina bawa ba me neman gafara in gafarce shi,ina bawa mai neman wani abu awajena in cika mishi burinsa,barinma da ake kwaza ruwan sama kowani musulmi na kwarai yasan muhimmacin yin adua ayayin da ake ruwan sama,domun kuwa tana daya daga cikin lokutan da ubangijinmu mai rahma yafi amsar bukatan bayinsa cikin gaggawa.

Jallabiyarsa ya zura snn ya shimfida sallaya
Ya tada kabbara a cikin nitsuwa.

Sallan tahajjudi yay har raka"oi goma sha biyu ya hada da shafi'i da wutri domin yin hakan yana da fa'ida sosai musammn ma inbakayi yisu a bayan sallan isha'i ba.

As usual addu,oin samun nasara da kariya ya dingayiwa iyayensa acikin kowani sujada daya gabatar acikin sallan sa harya kammala,yanayi yana mai neman gafara yana kuma neman guidance daga wajen ubangiji akan dukkan lamuran rayuwarsa.

'Lokcin ana neman karfe hudu da rabi na dare ya idar da sallan, awajen ya zauna ya dinga tasbihi yana salati wa Annabi.S.A.W daf zai shafa adduar domin ya gabatar da salatul fijr wasime ta fado mishi acikin ransa...

wani jimmm yyi da nauyin zuciya idanuwan shi a lumshi cikin tunanin rayuwar sa da ita anan gaba,hannun sa ya daga sama yafara rokon Allah abubuwa masu tarin yawa akanta.

Mafi muhimmancin adduar sa shine yana fatan Allah ya sa alakar su ta aure data kullu a bazata ta kasance tarayyar alheri ce agaresu duka na har abada.

Shidinma ayanzu yana da burirrikan sa akanta masu kyau daya boyesu acikin ransa,harga Allah so yake suyi rayuwarsu mai dadi,mai cike da sassanyar kauna da cikakiyar shakuwar da zata kwantar musu da hankli ta kuma saka ma zukatan su farinciki da annashuwa.

Saidai ayanzu hakan bazaiyu ta cikin sauki ko gaggawa ba,dole ne ya daure yay moulding dinta kalar yadda yake so,ya kuna nitsar da tarbiyanta sosai Dan yasan duk abunda yay sanya akai game da ita toh akansa ko yayan sa illar zai kare tunda shi baiya da wani ra'ayin zama da mata biyu...

dan haka ya qudira acikin ranshi cewa dagaske zai zage damtse yy kkri wajen kulawa da tarbiyan wasimén sa harsai ta zamto kalar uwar dayake so ta zama ma yayansa.

FITAR RANAWhere stories live. Discover now