f p 1♥️

173 8 0
                                    

𝑭𝒂𝒕𝒚𝒎𝒂𝒔𝒂𝒓𝒅𝒂𝒖𝒏𝒂✔️

     𝒃𝒐𝒐𝒌 𝒐𝒏𝒆

𝒑𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆 1

Takasance kalar macen datakeso tazama, tanayin rayuwan ta Kaman yanda takeso, babu wanda yake takuramata, ko iyayenta basa matsamata tayi abunda bataso.

Saboda sun yarda da ita, sun san bazata taba jawowa kanta abun da zatayi dana sani ba, takasance mace wacce take yin duk abunda takeso, Kuma wacce take samun duk abunda takeso.

Tana rayuwane according to yanda ta tsara, musamman fannin soyayya, tana soyayya da duk wanda take so batare datasha wahala ba Kuma badan wani abu ba, kawai yakasance tun tasowanta bata taba neman abu tarasaba.

So she is use to it,a duk sanda zatayi sabon saurayi takanji hakan ajikinta ta hanyar yawan bugawar da zuciyan ta takeyi a koda yaushe, akwai mutane biyu datake so Kaman rayuwan ta, AMEEN dakuma AMJAD.

Sudin cikin samarinta sutakeyiwa son dabatasan kalarshiba, Kuma acikin su biyun AMJAD yakasance na farko a zuciyata tana mishi so irin wanda batayiwa ko wane dan adam shi, ya kasance wani sashi na jiki da zuciyan ta.

Amma 'kaddarar data kasance taka baka isa ka guje mata ba, 'kaddararta takasance mafi zaman kaddara saboda ko amafarki bata sakawa ranta rayuwa da wanda ba Amjad ba .

AMJAD yakasance 'kanin matar mahaifinta ne Kuma a gida daya suke zaune tun suna yara.

Ayaune 5 ga watan December shekara ta dubu biyu da ashirin da daya 'kaddara tayi sanadiyyar juyewar rayuwarta.

'Kaddara tayi sanadiyyar shigarta wani hali da wata rayuwa wacce Bata san sanda zata fita ba, wata kila har abada wata kila Kuma jarrabawarta Kenan.

Tafiya take da waya a hannun ta tana duba abu a ciki, dariya take yi wacce daka gani kasan tana cikin matsanancin farin ciki.

Lofan gate tabud'e kasancewan daga islamiyya take Kuma islamiyyan a kofan gidansu yake, yaune ta rubuta takardan karshe na gama secondary school.

Kuma yaune mahaifin ta yabata kalan wayan da tafi so arayuwan ta, so murna biyu take ciki abun da bata saniba yau rayuwan ta zai canja daka farin ciki xuwa bakin ciki,koda ta shiga gate na farko anan ta iske malaminta wanda yake Kaman yayanta, so ta tsaya suna Magana akan sabuwar wakar da zasuyi sai wayan ta yayi ringing.

Koda taduba sai taga ABEY MY LOVE, mahaifinta Kenan wanda take kira da ABEY , receiving na call din tayi sannan ta shiga gate na biyu, tana karasa shiga kunnuwan ta sukajiye mata abun da yayi sanadiyyar sa taji Kaman rugugin tsawa a xuciyar ta.

Daman tunda ta dauka batayi maganaba tana sauraron abunda mahaifin ta yake fada acikin wayan,

D'IYATA, SUNAN DAYAKE KIRANTA DASHI KENAN, KINSAN DUK WANI MAHAIFI BAZAI SO YA ZA'BARWA 'YAR SHI ABUNDA ZAI CUTAR DA ITA BA, KUMA NASANKI KINA YIN DUK ABUNDA NA UMURCEKI DASHI SHIYASA NAKE ROKON ALFARMA DA KI AURI YAYANKI HABBAN , IDAN KIKAYIMUN HAKAN ZANJI DADI KUMA HAKAN ZAI SAKANI FARIN CIKI.

Hannun ta taji yafara rawa wayanta na shirin faduwa, dakyar da ikon Allah ta iya tashi ta karasa shiga gate din dazai sa da ta da ainihin cikin gidan, tana karasa shiga kai tsaye part din mamanta ta nufa.

Ko da tashiga siser dinta Hamdan tana palorn su a zaune , a bakin kofa ta zube tana maida numfashi , dai dai lokacin wani kiran ya sake shigo wa wayan ta.

Dakyar ta iya daga wa, saboda batason jin abunda Abey zai fada mata.

Koda ta dauka idanun Hamdan na kanta, sai tasaka wayan a handsfree , ananne Hamdan taji meyake faruwa , daganan Abey yabama Fatouma mintuna 30 tayi shawara.

Ananne Hamdan ta tada masifa saboda mama bata nan, rike hannun Fatouma tayi suka shiga dakinta sannan ta dauki waya ta kira yayansu Musty , ba'afi mintuna biyar ba sai gashi ya shigo dakin ranshi amatukar bace.

Bai tsaya sauraren komai ba yafara yiwa Fatouma fada, dan ance zatayi aure zata zauna tanaiwa muta ne kuka, hannun Hamdan yaja suka fice daga dakin, ita kuwa Fatouma washroom tashiga.

Tana shiga tasakar wa kanta ruwan sanyi sabo da ji takeyi Kaman ana yanka naman jikinta, a lokacinne Kuma wani irin kuka yazo mata.

Wanda a tsawon rayuwar ta bata taba yin kalanshiba, ana cikin hakanne Kuma Hamdan tashigo , sosai hankalinta yatashi ganin halin da Fatouma take ciki, dai dai lokacin Kuma wayan ta yayi ringing.

Wani irin buga wa zuciyan ta yayi wanda hakan ya farune saboda tasan Abey ne yake kira, Hamdan ce ta dauko wayan daga cikin 'daki tare da daga kiran tasaka a handsfree.

Muryan Abey yafito daga wayan yafito yana fading, mintuna talatin sun cika 'diyata menene amsarki, Hamdan nacewa tace aa.

Amma a zuciyar ta tanajin komai mahaifin ta ya nema a gurin ta bai kamata ta'kiyi ba saboda kamar ta sabawa Allah ne, saboda tasan mahifinta bai taba matsa mata tayi abuba.

Kuma yana yimata duk wani abu da take so, batare da wani dogon tunaniba, ta amsa mishi da cewa, ABEY ALLAH YA ZABA MANA ABUN DA YAFI ZAMA ALKHAIRI.

Wani irin kallo mai cike da tausayi Hamdan take yimata, shikuwa Abey cike da farin ciki yake saka mata albarka bayan wasu sakanni yayi hanging call din.

Jawo ta Hamdan tayi ta rungume ta hawaye na zuba a idanun ta, saboda tasan qanuwar ta zata cutu a wannan auren, saboda hakurin ta da rashin Magana, shi kuma wanda za'a aura mata sam ba mijin daya kamata ta aura bane.

Sai da Fatouma tayi kuka har idanuwan ta suka yi jawur sanna Hamdan ta d'ago ta suka dawo cikin dakin, gudun kar sanyi yashige ta yasa Hamdan ta taimaka mata ta canja kaya tasha magani sannan ta kwantar da ita tare da ficewa daga dakin.

Wani irin rawa jikin ta yakeyi saboda Abey yace anjima Hammad zaizo , Kuma tasan dole tare da AMJAD zasuxo , saboda tasan su abokaine.

Zuciyar ta bugawa takeyi Kaman zata faso 'kirjin ta saboda har tanajin karan bugun a waje, wayan ta ta dauka tare da kamo numban AMJAD tayi dialing, ringing daya ya dauka tare da fadin "Fatouna".

Wani rin kuka mai daga hankali ta saki wanda yasa zuciyar AMJAD bugawa da mugun karfi, bai sake cewa komai ba ya kashe wayan ya nufo cikin gidan , Hamdan naganin shi tasan mai faruwa ta faru , sunan shi takira.

Dukda baya cikin natsuwar shi hakan bai hanashi tsayawa ba, tasowa tayi ta karaso inda yake ta kama hannayenshi guda tare da fadin, "duk abunda yasamu dan adam kaddararshice a hakan".

Ku rungumi kaddara ayanda tazo muku inshaAllah zakuci ribar hakan.

Jaye hannayen shi yayi yanufi dakin Fatouma hankali atashe , saboda yazaci wani abunne yasame ta.

Koda yatura kofan, tana kwance hawaye na tsiyaya a fuskan ta duk wani mai imani dole ya tausaya mata, dasauri ya karasa gurinta , tana ganin shi ta mika mishi hannu.

Akwai abunda bakin ta yakeson fada amma harshen ta yayi mata nauyi, yana karaso wa ya tada ita daga zaunen tare da rungume ta Kaman wanda za'a raba da mahaifiyarsa.

Sai lokacin Fatouma ta iya bude bakin ta tafara magana, "Hammana , (dayake haka take kiranshi), Hammana ka yafe mun nayi sandiyyar rushewar rayuwar mu.

Wallahi ina sonka son da ko kaina bana yiwa shi, ina ji idan na rasa ka Kaman na rasa numfashina, yau na yanke wani hukunci ba tare da sanin ka ba, a sanadiyyar hakan inaji Kaman bazan kara mintuna arayeba.

Inaji kaman naci amanan ka naci amanan soyayyar da kakeyimun, amma Kuma nasan bazakaso insa'bawa Waleed ba Kuma nasan bazaka ga laifi na ba.

Hammana kayimun kowane kalan hukunci amma karkace zaka yi fushi dani, karkace zaka saka zuciya ta cikin bakin ciki, kayafemun, nan da wata daya za'a dauramun aure da Habban".

Kaman saukan aradu haka AMJAD yaji wannan maganan akunnuwan shi, bai san sanda ya ture ta bayaba tareda tashi daga kan gadon ya....

ya Allah am so interested in this book yanzun aka fara labarin karda kubari abarku abaya

#𝒇𝒂𝒕𝒚𝒎𝒂𝒔𝒂𝒓𝒅𝒂𝒖𝒏𝒂

#𝒎𝒆𝒆𝒆𝒓𝒂𝒓𝒉

ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶 Where stories live. Discover now