f p 5♥️

29 3 0
                                    

   *fatymasardauna*

*by meeerarh*

  *5*

       (Barkanmu da sallah 'yan uwa dafatar anyi sallah lafiya, Allah ya maimaita mana😊)

      Zaro ido tayi saboda ganin da ta yiwa Musty tsaye a palon yana kallon ta, wani irin duka kirjin ta yayi saboda tabbas idan har yana palon tun tuni,  Yasan mai yafaru.

   Tafiya tafara yi jikin ta duk asanyaye taje inda yake ta duka tare da kama hannayen sa ta zaunar dashi akan kujera.

     Fuskan ta ya shafa cike da tausaya wa 'kanuwan nashi, magana ya fara yi mata cikin tattausan lafazi.

    "Nasan yaune ranan karshe da soyayyar dake wanzuwa a tsakanin ku zata rabe.

     Karki ji komai nasan yanda kike ji, kuma InshaAllah zan rufa miki asiri kaman yanda zan rufa wa kaina".

    Runguman shi tayi tare da sakin kuka mai matukar ta'ba zuciya, bayan wasu mintota ya tabbatar da ta samu relief sannan ya kama hannun ta suka nufi cikin gidan.

     Koda suka shiga a Palo suka tarar da mama, hankali atashe mama tayo kansu tana tambayan mai ya faru.

  Saboda yanda taga gaba daya Fatou ta yakuce kaman an bata kashi.

   Murmushi Musty yayi cikin dakiya ya ce, "wallahi fita mukayi dani da ita da Amjad,  so muna hanyar dawowa tace kanta na ciwo.

   Shinefa da muka je asibiti sai da suka riketa wai bata da lafiya amma ba'a kawota andubataba".

   Numfashi mama tasauke tare da fa'din, "c'mon Fatou so nawa zan fa'da miki ki cire komai a ranki.

     Wuce muje kiyi wanka kici abinci , haba duk kinbi kin lalace kaman ba keba,  gaskiya idan ba kyason 'bacin raina karna sake jin kalan hakan".

     Hawayen dasuke neman zubomata tayi saurin tare wa tare da rungume maman Nata tafara fa'din.

    "Ina farin ciki mamana, yau Hammana yabani duk wani farin ciki amatsayin kyautar bikina".

    Jin yanda take maganane ya saka mama dagowa tare da kallon cikin idanuwan ta.

    Tabbas idan ba 'karya idanuwan ta suka yi mata ba yarinyarnan ba ta da cikakkar lafiya .

   Janta tayi suka nufi 'daki bayan Musty yayi musu saida safe.

   
   Wanka ta sakata tayi tasaka pjamis tare da kwantar da ita kaman 'karaman yarinya.

Tayi kusan awanni biyu sannan wani wahalallen barci ya 'dauketa.

     RANAR ASABAR RANAR 'DAURIN AURE😭

  

    
    Dawani irin matsanancin ciwon kai tatashi a yayinda Amjad yake can daki yana fama da matsanancin ciwon kan shima.

  Hamdan ce ta shigo 'dakin dan kawomata ruwan lalle wanda yake al'adar hausawa a duk ranar aurar da 'ya mace.

  Dakyar da su'din goshi tasamu ta tashi ta shiga toilet, numfashi ta sauke ganin yanda dakin ta yayi mugun datti.

    Gyaran dakin tafarayi tana mitar wannan al'amari , Fatou da ta kasance mace mai tsabta ce tabar 'dakin ta a haka.

      Cikin yan mintota saiga Fatou ta fito,  zama tayi agefen gado tare da fa'din.

"Yanzun saura awa daya na zama matar wani wanda ba Amjad ba ko Hamdan".

    Numfashi Hamdan ta sauke tare da zama a gefen ta.

     Kafa'dan ta ta dafa tare da sharema ta hawayen da suka sulalo daga idanun ta.

      "Yanzu karfe goma, kuma shadaya za'a 'daura, ki cire komai a ranki.

     Yanzu Habban shine duniyarki kuma shine lakhirarki, shine farin cikin ki kuma shine ba'kin cikinki,  shine aljannarki kuma shine wutarki, kikasance mai yimishi biyayya komai zai faru, dan bakya sonshi ba hujjabane na 'kin yi mishi biyayya, kimanta da Amjad , kimanta da kin ta'ba sonshi, duk da ba abu bane mai yuwa kamanta masoyinka na farko, amma kiyi iya 'ko'karinki,  kibarwa Allah al'amuranki, karki tambayi dalilin wannan kaddarar,duk abunda kikaga Allah yayi hakan shine alkhairi, ki daina kuka tashi ki shirya Allah yana tare da ke".
   

(@habibtie 🥺na bazan taba mantawa da keba , fatymasardauna kin 'karfafamun guiwa a sanda Shai'dan yakeso na kaucewa hanyar Allah, Kedin masoyitace saboda masoyine kawai zai fada maka gaskiya a sanda idanuwan ka suka rufe, Allah ya kawo ranar dazan saka miki ina sonki saboda Allah,  Ke'din ta musammance a rayuwa ta, kuma abun da ban fa'damiki ba, ina son mijina a lokacin zuciyace taso ta sakani cikin mawuyacin hali, amma kinyi sanadiyyar da zuciyar batayi tasiri akaina ba Allah yasakamiki da mafificin alkhairi yabaki miji mafi alkhairi 🥺♥️)

    

#MEEERARH

ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶 Where stories live. Discover now