f p 11♥️

32 4 0
                                    

♥️FATYMASARDAUNA♥️

    *eleven*

#meeerarh

Wasu abubuwa ne suketa  faruwa da Fatou ta kasa ganewa,  Yawan zazzabi,  ciwon kai, sai kuma amai da take yawan yi da safiyar Allah.

Yau da safe Fatou na d'aki sai kwara amai takeyi a kan gadon ta, shikuwa Habban da yaga har tara na safe bata fito ba, sai ya kasa natsuwa, yajira har 9:30 ok zata fito amma bata fito ba.

Tashi yayi ya nufi d'akin ta yana fargabar abun da hakan zai iya jawowa, saboda tun da suka shirya tsakaninsu bayason yayi abunda zai sa tace baiyi daidai ba.

Tura k'ofar yayi bakinsa d'auke da sallama, da mugun sauri ya isa inda take saboda halin daya ganta a ciki.

Amai yayi kaca kaca da jikin ta da gadon , saboda tsananin wahala har ta sume.

Gadon ya nufa tare da ciccib'arta ya wuce toilet d'in cikin d'akin,  bayan ya tsabta ce jikin ta ya cire kayan da take sanye dasu.

Doguwar Arabian gown ya saka mata tare da ciccib'arta ya nufi asibiti, bayan gwaje gwajen da akayi , doctor ya tabbatarwa Habban ciki ne da ita na tsawon watanni shida.

Sosai mamaki da farin ciki suka cika shi lokaci d'aya, yayi mamakin yanda akayi ba'a gane hakan ma.

Kuma kasancewar bata da girman ciki yasa basu ganeba, dukda taji wasu sanje sanje  a jikinta.

Sannan tabbas farin cikin da yake ciki ta zarce misali, domin ji yakeyi kaman an mishi albishir d'in makkah.

Ita kuwa Fatou koda ta tashi ta tsinci kanta asibiti batayi mamaki ba, sai fai maganan da taji doctor yanayi shiya d'aga mata hankali.

Saboda me ma sukayi bare ace wai tana da ciki, sam ta kasa gasgata mavanan da gaji yana fad'a.

Shiru tayi tana saurara su , bayan sun gama magana Habban ya k'araso bakin gadon da take kwance.

Ganin idonta biyu yasa shi k'ara fad'ad'a murmushinsa, hannayenta biyu ya rik'e yace, "Fatooouna,  kinga yanda Allah ke lamarin sa, dabararka ba zata tab'a fishsheka ba, Allah ya azurtamu da samun juna biyu, kuma kinsan meye?, watan shifa shida, akwai mamaki ko", ya k'arasa maganar alamun mamaki.

Murmushi tayi mishi, hakan ya sakashi cikin wani kalan farin ciki dabai tab'a shigaba.

Taimaka mata yayi ta tashi sannan yayiwa doctor godiya da kyautar kud'i masu yawa sannan suka fice.

A man hanya ya kira Hamdan ya fad'a mata , kasancewar sun dad'e da shirya wa, bayan Hamdan ya fad'awa mamanshi, sannan mahaifinshi, da Abey, sannan ya kira mama.

A k'arshe ya dannan kiran Amjad,  ring biyu ya d'auka, bayan sun gaisa kaman babu komai a rayukansu, Habban take fad'a masa cewa sun samu k'aruwa.

Matsanancin farin ciki Amjad ya shiga kaman ance shine matar sa take da ciki, sosai yayi wa Habban murna , sannan ya nemi ya bashi Fatou.

Ita kuwa da kunya duk tabi ta rufe ta dukda har yanzu bata yarda akwai cikin ba, mik'a mata wayar yayi ta karb'a dukda batasan waye ba.

Sallama tayi Amjad ya amsa, Jim muryarsa yasa hankalinta ya tashi, saboda gani takeyi kaman taci amananshi .

Har ya gama surutunsa cike da farin ciki bata k'ara ce mishi k'ala ba.

Bayan sunyi sallama ta mik'awa Habban wayar, tana mamakin lokacin da har suka dawo haka, bayan tasan abun da yake tsakaninsu.

Daga nan gidan su Habban suka nufa,cike da farin ciki mahaifiyar sa ta tarbesu.

Sai dare suka bar gidan suka nufo gidansu.

*YAU BANYI NIYYAR YIN POST BA , AMMA SABODA FARIN CIKIN DA NAKE CIKI, KASANCEWAR HABIBTIE NA♥️(FATYMASARDAUNA)♥️ TA DAWO ONLINE, YASA NAYI TYPING D'IN , SAI MUN HAD'U JIBI, PLEASE VOTES COMMENTS AND SHARES, HAKAN KAMAN K'ARFAFAMUN GUIWA NE,WELCOME BACK HABIBTIE I REALLY MISSED YOU*

#meeerarh





ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶 Where stories live. Discover now