f p 14♥️

33 3 0
                                    

♡fatymasardauna ♡

    ♡Written by meeerarh♡

         ♡page 14♡

♡second to the last page♡

7:50pm

AIRPORT

Habban ne a tsaye yana jirar saukar jirginsu Abey, sosai yake jin farin cikin dawowar su.

Ai kuwa 8:00pm dot jirgin su ya sauka, bayan wasu mintota sai gasu sun fito, Amjad, Hamdan,  Abey,  Mama, haka suke tafiya a jere.

Hangosa da sukayi yasa dukkansu suka fad'ad'a murmushinsu, nufan su yayi shima yana murmushin.

Amjad ya fara Hugging so tight,  cause they are now best friends,  bayan sun yi breaking hug d'in ya duk'a har k'asa ya gaida Abey da Mama, bayan ya tashi suka yi musabaha da Hamdan tana tambayarsa Fattou.

Murmushi yayi yace" tana can tana jirarku a gida, ta shirya muku surprise mai girma", Amjad dake gefe yace"Allah yasa 'yan biyu ne".

Dukka dariya sukayi sannan suka nufi motan da Habban yazo dashi, k'iran G.wagon black colour.

Cikin mintota kad'an suka isa gida kowa na d'aukin ganin Fattou da surprise d'in data shirya.

Sosai workers d'in gidan sukayi farin cikin dawowar su, saboda a lokacin da gasunan sam gidan babu dad'i.

A b'angaren Fattou kuwa tana can ta sa an gaya babban palon Abey, ta saka yaran a small infants bed ta lullub'esu.

Jin k'aran gate yasa  jikin ta har rawa yakeyi saboda matsuwar da tayi su shigo.

Bob's ta kashe sannan ta shige dinning Area dake cikin palon.

Habban kuwa cewa yayi dasu su shiga palon Abey dan anan surprise d'in yake.

Basuyi musu ba suka nufi palon, Jim sukayi ganin gurin babu haske, saga can kuwa Fattou ta yi pressing remote d'in fitilun.

Faux haka haske ya gauraye d'akin, cak dukkansu suka tsaya ganin gado da 'ya'ya a ciki.

Amjad ne yayi saurin isa inda babies d'in suka tare da 'daukan su duka, zirr haka hawaye suka zubo daga idanuwansa.

Rungumesu yayi sosai saboda wani irin so dayaji yana yi musu, musamman macen yarinyar, saboda gani yakeyi kaman 'yar cikinsa ce.

Ita kuwa Fattou ganin yana hawaye yasa duk jikin ta yayi sanyi.

Sum sum ta fito daga dinning arean ta nufo su, ganin ta yasa ya mik'a Mata hannu d'aya dan yama manta da aure a kanta, hi yakeyi kaman matar sa ce.

Ganin haka yasa Murmushin dake fuskar Habban ya k'ara fad'ad'a, Dan yanzu ya k'ara tabbatar da cewa bai yi kuskure akan hukuncin da ya yanke ba.

Su kuwa su Hamdan sosai surprise d'in ya shigesu,  wai har yaushe aka San da cikin Fattou bare ace har ta haihu.

Bayan komai ya lafa dukkansu sun nuna murnarsu sosai da farin ciki.

Habban ya nemi dasu zauna da akwai magana a bakin sa, bayan sun zauna ya gyara murya ya fara magana.

"Akwai wani hukunci dana yanke, amma sai na shawarci iyayena suka goyamun baya, dukda badu so ba , amma suna sun tabbatar da hakan shine adalci, Fattou ki sani har abada ina sonki , kuma zan ci gaba da sonki, hau bayan da kika haihu, na sakeki saki uku, kuma dukkanmu munsan babu idda a kanki , saboda haka ina rok'on alfarma , Abey dan Allah a d'aurawa Amjad da Fattou aure, saboda aure na da ita ba komai bane face rabo dake tsakaninmu na wad'annan yara, Dan Allah ku gafarce ni, nasan banyi muku adalci ba".

Dukkansu ba k'aramin shock suka ji ba tunda ya ambaci saki, musamman Fattou da ta daina jin komai, a ranta tana tunanin ai komai tayi mishi bai kamata ya yanke wannan hukuncin ba,kuma its fa Allah ya gani tana son mijinta, ita kuwa Hamdan kuka ta fashe dashi , Abey da Mama kuwa basu nuna komai a fuskokinsu ba, dukda sun ji zafin abun da ta aikata, Amjad kuwa kansa kawai ya duk'ar a k'asa yana takaicin Habban.

Abey sauke numfashi yayi yace,"to ALHMDLH tunda hakan kaga yafi, kuma iyayenka sun baka goyon baya, na tabbatarwa ba zasu yi abunda zai cutar daku duka ba, Allah yasa hakan yafi zama mafi alkhairi, Amjad Fattou,  ku shirya gobe bayan sallah asubahi zan d'aura auren ku".

Yana fad'ar haka ya tashi ya shige cikin corridor d'in da zai sadashi da d'akunan sa.

Jiki a sab'ule Mama Hamdan da Fattou da har yanzu bata a natsuwar ta suka fice daga palon, akabar Habban da Amjad a gurin.

A harzuk'e Amjad dake gefen Habban ya kau mishi naushi.

Dukda Habban yaji zafi amma baisa ya rama ba, saima rungume Amjad da yayi a jikin sa, kuka sosai Amjad ya fashe dashi , kukan da baima san na meye ba.

Sai da yayi mai isar sa sannan Habban ya fara magana,"kayi mun afuwa, hakan shine mafi alkhairi,  a d'azu bayan ta aihu, doctor yace macen jaririyar yarinyar tana buk'atar jini, an gwada jini na amma sam bai yi matching da nata ba, bayan an duba jininta aka ga, AA+ne, kuma duk ahalin mu kai ne kad'ai da wannan group d'in , hakan ya tabbatar mun da yarinyar 'yarka ce, bayan na tambayi doctor idan za'a iya haifar 'yan biyu daga maza biyu, ya tabbatarmun cewa tabbas yaran ba sperm d'aya ne ya da suba, kowannensu da mahaifinsa, sannan macen ta girmi namijin da kwana d'aya, hakan ya tabbatarmun da zargina, dalilin dayasa na yanke hukuncin kenan, saboda ina da yak'ini har yau kuma son junanku".

Bayan sun sasanta kansu kowa ya kama gaban sa, Amjad bai ma San meyake yi mishi dad'i ba, gani yakeyi kaman bai yi musu adalciba,  saboda shine dalilin da auren su ya mutu.

The next morning

7:00am

BA ZAKU SO A BARKU A BAYA BA, ADEEMA ONE OF BEST PAID BOOKS.

NORMAL GROUP 200 NAIRA 2 PAGES PER WEEK

V I P GROUP 500 NAIRA 5 PAGES PER WEEK

FREE PAGES ARE COMING REAL SOON, KU HANZARTA SIYA.

THANKS YOU MEEERARH

ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶 Where stories live. Discover now