GABA DA GABANTA 6

322 19 0
                                    

GABA DA GABANTA

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

P6

Follow my Arewabooks account
Ayshercool7724
https://arewabooks.com/u/ayshercool7724

Tafiya take tana ratsa tsakanin gonaki, ga duhu ga babu haske, amma hakan bai dameta ba, babban burinta shine ta ga ta baro cikin ƙauyen nan cikin salama, ba tare da wani ya ganta ba.

Baba Hassan kuwa bacci ma ɓarawo ne ya ɗauke shi, tunanin mafita kawai yake yi, zuciyarsa ta dinga raya masa kawai ya haƙura ya tafi ƙauye, komai zai faru ya faru, idan ya so ya haƙura da aikin, amma gefe guda yana tunanin idan ya bar aikin gadin me zai yi? Wace sana'a zai yi? Wata shawara yake ta jujjuyawa a ransa wadda ba shi da tabaccin zata karɓu.

A haka har garin Allah ya waye, gaba ɗaya jikinsa a sanyaye yake gudanar da komai, yana nan zaune a bakin gate yana ta jujjuya yadda zai ɓullowa lamarin, wajen ƙarfe goma Fadila ta fito ta fita, wajen ƙarfe sha ɗaya kuma Alhaji Ahmad ya fito, cikin wani ash ɗin yadi, an fito masa da motar sa da zai fita da ita.

Alhaji Ahmad yana ƙoƙarin shiga mota, Baba Hassan ya cin masa, cikin girmamawa ya gaisheshi, Alhaji Ahmad ya amsa cikin mutuntawa.

Baba Hassan ya duƙa ya ce "Yallaɓai dan Allah alfarma nake nema".

Alhaji Ahmad ya gyara tsayuwa ya ce "Ina jinka".

Baba Hassan ya ce "Dama Yallaɓai game da 'yar wajena ce, jarrabawar nan ba a samu damar yin ta ba"

"Subhanallah, garin yaya?"

"Kuɗin aka kai a ƙurarraren lokaci, to yarinyar tawa tana son ta yi karatu sosai da sosai, to ka san mutanenmu na karkara, 'yan uwana ba son karatun nata suke ba, to rashin samun damar rubuta jarrabawar ya sanya suna ƙoƙarin su Aurar mini da ita. Shi ne nace dan Allah tun da dama Asabe ta tafi, a taimaka mini a ɗauki yarinyar tawa ta maye gurbin Asabe, idan ya so kuɗin aikin nata sai a sakata a makarantar boko, a dinga biya mata kuɗin makarantar".

Alhaji Ahmad ya ce "Malam Hassan wannan ai ba wani abun damuwa bane, bakomai ka kawota ai ilimi ga 'ya mace abin so ne, idan na dawo an jima ka tuna mini zan yiwa mutan gidan magana, ka kawota".

Wata ƙwallar farinciki ta cikawa Baba Hassan ido, ya zube ƙasa yana faɗin "Na gode, Na gode Allah ya jiƙan magabata ya yauƙaƙa Arziki, Allah ya biya maka buƙatunka na Alkhairi duniya da lahira, yadda ka Sanya farinciki a cikin zuciyata da ceto 'yata ubangiji Allah ya faranta maka, yayi maka tukuici na Alkhairi".

Alhaji Ahmad ya ce "Haba Malam Hassan, kar ka damu dan Allah wannan ai ba wani abin damuwa bane, Allah yayi wa yaranmu albarka baki ɗaya".

"Ameen Yallaɓai godiya nake".

Baba Hassan ji yake kamar an yaye masa damuwar da yake ciki, dan yana zuwa ɗakinsa yayi sujudu shukur, ya lalubo wayarsa ya kira Saminu.

Sai da ta kusa tsinkewa Sannan Saminu ya ɗaga, suka gaisa Baba Hassan ya ce "Saminu, dan Allah idan ka tashi tahowa, duk yadda zaka yi ka taho mini da Amina garin nan, ko a tasha ka ajiyeta sai ka kirani in zo in tafi da ita".

Saminu ya ce "To shikenan, amma ba zan taho yau ba gaskiya, sai dai gobe in Allah ya kaimu"

"Bakomai, amma dan Allah kar ka bari su farga su san da ita zaka taho, idan kuka taho daga baya nazo in musu bayani, idan suka san zaka kawo mini ita ba zasu bari ba".

Saminu ya ce "ba komai, kar ka damu Baba insha Allah zan kawo maka ita lafiya".

"To shikenan Saminu, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"

************

Yau Juma'a dan haka wankan hijjabi ta yi, pink tun daga sama har ƙasa, ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, ta shigo tana rataye da jakarta pink, hannunta riƙe da robar ruwa da mukullin motarta, bai san yadda aka yi ya shagala da kallonta ba, tayi kyau ƙarshe, ga wani irin sassanyan ƙamshi da take yi. Sai dai ta yi missing ɗin lectures ɗin farko da aka yi, dan suna takun saƙa da malamin, dan haka yau ba ta yi attending darasin sa ba, kuma darasin da yayi da lissafi a ciki, kuma ko da kai aka yi lissafin a ajin, abu ne mawuyaci mutum ya fahimta saboda yayi tsauri da yawa.

GABA DA GABANTAWhere stories live. Discover now