GABA DA GABANTA 28-29

260 20 7
                                    

GABA DA GABANTA

BY

AISHA ADAM (AYSHERCOOL/JAKADIYAR AREWA)



PAGE 28-29


Sai da hantar cikin Alhaji Ahmad ta kaɗa, saboda tsananin tsoron da ya shiga, har wata ƙishirwar wucin gadi ce ta kama shi, amma cikin dakiya da maziya ya maze ya bari ta ƙaraso.
"Meye wannan nake gani haka?" Tayi maganar tana nuna masa littafin.

Cikin rashin fahimta ya kalleta ya ce "Ban fahimta ba"

"Littafin 'yar aiki na gani a ɗakin aikin ka".

Alhaji Ahmad ya miƙe tsaye ya ce "Eh, na shiga zan yi amfani da ɗakin, amma duk yayi ƙura, duk da ba na shiga sai ina buƙatar yin aiki, ai Yakamata ki dinga sakawa ana gyarawa, ko gogewa ne ayi, ganin ba ayi hakan bane ya sa na bawa yarinyar umarnin gyarawa, ina ga mantawa tayi da shi a ciki". Har zuciyarta ta ji ta gamsu da bayanin da yayi mata.

'haka ne, hankalina ne bai kai a gyara ɗin ba, kuma nafi son idan za a gyara ɗin, a gyara ina wurin kar ayi maka ɓarna. A dawo lafiya"

"Yauwa na gode" ya amsa cikin mazewa ya juya ya bar Falon, yana yiwa Allah godiya da ya rufa masa asiri.

Amina kuwa da shirirtarta, tunani ta dinga yi a kan ta yaya ake sayar da kuɗi, kamar yadda Daddy ya gaya mata, amma bata iya gano ta yadda za'a sayar da kuɗi ba.
Lesson ɗin da take zuwa Makaranta ta fara gajiya, dan babu hutu sam, ga aikin gidan nan ba afuwa, kullum da abin da za'a ƙaƙalo a saka ka.

Yau Fadila a makare ta zo ita ma, motarta ta so ta bata matsala a hanya, sai dai tana zuwa ta tarar da kankiya ne a cikin ajin, bata ko bi ta kansa ba ta shiga ajin, sai dai ta hango Yazeed a wurin zamanta, a jikin window.
Tuno ranar da tayi masa wulaƙanci tayi, har ciwonsa ya tashi, dan haka ba tace masa komai ba ta zauna a kusa da shi. Wani irin warning glance sir Kankiya yayi mata, amma ta share shi, ta ciro littafinta daga jaka.
Gaba ɗaya annurin fuskar Kankiya ya ɗauke, ya ɗaure fuska gashi baya son ya aikata wani abu, da zai sa wani ya fuskanci son Fadila yake, kuma yana adawa da Yazid.
Haka ya gama lectures ɗin yana harar Fadila, ita kuwa ta nuna sam bata san ma me yake yi ba.
Bayan fitarsa ta ɗan saci kallon Yazid, ta basar, shikuwa ƙamshin turarenta ya hanashi sukuni.
Littafinta ya janyo, ya juya bayan yayi rubutu "Ina kwana ukuty?" Kallonsa tayi, gata gashi maimakon yayi mata magana, amma saboda wani salon rainin hankali shine ya rubuta mata.

Banza tayi masa taƙi kulashi. Ya sake rubuta mata 'Ya kika yi shiru, ko in tasar miki daga wurinki, naga kin haɗe rai?"

Babban abin da ya bata mamaki,bai wuce yadda yake rubutun da irin handwriting ɗinta ba. Kallonsa tayi cikin mamaki tana sake kallon rubutun, ba wanda zai ce ba nata bane.
Ganin tana kallonsa tare da kallon rubutun ne ya sanya shi ɗage mata gira ɗaya.

"Talk" ya sake rubuta mata.

"Bani littafina, tun da kurmancewa kayi yau"

Murmushi yayi ya ce "Ban kurmance ba, azumin magana nake".

Ta zura littafin a jaka, ya miƙo mata wasu takardu, tasa hannu ta karɓa tana dubawa.
Presentation ɗin da za suyi ne, na 'yan group ɗin su gaba ɗaya yayi musu, kuma a rubuce ya kai fullscap bakwai,tabi tsararren rubutun nasa da kallo, sannan ta kalleshi cikin mamaki 'Wai duk daga jiya zuwa yau kayi wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"Amma ai ka wahalar da kanka da yawa, wannan uban rubutun haka? Shikenan Sai mu kai Cafe a buga?"

Duk da yau baya son yin Magana, amma yaji daɗin yadda ta yaba ƙoƙarin sa.
Dan haka ya ce "Eh, da ina da babbar waya ko system, da a ciki zan mana sai ayi printing, kowa a bashi wanda zai yi presenting"

GABA DA GABANTAWhere stories live. Discover now