GABA DA GABANTA
AISHA ADAM AYSHERCOOL
44
Ganin Alhaji Ahmad ma ya ɗau zafi sosai, ya sanyata saurin saukowa daga nata fushin, dan da wuya yayi fushi amma idan yayi fushi wahalar sha'ani ne da shi fiye da tunani.
Dan haka ta ce "Naji shikenan ya wuce, na haƙura da saƙon na san yadda zan yi"
Bedroom ɗinsa ya wuce ya barta, tabi bayansa tana cigaba da lallaɓa shi, amma ya shareta ya ƙi saurarta.Ba ƙaramin yarfa Kankiya Fadila tayi ba, ganin yadda yake muzurai ake tsoronsa amma Fadila ta yarfa shi a gaban ɗalibai, hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba, kuma hakan ya jefa zargi a zukatan ɗaliban, mai zai sa Fadila ta tsinka malamin haka duk da yadda ake tsoronsa.
"Yazid, Yazid" tsayawa yayi ya waiwaya da jin muryarta a cikin dodon kunnuwansa.
Ta ƙarasa in da yake da sauri, bai ƙosa ba ya jira har ta cin masa.
Cikin damuwa ta ce "Sannu, ya jikin naka? Ashe baka da lafiya?"
"Eh, amma da sauƙi sosai Alhamdilillah"
"Wai meya sameka ne?"
"Rashin lafiya ne" ya bata amsa.
"Wane irin rashin lafiya?" Ta kuma tambayarsa cikin kulawa.
"An mini aikin appendix ne, sai kuma asma da ta dameni shikenan amma da sauƙi sosai"
"To yanzu ina zaka daga nan?"
"Gida zan tafi"
"Ok, to muje in sauke ka"
Da sauri ya girgiza mata kai ya ce "A'a ki bari na gode zan tafi"
"Ba ka ganin a yadda kake tafiya, kazo muje in sauke ka"
"Na gode, amma ba zan hau motarki ba, ban kai in hau mota irin wannan ba, ba ta dace da hawan talaka kamata ba" daga haka ya juya yana tafiya a hankali.
Tsayawa tayi tana cigaba da kallon yadda yake tafiya a hankali, har ya ɓacewa ganinta.
Tafe suke suna hira jefi jefi ita da Zakiru, yana bata labarin yanayin zamantakewar gidan kafin zuwanta.
"Ai nake gaya miki, ko 'yan uwan maigidan nan duk zumuncinsu sun haƙura sun daina zuwa, sun zuba masa ido, shi kansa sai lokaci lokaci yake zuwa, dama bata yadda yaranta suje ba, kuma fa 'yan gari ɗaya ne, saboda azabar baƙin halinta, duk son sa da yayi taimako sai dai yayi bata sani ba. Ai matar nan bana zaton tana son taga Annabi"
Amina ta ce "A'a karka ce haka, amma ina mamakin ita ko nata 'yan uwan basa zuwa sai ƙawaye"
"To ina taga wasu 'yan uwa ma, sukan zo wasu lokutan suna ba wani kallon arziki take musu ba, amma a hakan tana jidar kaya ta bani in kaiwa wasu daga 'yan uwanta, ai ita idan kika ga tana rawar kai tana nan nan da kai, to mai kuɗi ne kai, duk ta kanainaye maigidan baya jin maganar kowa sai tata, ai har gara yanzu a kan da, sanyinsa yayi yawa, sai ya fito cikin mutane ya fito yana taƙama baki Ga yadda ake girmama shi a waje ba, amma a gidansa ba shi da kataɓus ga shegen son 'ya'ya kamar masifa, waccan tsigalaliyar 'yar ta sa idan ta zauna tana taɓara abin takaici, gata halinta ɗaya da uwarta na rashin mutunci, ba kunya idan nayi kuskure take ƙare mini zagi, ai Alhaji Ahmad yayi ta kowane fanni amma a gidansa dai damisar kwali ne"
"Zakiru ya isheka haka, wasa yayi wasa banda tsikarin uwar miji da taɓarya" tayi maganar ranta a haɗe.
Zakiru ya ce "Kamar yaya kenan?"
"Ina ruwanka da abin da ke faruwa a gidansa kake ce masa damisar kwali, kai waya san yadda taka matar ke juyaka, ya isheka bana son wannan hirar"
Zakiru ya yi murmushi ya ce "Allah ya baki haƙuri, tuba nake"

YOU ARE READING
GABA DA GABANTA
RandomGABA DA GABANTA (Aljani ya taka wuta)😂 don't miss it, akwai cakwakiya