40

190 18 0
                                    

GABA DA GABANTA

BY
AISHA ADAM AYSHERCOOL

AREWABOOKS AYSHERCOOL7724
WATPAD ayshercool 7724

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=pfbid026t2vzuetnW2Fw4oD3AtFx8ssrmVz8MvDoQw62FEKNmt4Mc6YNC9ccxnCrk7CoCSNl&id=100089289690624

_Assalamu alaikum 'yan'uwa masu albarka_

_Muna roƙon arziƙi ku shiga wannan link ɗin ku yi mana sharhi kan labarin idan kun karanta, ku danna like sannan ku yi share ɗin shi, Allah Ya saka muku da alheri Ya ba ku tukuici da gidan Aljanna maɗaukakiya._

_SANARWA DAGA: GAMAYYAR MARUBUTAN JIHAR KANO (GAMJIK)_



40

Saroro baki buɗe, Hajara tabi Amina da kallon mamaki, gaba ɗaya gani take kamar ba Aminan da ta sani ba ce, wani ɓoyayyen abu take gani a kan fuskar Amina mai kama da ƙudurin da zata iya jurewa kowace irin barazana. Banda haka, ta yaya zata shigo falon matar gida tare da maigidan cikin wani yanayi da haryanzu ta rasa muhallin da zata saka shi.
Soyayya ce kenan? Ta tambayi kanta.
'a'a ba zai taɓa yiwuwa ba, mutumin da yake aiki a wani gari daban gari mai cike da goggagun mata masu ji da kansu, mai ɗumbin dukiya mai tarin yawa, ta yaya zai ɓige da son 'yar cikinsa, 'yar cikin nasa kuma mai aiki 'yar ƙauye?.

Sukuku haka Hajara ta bi hanyar da Amina tabi, tana tunanin yadda zata samo zaren labarin, ta gane a wani ma'auni zata ajiye alaƙar Amina da Alhaji Ahmad.

Cike da tsananin gulma da take cin Hajara, ta bi Amina ɗakinta, ta tarar da Amina ta cire uniform ta ɗaura towel zata shiga wanka.

Hajara ta kalli Amina tana ƙaƙalo murmushi ta ce "Wai nikam Amina, ban gane me kike ce mini ɗazu ba, naji kamar wata karin magana ki ka yi"

Amina tayi murmushi ta ce "Idan baki gane ba, ki barshi a haka kawai"

"Ba zaki mini bayani ba kenan, yau naga kin daɗe a makarantar"

"Eh, ai kin san muna zama yin lesson, shi ya sanya"

Hajara ta ce "Haka ne, tare kuka dawo da shi Alhajin kenan?"

"Eh Hajara, tare muka dawo, yaje ya ɗauko ni daga makaranta ne, shikenan? Ina son zan shiga wanka"

"To bari in baki wuri, Lallai Amina kin shigo gidan nan da ƙafar dama"

Amina bata kuma saurarrta ba, ta shige banɗaki ta bar Hajara.

Hajara ta riƙe haɓa tana sake jinjina kai, ga labari amma babu bakin bayarwa, dan ta san ko giyar karnuka ta sha, ba ta isa ta tunkari Hajiya Zainab da wata magana makamanciyar Wannan ba, dan ta san kome zai faru tare da ita zata kwaɓewa, to ta isa ma tayi wani yinƙuri na furta wani mummunan abu a kan maigida meye hujjarta?'

A fili ta ce "Allah ma ya ƙara, ni tsorona Allah ya sa ba lalubeta yake yi ba, ita matar gida tana can gantali kamar 'yar akuya kullum tana tafe kamar iska"

Ɓangaren Hafsa kuwa, ta rame tayi duhu, gaba ɗaya ta daina walwala, waccan rayuwar tata ta baya ta sake dawo mata sabuwa fil, cike da sabon salo mai ɗauke da ciwo irin na soyayya.
Tun daga koke koken nan da tayi, take fama da ciwon kai, tayi ta ƙoƙarin kawar da tunani da damuwa da Khalil, amma abu ya gagara tun tana ɓoyewa kar Mama ta gane, har abu ya zo ya zarce mata da zaɓi mai zafin gaske.
A hakan Mama ta gane, saboda ganin yawan kwanciyar da Hafsa take yi, ga rashin cin Abinci.

Cikin dare Mama ta tashi, domin yin sallar dare, ama ta dinga jin sheshsheƙar kukan Hafsa, ta miƙa hannu zata yaye abin rufar Hafsa, amma taji jikinta zafi rau.

"Hafsa meye haka? Meke damunki ne?"

"Mama bakomai"

"Kamar yaya babu komai, ji yadda jikinki yayi zafi, Hafsa kin ɗora kanki damuwa kina nema ki hallaka kanki, Hafsa ƙaddara ba zata samu bawa yayi tawakkali ba?"

GABA DA GABANTAWhere stories live. Discover now